Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp22 Na 1 pp. 6-7
  • 1 | Kar Ka Nuna Bambanci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 1 | Kar Ka Nuna Bambanci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:
  • Abin da Ayar Take Nufi:
  • Yadda Za Ka Bi Wannan Ayar:
  • 3 | Ka Cire Kiyayya Daga Zuciyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Abin da Mutum Zai Yi don Ya Daina Kin Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Jehobah “Ba Mai-Tara Ba Ne”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
wp22 Na 1 pp. 6-7
Wani mutum bakin fata rike da hoton wani bature da yake murmushi, wani bature rike da hoton wani bakin mutum da yake murmushi. Can kuma ga hotunan mutanen da suke fushi.

ABIN DA MUTUM ZAI YI DON YA DAINA KIN MUTANE

1 | Kar Ka Nuna Bambanci

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:

“Allah ba ya nuna bambanci, amma yana karɓar duk mai tsoronsa da kuma mai aikata adalci a kowace al’umma.”​—AYYUKAN MANZANNI 10:​34, 35.

Abin da Ayar Take Nufi:

Jehobaha ba ya damuwa da ƙasar da mutum ya fito, ko ƙabilarsa, ko launin fatarsa ko kuma al’adarsa. Abin da ya fi muhimmanci a gare shi, shi ne ainihin halin mutum. “Mutum yakan duba yadda mutum yake daga waje, amma Yahweh yakan dubi zuciya ne.”​—1 Sama’ila 16:7.

Yadda Za Ka Bi Wannan Ayar:

Ba za mu iya sanin tunanin zuciyar mutane ba. Amma za mu iya yin koyi da Allah ta wurin yi musu kirki ba tare da nuna musu bambanci ba. Ka yi ƙoƙari ka san halin mutum maimakon ka ce, ‘Haka mutanen nan suke.’ Ka tuna cewa kowa yana da nasa halin. Idan ka lura cewa kana ƙin wasu mutane don inda suka fito, ko ƙabilarsu, ka roƙi Allah ya taimake ka ka daina wannan halin. (Zabura 139:​23, 24) Idan ka roƙi Allah ya taimake ka ka daina nuna bambanci, ba shakka zai ji addu’arka kuma zai taimaka maka ka yi hakan.​—1 Bitrus 3:12.

a Jehobah ko kuma Yahweh shi ne sunan Allah.​—Zabura 83:18.

“Ban taɓa zaman lafiya tare da bature haka ba . . . Yanzu na shiga cikin iyali da ke da ’yan’uwa a duk faɗin duniya.” ​—TITUS

Labarin Wani Mutum—TITUS

Ya Daina Nuna Ƙiyayya

Titus.

A dā ran Titus ya ɓace sosai don dokokin da gwamnati ta kafa da niyyar nuna wa baƙaƙen mutane bambanci. Don haka, sai ya haɗa kai da wasu ’yan adawa. Titus ya ce: “Mukan je wurare a cikin gari inda baƙaƙen fata ba sa shiga, kamar su otel da wuraren shan giya, don mu ta da rigima.” Titus ya ce ƙiyayya ce ta sa yake hakan. Ya ƙara da cewa: “Idan na soma gardama da wani ko wata, ni ne ke soma kai hari.”

Da Titus ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah ne halinsa ya soma canjawa. Abin da ya koya ya canja tunaninsa. Wani abin da ya burge shi sosai shi ne alkawarin Allah cewa zai sa a daina mutuwa, da baƙin ciki, da kuka, da azaba.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​3, 4. 

Bai yi ma Titus sauƙi ya daina ƙin mutane ba. Ya ce: “Canja tunanina da halina ya yi mini wuya sosai.” Abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a Ayyukan Manzanni 10:​34, 35 ne ya taimaka masa. Wurin ya ce Allah ba ya nuna bambanci.

Ta yaya ya amfana? Titus ya ce: “Da na ga yadda Shaidun Jehobah suke ƙaunar juna, ko da daga wace ƙasa ko ƙabila suka fito, hakan ya nuna min cewa suna bin addini na gaskiya. Kafin ma in yi baftisma in zama Mashaidin Jehobah, wani bature a ikilisiyar ya gayyace ni mu ci abinci tare. Na ji kamar mafarki nake yi. Ban taɓa zaman lafiya tare da bature haka ba, ballantana ma mu ci abinci tare. Yanzu na shiga cikin iyali da ke da ’yan’uwa a duk faɗin duniya.”

Za ka iya karanta cikakken labarin Titus a Hasumiyar Tsaro na 1 ga Agusta, 2009, shafi na 28-29, akwai shi a jw.org/ha.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba