Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta Samu Ƙaruwa
An sanar wa iyalin Bethel da ke Amirka da kuma Kanada a safiyar ranar Laraba, 5 ga Satumba, 2012 cewa an naɗa wani sabon mamban Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Sunansa Mark Sanderson ne, kuma ya soma hidima a wannan matsayin a ranar 1 ga Satumba, 2012.
Ɗan’uwa Sanderson ya yi girma a birnin San Diego da ke jihar Kalifoniya a Amirka, kuma iyayensa Shaidu ne. Ya yi baftisma a ranar 9 ga Fabrairu, 1975, kuma ya soma hidimar majagaba a ranar 1 ga Satumba, 1983 a lardin Saskatchewan da ke ƙasar Kanada. A watan Disamba na shekara ta 1990, ya sauke karatu a aji na bakwai na Makarantar Koyar da Masu Hidima (wadda yanzu ake kira Makarantar Koyar da ’Yan’uwa Maza Marasa Aure) a Amirka. An naɗa shi a matsayin majagaba na musamman a watan Afrilu na shekara ta 1991 a lardin Newfoundland a ƙasar Kanada. Bayan ya yi hidima a matsayin mataimakin mai kula da da’ira, sai aka tura shi zuwa ofishin da ke Kanada a watan Fabrairu na shekara ta 1997. A watan Nuwamba na 2000, aka tura shi zuwa ofishin reshen da ke Amirka ya yi hidima a Sashen Masu Ba da Bayani Game da Asibitoci, kuma daga baya ya yi hidima a Sashen Hidima.
A watan Satumba na 2008, Ɗan’uwa Sanderson ya halarci Makaranta don Waɗanda suke Kwamitin da ke Kula da Ofishin Reshe kuma bayan haka, aka naɗa shi a matsayin mamban Kwamitin da ke Kula da Ofishin Reshe na Ƙasar Filifin. Sai aka tura shi zuwa Amirka a watan Satumba na 2010, don ya yi hidima tare da Kwamitin Hidima na Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah.