Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w24 Yuli pp. 20-25
  • Muhimman Darussa Daga Labaran Sarakunan Israꞌila

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Muhimman Darussa Daga Labaran Sarakunan Israꞌila
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SUN BAUTA WA JEHOBAH DA DUKAN ZUCIYARSU
  • SUN YI TUBAN GASKE
  • SUN CI-GABA DA BAUTA MASA A HANYAR DA YAKE SO
  • Shawara ta Karshe da Maza Masu Aminci Suka Bayar
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Tuna Cewa Jehobah “Allah Mai Rai” Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Nemi Amsoshin Waɗannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Daꞌira na Mai Kula da Daꞌira na 2026
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
w24 Yuli pp. 20-25

TALIFIN NAZARI NA 30

WAƘA TA 36 Mu Riƙa Kāre Zuciyarmu

Muhimman Darussa Daga Labaran Sarakunan Israꞌila

“Za ku sāke ganin bambanci tsakanin mai adalci da mugu, kuma tsakanin wanda yake bauta wa Allah da wanda ba ya bauta masa.”—MAL. 3:18.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu bincika labaran sarakunan Israꞌila don mu ga abin da Jehobah yake bukata daga gare mu.

1-2. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da wasu sarakunan Israꞌila?

LITTAFI MAI TSARKI ya nuna cewa sarakuna fiye da 40 ne suka yi mulki a ƙasar Israꞌila.a Kuma ya gaya mana irin rayuwar da wasunsu suka yi. Alal misali, ya nuna cewa sarakuna masu kirki ma sun yi wasu abubuwa da ba su dace ba. Sarki Dauda yana cikinsu. Jehobah ya ce: Dauda “bawana . . . ya kuma bi ni da dukan zuciyarsa, yana aikata abin da ya yi daidai a idona kaɗai.” (1 Sar. 14:8) Amma Dauda ya taɓa yin zina da matar wani har ya yi ƙulle-ƙulle don a kashe maigidanta.—2 Sam. 11:4, 14, 15.

2 Littafi Mai Tsarki ya kuma nuna cewa wasu sarakuna marasa kirki sun yi wasu abubuwa masu kyau. Rehobowam yana ɗaya daga cikinsu. A gun Jehobah, “ya aikata mugunta.” (2 Tar. 12:14) Amma da Jehobah ya ce masa kada ya yaƙi ƙabilu goma da suka fita daga mulkinsa, ya yi biyayya. Ƙari ga haka, ya gyaggyara birane kuma ya gina musu katanga masu ƙarfi don ya kāre mutanen Allah.—1 Sar. 12:21-24; 2 Tar. 11:5-12.

3. Wace tambaya mai muhimmanci ce ta taso, kuma me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Yanzu tambaya mai muhimmanci da ta taso ita ce: Da yake sarakunan Israꞌila sun yi abubuwa masu kyau da marasa kyau, me ya sa Jehobah ya ɗauki wasu a matsayin masu aminci, wasu kuma marasa aminci? Sanin amsar tambayar nan zai taimaka mana mu san abin da Jehobah yake bukata a gare mu. Game da sarakunan nan, za mu tattauna abubuwa uku da Jehobah ya duba, wato: Yaya yanayin zuciyarsu? Sun tuba da gaske? Kuma sun ci-gaba da bauta masa a hanyar da yake so?

SUN BAUTA WA JEHOBAH DA DUKAN ZUCIYARSU

4. Me ya bambanta sarakuna masu amincin da marasa amincin?

4 Sarakunan da Jehobah ya ce su masu aminci ne sun bauta masa da dukan zuciyarsu.b Alal misali, Sarki Jehoshafat “ya bauta wa Yahweh da dukan zuciyarsa.” (2 Tar. 22:9) Game da Josiya, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba a taɓa yin sarki kamarsa ba, ko kafin shi ko bayansa, wanda ya juya ga Yahweh da dukan zuciyarsa.” (2 Sar. 23:25) Sulemanu kuma fa, wanda daga baya ya yi wa Jehobah rashin aminci? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bai miƙa zuciyarsa gaba ɗaya ga Yahweh Allahnsa” ba. (1 Sar. 11:4) Abiyam shi ma wani sarki ne marar aminci, kuma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bai kuwa miƙa wa Yahweh Allahnsa zuciyarsa gaba ɗaya” ba.—1 Sar. 15:3.

5. Mene ne bauta ma Jehobah da dukan zuciya yake nufi?

5 Mene ne bauta ma Jehobah da dukan zuciya yake nufi? Wanda yake bauta ma Jehobah da dukan zuciyarsa yana yin haka ne don yana ƙaunar Jehobah sosai kuma yana daraja shi, ba don ya zama dole ba. Irin wannan mutumin ba ya daina ƙaunar Jehobah da kuma daraja shi.

6. Ta yaya za mu bauta ma Jehobah da dukan zuciyarmu? (Karin Magana 4:23; Matiyu 18:8)

6 Ta yaya mu ma za mu bauta ma Jehobah da dukan zuciyarmu kamar sarakunan Israꞌila masu aminci? Mu guji duk wani abin da zai sa mu yi wa Jehobah rashin aminci. Alal misali, yin nishaɗi da bai dace da Kirista ba, zai iya sa mu soma son abin da Jehobah ba ya so. Ƙari ga haka, ya kamata mu yi hankali da irin abokai da muke yi, don kar su sa mu soma tunani cewa samun abin duniya ne ya fi muhimmanci. Da zarar mun ga cewa wani abu yana sa mu so abin da Jehobah ba ya so, mu yi maza-maza mu yar da shi.—Karanta Karin Magana 4:23; Matiyu 18:8.

7. Me ya sa yake da muhimmanci mu guji nishaɗi marar kyau da abokan banza?

7 Kada mu bar wani abu ya hana mu bauta ma Jehobah da dukan zuciyarmu. Idan ba mu yi hankali ba, za mu iya ruɗin kanmu cewa ko da muna yin nishaɗi marar kyau ko muna bin abokan banza, hakan ba zai shafi dangantakarmu da Jehobah ba muddin muna yin ayyukan ibada da himma. Alal misali, a ce ana iska sosai da kura, sai ka share ɗakinka ka kuma goge koꞌina. Amma kuma ka bar ƙofa da wundodinka duk a buɗe. Me zai faru da ɗakin da ka goge? Nan-da-nan kura zai mamaye koꞌina, ko ba haka ba? Haka ma yake da abokantakarmu da Jehobah, ba yin ayyukan ibada kawai muke bukatar mu yi ba. Dole mu ƙi irin tunani da raꞌayoyin mutanen duniyar nan, in ba haka ba, za su hana mu ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarmu.—Afis. 2:2.

SUN YI TUBAN GASKE

8-9. Da aka gaya ma Sarki Dauda da Sarki Hezakiya laifinsu, mene ne suka yi? (Ka duba hoton.)

8 Kamar yadda aka ambata a sakin layi na farko, Sarki Dauda ya yi zunubi mai tsanani. Amma da annabi Natan ya gaya ma Dauda laifinsa, ya ƙasƙantar da kansa kuma ya tuba. (2 Sam. 12:13) Dauda bai tuba don ya kauce ma hukunci da ya kamata a yi masa, ko kuma don ya ruɗi annabi Natan ba. Abin da ya ce a Zabura ta 51 ya nuna cewa tuban gaske ne ya yi.—Zab. 51:3, 4, 17, da rubutu da ke saman surar.

9 Sarki Hezekiya shi ma ya yi zunubi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Saboda yawan girman kansa, . . . Yahweh ya yi fushi da shi, da mutanen Yahuda da Urushalima.” (2 Tar. 32:25) Me ya sa shi girman kai? Wataƙila yawan dukiyarsa ne, ko nasarar da ya yi a kan Assuriyawa, ko kuma don yadda Jehobah ya warkar da shi a hanya mai ban mamaki. Mai yiwuwa girman kai ne ya sa Hezekiya ya nuna wa Babiloniyawa yawan dukiyarsa, kuma annabi Ishaya ya tsauta masa don abin da ya yi. (2 Sar. 20:12-18) Amma daga baya, Hezekiya ya ƙasƙantar da kansa kuma ya tuba kamar Dauda. (2 Tar. 32:26) A ƙarshe, Jehobah ya ɗauke shi a matsayin sarki mai aminci da ya “aikata abin da yake daidai.”—2 Sar. 18:3.

Hotuna: 1. Sarki Dauda ya kalli sama yana nadama lokacin da Natan yake masa magana. 2. Sarki Hezekiya ya sunkuyar da kansa yana nadama lokacin da Ishaya yake masa magana.

Da aka gaya wa Sarki Dauda da Sarki Hezekiya laifinsu, sun ƙasƙantar da kansu kuma sun tuba (Ka duba sakin layi na 8-9)


10. Da aka gaya ma Sarki Amaziya laifinsa mene ne ya yi?

10 Sarki Amaziya na Yahuda bai yi kamar Sarki Dauda da Sarki Hezekiya ba, don ya yi abin da yake daidai “amma ba da dukan zuciyarsa ba.” (2 Tar. 25:2) Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya faɗi hakan? Domin bayan da Jehobah ya taimaki Amaziya ya ci Edomawa da yaƙi, sai ya kwaso gumakansu kuma ya yi musu sujada.c Da annabin Jehobah ya gaya masa laifinsa, ya ƙi ji, kuma ya kore shi.—2 Tar. 25:14-16.

11. Bisa ga 2 Korintiyawa 7:9, 11, me muke bukatar mu yi don Jehobah ya gafarce mu? (Ka kuma duba hotunan.)

11 Me muka koya daga labaran nan? Sun nuna cewa idan muka yi zunubi, muna bukatar mu tuba kuma mu yi iya ƙoƙarinmu kar mu maimaita zunubin. Idan kuma dattawa sun yi mana gargaɗi a kan abin da muke ganin ba wani abu ba ne fa? Kar mu ɗauka cewa Jehobah ba ya son mu ko kuma dattawan ba sa son mu, shi ya sa suka yi mana gargaɗin. Domin ko sarakunan Israꞌila masu kirki ma an yi musu horo da gargaɗi. (Ibran. 12:6) Idan aka yi mana gargaɗi, (1) mu amince cikin sauƙin kai, (2) mu yi gyara da ake bukata, kuma (3) mu ci-gaba da bauta ma Jehobah da dukan zuciyarmu. Idan muka yi tuban gaske, Jehobah zai gafarce mu.—Karanta 2 Korintiyawa 7:9, 11.

Hotuna: 1. Wani dattijo da matashi ne yana magana da wani danꞌuwa. Danꞌuwan kuma yana kallon giya da ke cikin kwalba da kuma kofi. 2. Danꞌuwan yana nazarin Littafi Mai Tsarki da littafin nan, “Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!” darasi na 43. 3. Dattijon da danꞌuwan suna waꞌazi gida-gida tare.

Idan aka yi mana gargaɗi, (1) mu amince cikin sauƙin kai, (2) mu yi gyara da ake bukata, kuma (3) mu ci-gaba da bauta ma Jehobah da dukan zuciyarmu (Ka duba sakin layi na 11)f


SUN CI-GABA DA BAUTA MASA A HANYAR DA YAKE SO

12. Wane abu mai muhimmanci ne ya bambanta sarakuna masu amincin da marasa amincin?

12 Sarakunan da Jehobah ya ɗauke su a matsayin masu aminci sun bauta masa a hanyar da yake so. Sun kuma ƙarfafa talakawansu su yi haka. Kamar yadda muka sani, sarakunan nan ma sun yi kurakurai, amma sun bauta ma Jehobah shi kaɗai, kuma sun yi iya ƙoƙarinsu su kawar da bautar gumaka.d

13. Me ya sa Jehobah ya ɗauki Sarki Ahab a matsayin marar aminci?

13 Sarakuna da Jehobah ya ɗauke su a matsayin marasa aminci kuma fa? Su ma sun yi wasu abubuwa masu kyau. Alal misali, Sarki Ahab mugu ne, amma da ya ji cewa an kashe Nabot saboda shi, ya ƙasƙantar da kansa kuma ya yi baƙin ciki. (1 Sar. 21:27-29) Ya kuma gina birane, kuma ya ci magabtan Israꞌila da yawa da yaƙi. (1 Sar. 20:21, 29; 22:39) Amma akwai wani babban zunubi da Ahab ya yi. Ya bar matarsa ta zuga shi ya ɗaukaka bautar gumaka. Kuma bai taɓa yin tuba ba.—1 Sar. 21:25, 26.

14. (a) Me ya sa Jehobah ya ɗauki Sarki Rehobowam a matsayin marar aminci? (b) Wane abu ne yawancin sarakuna marasa amincin suka yi?

14 Wani sarki marar aminci kuma shi ne Rehobowam. Kamar yadda aka ambata a sakin layi na biyu, ya yi abubuwa da dama masu kyau. Amma da mulkinsa ya kafu sosai, sai ya daina bin koyarwar Jehobah kuma ya soma bauta ma gumaka. (2 Tar. 12:1) Bayan haka, bai tsaya a wuri ɗaya ba, wani lokaci ya bauta ma Jehobah, wani lokaci kuma ya bauta ma gumaka. (1 Sar. 14:21-24) Ba Rehobowam da Ahab ne kaɗai sarakuna da suka daina bauta wa Jehobah a hanyar da yake so ba. Yawancin sarakuna marasa amincin sun bauta wa gumaka, kuma sun zuga talakawansu su yi hakan. Wannan ya nuna cewa wani muhimmin abin da ya sa Jehobah ya ɗauki wasu sarakuna a matsayin masu aminci shi ne, sun bauta masa a hanyar da yake so.

15. Me ya sa yake da muhimmanci mu guji duk wani abin da ya danganci bauta ta ƙarya?

15 Me ya sa yadda sarakunan suka bauta ma Jehobah yake da muhimmanci a gare shi? Wani dalili shi ne, hakkinsu ne su ƙarfafa mutane su bauta masa a hanyar da yake so. Ƙari ga haka, bauta wa gumaka takan sa mutane su yi zunubai masu tsanani, da kuma mugunta. (Hos. 4:1, 2) Ban da haka ma, an keɓe sarakunan da talakawansu da tsarki ga Jehobah. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce bautar gumaka da suka yi kamar karuwanci ne. (Irm. 3:8, 9) Yin zina cin amana ne sosai ga wadda mutum ya aura. Haka ma idan wanda ya yi alkawarin bauta ma Jehobah ya yi wani abin da ya danganci bauta ta ƙarya, ya ci amanar Jehobah ke nan, kuma abin zai ɓata Mishi rai ba kaɗan ba.e—M. Sha. 4:23, 24.

16. Mene ne ke bambanta mai adalci da mugu a idanun Jehobah?

16 Wane darasi hakan ya koya mana? Darasin shi ne: Dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu guji duk wani abin da ya danganci bauta ta ƙarya. Ban da haka, dole mu ci-gaba da bauta ma Jehobah a hanyar da yake so, kuma da ƙwazo. Annabi Malakai ya bayyana abin da ke bambanta mai adalci da mugu a idanun Jehobah. Ya ce: “Saꞌan nan za ku sāke ganin bambanci tsakanin mai adalci da mugu, kuma tsakanin wanda yake bauta wa Allah da wanda ba ya bauta masa.” (Mal. 3:18) Don haka, kar mu taɓa yarda ajizancinmu ko kurakuran da muka yi ko wani abu dabam, ya sa mu yi sanyin gwiwa har mu daina bauta ma Jehobah. Domin daina bauta ma Jehobah, babban zunubi ne.

17. Idan mutum ya auri wadda ba ta bauta ma Jehobah, ta yaya hakan zai shafi dangantakarsa da Jehobah?

17 Idan kana so ka yi aure, abin da Malakai ya faɗa zai taimaka maka ka zaɓi wadda ta dace. Wataƙila wadda kake so ka aura tana da hali mai kyau, amma idan ba ta bauta ma Jehobah, Jehobah ba zai ɗauke ta a matsayin mai adalci ba. (2 Kor. 6:14) Ƙari ga haka, idan ka aure ta, za ta taimaka maka ka ci-gaba da bauta ma Jehobah? Ka ɗauki darasi daga abin da ya faru da Sulemanu. Wataƙila matan da ya aura suna da wasu halaye masu kyau, amma ba sa bauta wa Jehobah, kuma da sannu-sannu sun rinjaye shi ya soma bauta wa gumaka.—1 Sar. 11:1, 4.

18. Me ya kamata iyaye su koya ma yaransu?

18 Iyaye, za ku iya yin amfani da labaran sarakunan nan ku koyar da yaranku su so bauta ma Jehobah. Ku sa su fahimci cewa a gun Jehobah, sarakuna da suka bauta masa kuma suka ƙarfafa mutane su yi hakan ne masu aminci. Ku koya musu, kuma ku nuna musu ta halinku, cewa ayyukan da suka fi muhimmanci su ne ayyukan ibada, kamar yin nazarin Littafi Mai Tsarki, da zuwa taro, da yin waꞌazi, da dai sauransu. (Mat. 6:33) Idan ba ku yi haka ba, zai yi musu wuya su ƙaunaci Jehobah kuma su so bauta masa. A maimako, za su riƙa bin ku ne kawai, wataƙila ma su daina bauta wa Jehobah.

19. Idan mutum ya daina bauta ma Jehobah, na shi ya ƙare ke nan? (Ka kuma duba akwatin nan “Za Ka Iya Komowa ga Jehobah!”)

19 Idan mutum ya daina bauta ma Jehobah, hakan yana nufin cewa nashi ya ƙare ke nan? Aꞌa, domin zai yiwu mutumin ya tuba kuma ya koma bauta ma Jehobah. Abin da zai taimaka masa shi ne, ya ƙasƙantar da kansa kuma ya gaya wa dattawa su taimaka masa. (Yak. 5:14) Yin haka ba zai yi masa sauƙi ba, amma idan ya yi iya ƙoƙarinsa kuma ya komo ga Jehobah, zai ga cewa kwalliyar ta biya kuɗin sabulu!

Za Ka Iya Komowa ga Jehobah!

Ka tuna da labarin Sarki Manasse. “Ya aikata mugunta sosai a idon Yahweh.” “Ya kakkashe marasa laifi da yawa.” Ya yi ayyukan sihiri dabam-dabam, har ya yi hadaya da yaransa ga gumakan da yake bauta wa. (2 Sar. 21:6, 16) Ya sa mutanen Yahuda “suka aikata mugunta fiye da alꞌumman da Yahweh ya kora daga ƙasar.” (2 Sar. 21:9; 2 Tar. 33:1-6) Amma da aka kai shi zaman bauta a ƙasar Babila, sai ya tuba. Da yake zunubansa masu tsanani ne kuma ya daɗe yana yinsu, ba sau ɗaya ne kawai ya nemi gafara ba. Saꞌad da yake cikin tsananin wahala, Manasse ya “[ci-gaba da, NWT] ƙasƙantar da kansa” da yin “kuka ga Allah.” Jehobah ya ji kukansa kuwa? Ƙwarai! Jehobah ya tausaya masa kuma “ya amsa roƙonsa.” Jehobah ya gafarta masa, ya komar da shi Urushalima, kuma ya mai da shi a kan kujerar mulkinsa.—2 Tar. 33:12, 13.

A yau, idan mutum ya daina bauta ma Jehobah, amma ya yi tuban gaske, shin Jehobah zai gafarta masa? Ƙwarai kuwa! Shi ya sa Ishaya 55:7 ta ce: “Bari mai mugunta ya bar hanyarsa, marar adalci kuma ya bar tunaninsa. Bari ya komo ga Yahweh, shi kuwa zai yi masa jinƙai, ya komo ga Yahweh gama a shirye yake ya gafarce shi.” Don haka, kar ka bar wani abu ya hana ka ɗaukan matakan da ya kamata don ka komo ga Jehobah!

20. Idan muka bi misalin sarakunan Israꞌila masu aminci, yaya Jehobah zai ɗauke mu?

20 Waɗanne darussa ne muka koya daga labaran sarakunan Israꞌila? Mun koyi cewa za mu iya zama kamar sarakuna masu amincin idan muka ci-gaba da bauta ma Jehobah da dukan zuciyarmu. Idan muka yi kuskure, mu ɗau darasi daga abin da ya faru, mu tuba, kuma mu yi gyara da ake bukata. Idan ka ci-gaba da bauta ma Jehobah shi kaɗai, zai ɗauke ka a matsayin wanda yake aikata abin da ya yi daidai.

TA YAYA ZA MU . . .

  • ci-gaba da bauta ma Jehobah da dukan zuciyarmu?

  • nuna cewa mun tuba da gaske?

  • ci-gaba da bauta ma Jehobah a hanyar da yake so?

WAƘA TA 45 Abubuwan da Nake Tunani a Kai

a A wannan talifi, idan aka ce “sarakunan Israꞌila,” ana nufin dukan sarakuna da suka yi mulki a kabilu biyu na Yahuda da kabilu goma na Israꞌila.

b MAꞌANAR WASU KALMOMI: Littafi Mai Tsarki yakan yi amfani da kalmar nan “zuciya,” don ya kwatanta irin mutumin da muke, wato muradinmu, da halayenmu, da abubuwan da muka iya yi, da dalilin da ya sa muke yin abubuwa.

c A zamanin dā, idan sarakuna da ba Israꞌilawa ba suka ci wata ƙasa da yaƙi, sukan bauta wa allolin ƙasar.

d Sarki Asa ya yi zunubai masu tsanani sosai. (2 Tar. 16:7, 10) Amma Littafi Mai Tsarki ya ce ya yi abin da yake daidai a idon Yahweh. Ko da yake bai ji gargaɗi da aka yi mishi da farko ba, mai yiwuwa daga baya ya tuba. Ayyukan kirki da ya yi sun fi kurakurai da ya yi, kuma abin da Jehobah ya gani ke nan. Wani abu mai muhimmanci shi ne, Jehobah ne kaɗai Asa ya bauta wa, kuma ya yi iya ƙoƙarinsa ya kawar da bautar gumaka a mulkinsa.—1 Sar. 15:11-13; 2 Tar. 14:2-5.

e A Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa, doka ta farko da ta biyu sun haramta yin sujada ga wani ban da Jehobah.—Fit. 20:1-6.

f BAYANI A KAN HOTUNA: Wani dattijo da matashi ne, yana yi ma wani ɗanꞌuwa magana a kan yadda yake shan giya. Ɗanꞌuwan ya ƙasƙantar da kansa, ya amince da gargaɗin, ya ɗauki mataki da ya kamata, kuma ya ci-gaba da bauta ma Jehobah da dukan zuciyarsa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba