Sabbin Membobi Guda Biyu na Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu
A RANAR 5 ga Oktoba, 2024, an yi wata sanarwa mai muhimmanci a taron shekara-shekara cewa: An naɗa Ɗanꞌuwa Jody Jedele da Ɗanꞌuwa Jacob Rumph su zama membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu. ꞌYanꞌuwa biyun sun daɗe suna bauta wa Jehobah da aminci.
Ɗanꞌuwa Jody Jedele da matarsa, Damaris
An haifi Ɗanꞌuwa Jedele a Missouri, a ƙasar Amurka kuma iyayensa Shaidu ne. Gidansu yana yankin da babu Shaidu sosai. Saboda haka, ya haɗu da ꞌyanꞌuwa daga wurare dabam-dabam da suke zuwa yin waꞌazi a yankinsu. Ƙauna da haɗin kan ꞌyanꞌuwan sun burge su sosai. Ya yi baftisma a ran 15 ga Oktoba, 1983. Yana son yin waꞌazi sosai, kuma bayan ya gama makarantar sekandare, ya soma hidimar majagaba na kullum a Satumba 1989.
Saꞌad da Ɗanꞌuwa Jedele yake ɗan yaro, iyayensu sukan ɗauke shi da ꞌyarꞌuwarsa su kai ziyara a Bethel. Hakan ya sa yaran sun kafa burin yin hidima a Bethel, kuma su biyun sun cim ma burinsu. Ɗanꞌuwa Jedele ya soma hidima a Bethel da ke Wallkill a watan Satumba 1990. Ya soma aiki ne a Sashen Share-share, kuma daga baya ya koma Sashen Kula da Lafiya.
A lokacin, an bukaci ꞌyanꞌuwa maza su zo su yi hidima a ikilisiyoyin da ake Sifanisanci. Ɗanꞌuwa Jedele ya soma halartar ɗaya daga cikinsu kuma ya soma koyan yaren. Ba da daɗewa ba bayan hakan, ya haɗu da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Damaris, da take hidimar majagaba a daꞌirarsu. Da shigewar lokaci, sun yi aure, kuma su biyu suka ci-gaba da hidima a Bethel.
A 2005, sun bar Bethel don su kula da iyayensu. A lokacin, sun yi hidimar majagaba na kullum. Ɗanꞌuwa Jedele ya taimaka wajen koyarwa a Makarantar Hidima ta Majagaba, kuma ya yi hidima a Kwamitin Hulɗa da Asibitoci da Kwamitin Gini na Yanki.
A 2013, an gayyaci Ɗanꞌuwa da ꞌYarꞌuwa Jedele zuwa Bethel don aikin gine-ginen da ake yi a Warwick. Tun daga lokacin, sun yi hidima a Bethel da ke Patterson da kuma Wallkill. Ɗanꞌuwa Jedele ya yi hidima a Sashen Gine-gine da kuma a Sashen Masu Ba da Bayani Game da Asibitoci. A watan Maris 2023, an naɗa Ɗanꞌuwa Jedele a matsayin mataimakin Kwamitin Hidima. Yayin da yake tunani a kan hidimomi dabam-dabam da ya yi, ya ce: “Idan aka ce ka soma wata sabuwar hidima, tsoro zai iya kama ka. Amma a lokacin ne kake bukatar ka dogara ga Jehobah domin shi ne zai iya taimaka mana mu iya yin duk wani aikin da ya ba mu.”
Ɗanꞌuwa Rumph da matarsa, Inga
An haifi Ɗanꞌuwa Rumph a California, a ƙasar Amurka. Saꞌad da yake ɗan yaro, mahaifiyarsa ta daina fitan waꞌazi da kuma zuwan taro. Amma ta yi ƙoƙari ta koya masa gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, kowace shekara, yakan ziyarci kakarsa da take bauta wa Jehobah da aminci. Ta sa ya yi marmarin yin nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma saꞌad da yake shekara 13, ya ce a soma yin nazari da shi. Ya yi baftisma a ranar 27 ga Satumba, 1992. Ana nan, sai mahaifiyarsa ta soma fitan waꞌazi da zuwa taro, saꞌan nan mahaifinsa da ꞌyanꞌuwansa suka samu ci-gaba kuma suka yi baftisma.
Saꞌad da yake matashi, Ɗanꞌuwa Rumph ya ga irin farin cikin da majagaba suke yi. Saboda haka, bayan ya gama makarantar sekandare, ya soma hidimar majagaba a Satumba 1995. A shekara ta 2000, ya ƙaura zuwa Ecuador don ya yi hidima a inda ake bukatar masu shela. A wurin ya haɗu da wata ꞌyarꞌuwa majagaba ꞌyar Kanada mai suna Inga, kuma daga baya sun yi aure. Bayan aurensu, sun yi hidima a wani gari da ke ƙasar Ecuador, kuma a lokacin ꞌyanꞌuwa kaɗan ne a wurin. Amma a yau, akwai ꞌyanꞌuwa da yawa a wurin.
Da shigewar lokaci, Ɗanꞌuwa Rumph da matarsa sun soma hidima a matsayin majagaba na musamman. Kuma daga baya, sun soma hidimar kula da daꞌira. A 2011, an gayyace su su halarci Makarantar Gilead aji na 132. Bayan sun sauƙe karatu, sun yi hidima a ƙasashe dabam-dabam. Ƙari ga haka, sun yi hidima dabam-dabam kamar hidima a Bethel, da waꞌazi a ƙasashen waje, da kuma hidimar kula da daꞌira. Ɗanꞌuwa Rumph ya kuma sami damar koyarwa a Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki.
A lokacin annobar korona, Ɗanꞌuwa Rumph da matarsa sun dawo ƙasar Amurka. Sun soma hidima a Bethel da ke Wallkill, kuma a wurin Ɗanꞌuwa Rumph ya soma aiki a Sashen Kula da Hidima. Daga baya, sun sake koma Bethel da ke ƙasar Ecuador, kuma a wurin Ɗanꞌuwa Rumph ya zama memban Kwamitin da Ke Kula da Reshen Ofishin. A 2023, sun koma ƙasar Amurka kuma suka soma hidima a Warwick. A Janairu 2024, an naɗa Ɗanꞌuwa Rumph a matsayin mataimakin Kwamitin Hidima. Yayin da yake tunani a kan hidimomi dabam-dabam da ya yi, ya ce, “Abin da ya fi muhimmanci shi ne mutanen da muke aiki da su, ba irin hidimar da muke yi ba.”
Muna alfahari da ꞌyanꞌuwan nan don aiki tuƙuru da suke yi, kuma muna girmama irin waɗannan ꞌyanꞌuwan.—Filib. 2:29.