Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w19 Janairu p. 31
  • Sabon Memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sabon Memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Makamantan Littattafai
  • Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta Samu Ƙaruwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Sababbi da Aka Haɗa Cikin Hukumar Mulki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Sababbi Waɗanda Aka Daɗa Cikin Hukumar Mulki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Sabbin Mambobi Guda Biyu na Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
w19 Janairu p. 31
Kenneth da Jamie Cook

Ɗan’uwa Kenneth E. Cook, Jr., da matarsa Jamie

Sabon Memban Hukumar Da Ke Kula Da Ayyukanmu

A SAFIYAR ranar Laraba, 24 ga Janairu, 2018, an sanar wa ’yan’uwa da ke hidima a Bethel da ke Amirka da kuma Kanada cewa an naɗa Ɗan’uwa Kenneth Cook Jr., a matsayin memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah.

An haifi Ɗan’uwa Cook a kudancin jihar Pennsylvania da ke Amirka, kuma ya yi girma a wurin. Ya koyi gaskiya daga wani ɗan ajinsu kafin ya sauke karatu daga makarantar sakandare kuma ya yi baftisma a ranar 7 ga Yuni, 1980. Ya soma hidimar majagaba na kullum a ranar 1 ga Satumba, 1982. Kuma bayan ya yi hidimar majagaba na shekara biyu, sai ya soma hidima a Bethel da ke Wallkill a Amirka a ranar 12 ga Oktoba, 1984.

Ɗan’uwa Cook ya yi hidima a sashe dabam-dabam, hakan ya ƙunshi Sashen Buga Littattafai da kuma Sashen da Ke Kula da Ma’aikatan Bethel. Ya auri matarsa Jamie a shekara ta 1996, kuma ta soma hidima tare da shi a Wallkill. Ɗan’uwa Cook da matarsa sun koma Cibiyar Koyarwa da ke Patterson a Amirka a watan Disamba 2009. Ya yi aiki a Sashen Amsa Tambayoyin Masu Karatu a wurin. A watan Afrilu, 2016 bayan ya ɗan koma Bethel da ke Wallkill, Ɗan’uwa Cook da matarsa sun koma Bethel da ke Brooklyn. Bayan watanni biyar sai suka koma hedkwatarmu da ke Warwick a Amirka. Ɗan’uwa Cook ya soma hidima a matsayin mataimakin Kwamitin Rubuce-Rubuce na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah a watan Janairu 2017.

Membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu yanzu sun kai takwas:

K. E. Cook, Jr.; S. F. Herd; G. W. Jackson; M. S. Lett; G. Lösch; A. Morris III; D. M. Sanderson; D. H. Splane

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba