Ezra yana karanta wa mutanen Dokar, yana kuma yabon Jehobah
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Farin Cikin da Jehobah Yake Bayarwa Shi Ne Ƙarfinku
Mutanen sun taru don su saurari Ezra saꞌad da yake karanta Dokar (Ne 8:1, 2; w13 10/15 21 sakin layi na 2; ka duba hoton shafin farko)
Wannan lokacin farin ciki ne a bautarsu ga Jehobah, ba lokacin baƙin ciki don zunuban da suka yi a dā ba (Ne 8:9, 11, 12)
Farin cikin da Jehobah yake bayarwa shi ne ƙarfin bayinsa (Ne 8:10; w07 8/1 9 sakin layi na 9-10)
KA TAMBAYI KANKA, ‘Duk da cewa ina fuskantar matsaloli, waɗanne dalilai ne za su sa in riƙa farin ciki?’