SHAWARA A KAN YIN NAZARI
Ka Yi Nazari da Niyyar Gaya wa Wasu Abin da Ka Koya
Yin nazari yana sa mu farin ciki, amma za mu fi yin farin ciki idan muka gaya wa wasu abubuwan da muka koya da suka taimaka mana mu daɗa kusantar Jehobah. Karin Magana 11:25 ta ce: “Mai taimaka wa waɗansu, shi kansa zai sami taimako.”
Idan muka gaya wa wasu abubuwan da muka koya daga nazarinmu, hakan zai sa mu riƙa tunawa da sauƙi. Kuma za mu ƙara fahimtar batun. Ƙari ga haka, wasu za su iya amfana daga abubuwan da muka koya. Yin hakan zai sa mu yi farin ciki.—A. M. 20:35.
Ga abin da za ka iya yi: A cikin mako mai zuwa, ka yi ƙoƙari ka gaya wa wani abin da ka koya daga nazarinka. Za ka iya gaya wa wani danginka, ko wani a ikilisiyarku, ko wani a wurin aikinku, ko wani maƙwabcinka ko kuma wani da ka haɗu da shi a waꞌazi. Ka yi ƙoƙari ka bayyana abin da ka koya a hanya mai sauƙi.
Ka tuna: Saꞌad da kake gaya wa mutane abin da ka koya daga nazarinka, ka yi hakan don ka ƙarfafa su, ba don ka burge su ba.—1 Kor. 8:1.