Ya ‘San Hanyar’
WANI memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah, mai suna Guy Hollis Pierce, ya gama rayuwarsa a duniya a ranar Talata ta 18 ga Maris, 2014. Yana da shekara 79 sa’ad da begensa na zama ɗaya cikin ’yan’uwan Kristi a sama ya tabbata.—Ibran. 2:10-12; 1 Bit. 3:18.
An haifi ɗan’uwa Guy Pierce a Auburn, jihar California, a Amirka, a ranar 6 ga Nuwamba, shekara ta 1934 kuma an yi masa baftisma a shekara ta 1955. Ya auri wata ’yar’uwa mai suna Penny a shekara 1977. Tare da wannan matar da yake ƙauna sosai suka haifi ’ya’ya. Saboda haka, yana bi da mutane kamar uba. Kafin shekara ta 1982 suna hidimar majagaba da himma, kuma a shekara ta 1986 ya zama mai kula da da’ira a Amirka, kuma ya yi shekaru goma sha ɗaya yana wannan hidimar.
A shekara ta 1997, Ɗan’uwa Guy Pierce da matarsa suka soma hidima a Bethel da ke Amirka. Ɗan’uwa Pierce ya yi aiki a Sashen Hidima, kuma a shekara ta 1998 aka naɗa shi mataimakin Kwamiti Mai Kula da Ma’aikata na Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. A ranar 2 ga watan Oktoba ne aka sanar da naɗin ɗan’uwa Pierce a matsayin memban Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah a taron shekara-shekara na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. A shekarun baya kafin ya mutu, ya yi aiki da Kwamiti Mai Kula da Ma’aikata da Kwamitin Rubuce-Rubuce da Kwamitin Rubuta Littattafai da Kwamitin Buga Littattafai da kuma Kwamitin Mai Kula.
Mutane daga wurare da al’adu dabam-dabam suna ƙaunarsa domin shi mai fara’a ne. Amma, mutane sun so shi musamman don shi mai ƙauna ne da sauƙin kai kuma yana son bin doka da ƙa’ida. Ƙari ga haka, yana da bangaskiya sosai ga Jehobah. Ɗan’uwa Guy Pierce, yana da tabbaci cewa ba abin da zai hana Jehobah ya cika alkawuransa, kuma burinsa ne ya sanar da wannan gaskiyar ga dukan mutane.
Ɗan’uwa Pierce ya bauta wa Jehobah da ƙwazo, yakan tashi da sassafe kuma ya yi aiki har dare. Ya yi tafiya zuwa wurare dabam-dabam a faɗin duniya don ya ƙarfafa ’yan’uwa. Ƙari ga haka, yawan aiki ba ya hana shi kasancewa da duk wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa da ke Bethel da kuma wasu da ke zuwa wurinsa don zumunci ko neman shawara ko kuma taimako. Bayan wasu shekaru, ’yan’uwa sukan tuna da halinsa na karɓan baƙi da fara’arsa da kuma yadda yake amfani da Littafi Mai Tsarki don ya ƙarfafa su.
Ɗan’uwanmu da abokinmu Pierce ya bar matarsa da ’ya’yansa shida. Ban da haka ma, yana da jikoki da kuma tattaɓa-kunnuwa da yawa. Ƙari ga haka, shi kamar uba ne ga yan’uwa da yawa. Ɗan’uwa Mark Sanderson, wanda shi ma memban Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ne ya yi jawabin jana’izar Ɗan’uwa Pierce a Bethel da ke Brooklyn a ranar Asabar ta 22 ga Maris, 2014. A jawabinsa, ya ambata begen Ɗan’uwa Pierce na zuwa sama kuma ya karanta abin da Yesu ya faɗa cewa: “A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa. . . . Kadan na tafi na shirya muku wuri kuma, sai in sake dawowa, in karɓe ku wurin kaina; domin wurin da ni ke, ku zauna kuma. Wurin da zan tafi kuma, kun san hanya.”—Yoh. 14:2-4.
Hakika, muna kewar Ɗan’uwa Pierce sosai. Duk da haka, muna farin ciki don ‘ya san hanyar’ zuwa inda zai “zauna” har abada.