Sababbi da Aka Haɗa Cikin Hukumar Mulki
A RANAR Laraba da safe, 24 ga Agusta, 2005, iyalin Bethel da ke Amirka da kuma Kanada, ta wurin bidiyo suka ji sanarwa mai ba da farin ciki. Somawa daga 1 ga Satumba, 2005, za a daɗa sababbi mutane biyu, wato Geoffrey W. Jackson da kuma Anthony Morris na uku, ga Hukumar Mulki na Shaidun Jehobah.
Ɗan’uwa Jackson ya soma aikin majagaba a Fabrairu ta shekara ta 1971 a garin Tasmania, a jihar Australiya. A Yuni, shekara ta 1974 ya auri Jeanette (Jenny). Ba da daɗewa ba aka naɗa su majagaba na musamman. Daga shekara ta 1979 zuwa 2003, sun yi hidima na masu wa’azi a ƙasashen waje a Tuvalu, Samoa, da Fiji, wato ƙasashen tsibirai na Kudancin Tekun Pasifik. Da suke waɗannan tsibirai, Ɗan’uwa da ’Yar’uwa Jackson sun taimaka sosai wajen fassara littattafan Littafi Mai Tsarki. Somawa daga shekara ta 1992, Ɗan’uwa Jackson ya yi hidima na Kwamitin Reshe a Samoa, kuma daga shekara ta 1996 ya yi wannan hidima na Kwamitin Reshe a Fiji. A watan Afrilu na shekara ta 2003, da shi da matarsa Jenny suka koma Bethel na Amirka kuma suka soma aiki a Sashen Taimakon Masu Fassara. Ba da daɗewa ba bayan haka, aka mai da Ɗan’uwa Jackson mataimakin Kwamitin Koyarwa na Hukumar Mulki.
Ɗan’uwa Morris shi ma ya soma hidimar majagaba a shekara ta 1971 a Amirka. A watan Disamba na wannan shekara, ya auri Susan kuma suka ci gaba da aikin majagaba na kusan shekara huɗu kafin suka haifi ɗansu na fari, Jesse. Bayan shekara guda da wata takwas suka sami wani ɗa, Paul. Ɗan’uwa Morris ya sake shigan hidima ta cikakken lokaci a shekara ta 1979 ya yi hidimar majagaba na kullum. Matarsa ita ma ta shiga hidimar majagaba sa’ad da da yaran suka soma makaranta. Iyalin sun yi hidima a inda ake da bukata mai girma a Tsibirin Rhode da kuma Carolina ta Arewa a Amirka. A Carolina ta Arewa, Ɗan’uwa Morris ya yi hidima na wakilin mai kula da da’ira. An gayyaci Jesse da Paul zuwa reshe na Amirka, lokacin da kowannensu yake ɗan shekara 19. Yayin nan kuma Ɗan’uwa Morris ya soma aikin mai kula da da’ira. A shekara ta 2002 aka gayyace shi da matarsa Susan zuwa Bethel, suka soma aikinsu a ranar ɗaya 1 ga Agusta. Ɗan’uwa Morris ya yi aiki a Sashen Hidima a Patterson kuma bayan haka ya zama mataimakin Kwamitin Hidima na Hukumar Mulki.
Ƙari ga waɗannan sababbi biyu, Hukumar Mulki ta ƙunshi C. W. Barber; J. E. Barr; S. F. Herd; M. S. Lett; G. Lösch; T. Jaracz; G. H. Pierce; A. D. Schroeder; D. H. Splane; da kuma D. Sydlik. Dukan waɗanda suke cikin Hukumar Mulki shafaffun Kiristoci ne.