Sababbi Waɗanda Aka Daɗa Cikin Hukumar Mulki
A RANAR Asabar 2 ga Oktoba, 1999, an kammala Taron Shekara Shekara na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania da wata sanarwa na ban mamaki. Mutane 10,594 da suka halarta ko kuma da suka ji akan waya sun yi murnan jin cewa an daɗa mutane huɗu ma Hukumar Mulki na Shaidun Jehovah. Sababbin, dukansu Kiristoci ne shafaffu, sune Samuel F. Herd; M. Stephen Lett; Guy H. Pierce; da David H. Splane.
• Samuel Herd ya soma aikin majagaba a 1958, kuma daga 1965 zuwa 1997, ya yi aikin mai kula mai ziyara na ɗa’ira da kuma na gunduma. Daga baya, shi da matarsa, Gloria, suka shiga cikin iyalin Bethel na United States, inda Ɗan’uwa Herd yake aiki a Sashen Hidima. Yana kuma taimaka ma Kwamitin Hidima.
• Stephen Lett ya soma aikin majagaba a Disamba 1966, kuma daga 1967 zuwa 1971, ya yi hidima a Bethel na United States. A Oktoba 1971, ya auri matarsa, Susan, kuma ya shiga hidimar majagaba ta musamman. Daga 1979 zuwa 1998, ya yi hidima ta mai kula mai ziyara na ɗa’ira. Tun Afrilu 1998, shi da Susan suka shiga cikin iyalin Bethel na United States. A wajen ya yi aiki a Sashen Hidima kuma yana taimaka ma Kwamitin Koyarwa.
• Guy Pierce ya yi iyali sai kuma shi da matarsa suka soma aikin majagaba a Afrilu 1982. Ya yi hidimar mai kula mai ziyara na ɗa’ira daga 1986 har zuwa 1997, lokacin da shi da matarsa, Penny, suka zama sashen iyalin Bethel na United States. Ɗan’uwa Pierce yana hidimar taimaka ma Kwamitin Lura da Masu Hidima.
• David Splane ya soma aikin majagaba a Satumba 1963. Ya sauƙe karatu a aji na 42 na Gilead, ya yi hidimar mai wa’azi a ƙasar waje a Senegal, a Afirka, sai kuma ya yi shekara 19 a aikin ziyara na ɗa’ira a Canada. Shi da matarsa, Linda, suna Bethel a United States tun 1990, inda Ɗan’uwa Splane ya yi aiki a sashen Hidima da kuma na Rubuce-Rubuce. Tun 1998, yana taimaka wa Kwamitin Rubuce-Rubuce.
Duka da sababbi guda huɗun, yanzu Hukumar Mulki ta ƙunshi C. W. Barber, J. E. Barr, M. G. Henschel, G. Lösch, T. Jaracz, K. F. Klein, A. D. Schroeder, L. A. Swingle, da D. Sydlik. Addu’an dukanmu ne cewa Jehovah ya albarkaci kuma ya ci gaba da ƙarfafa Hukumar Mulki, wadda yanzu ta yi girma, yayin da suke ci gaba da kula da ayyuka na mutanen Allah da suka kewaye duniya da kuma biyan bukatunsu na ruhaniya.