Rahoton Taron Shekara-Shekara
Taron da Ya Bayyana Haɗin Kanmu da Kuma Shirye-Shirye Masu Ban Sha’awa
TARON shekara-shekara na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania yana zama lokacin farin ciki sosai. Taron shekara-shekara na 127 da aka yi a ranar Asabar, 1 ga Oktoba, 2011 ya ƙara nuna cewa hakan gaskiya ne ƙwarai. Baƙi da aka gayyata daga faɗin duniya sun taru a Majami’ar Taro na Shaidun Jehobah da ke Jersey City a jihar New Jersey, a ƙasar Amirka.
Ɗan’uwa Gerrit Lösch na Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya yi wa baƙi masu farin ciki maraba. Ya gaya wa baƙin da suka zo daga ƙasashe 85 cewa suna morar haɗin kan da babu irinsa a dukan duniya. Irin wannan haɗin kai shaida ce mai kyau da ke ɗaukaka Jehobah. Hakika, haɗin kai batu ne da aka sha maimaitawa a wannan taron.
ALBISHIRI DAGA ƘASAR MEZIKO
A sashen farko na taron, an ba da misalan wasu abubuwan da suka nuna cewa mutanen Jehobah suna da haɗin kai. Yanzu, ofishin reshe na ƙasar Meziko ne ke kula da aikin wa’azi a ƙasashe guda shida na nahiyar Amirka. Baltasar Perla ya gana da ’yan’uwa uku da ke hidima a Bethel na ƙasar Meziko game da wannan sabon tsarin. Suka ce yanzu ofishin reshe na Meziko yana da ’yan’uwa maza da mata daga al’adu da kuma ƙasashe dabam-dabam kuma suna jin daɗin yin hidima tare. Kamar dai Allah ya kawar da bambancin ’yan ƙasa da ke tsakaninsu.
Wani ƙalubale da wannan canjin ya kawo shi ne yadda za a taimaki masu shela sanin cewa ba a ware su daga ƙungiyar Jehobah ba duk da cewa babu ofishin reshe a ƙasashensu kuma. Don a cim ma wannan burin, an tanadar wa kowace ikilisiya har da waɗanda suke nesa sosai adireshin imel da za su riƙa aika saƙonni kai tsaye zuwa ofishin reshen.
LABARI DAGA ƘASAR JAPAN
Ɗan’uwa James Linton daga reshen Japan ya bayyana yadda girgizar ƙasa da tsunami da suka auku a ƙasar a watan Maris 2011 suka shafi ’yan’uwanmu. Shaidu da yawa su rasa ƙaunatattunsu da kuma dukiyoyinsu. Shaidun da bala’in bai shafe su ba sun ba da gudummawar gidaje guda 3,100 da kuma ɗarurruwan motoci. ’Yan’uwa da suka yi aiki tare da Kwamitin Gine-Gine na Yanki sun yi aiki sosai don su gyara gidajen ’yan’uwa. Mutane guda 1,700 ne suka ba da kansu don yin aiki a duk inda ake da bukata. Wani rukuni daga Amirka haɗe da wasu ’yan’uwa guda 575 sun taimaka da gyare-gyare Majami’un Mulki.
An mai da hankali sosai wajen ƙarfafa da ta’azantar da ’yan’uwan da wannan bala’in ya shafa. Dattawa sama da 400 ne suka ziyarci waɗannan ’yan’uwan don su ƙarfafa su da Littafi Mai Tsarki. Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta tura dattawa biyu masu ziyarar ofisoshin reshe daga hedkwatarmu na Amirka zuwa ƙasar domin su ba da ƙarfafawa. Ƙaunar da ’yan’uwa a dukan duniya suka nuna ya ƙarfafa su sosai.
NASARAR DA AKA YI A SHARI’A
Masu sauraro sun mai da hankali sosai yayin da Ɗan’uwa Stephen Hardy da ya zo daga reshen Biritaniya da kuma wasu ’yan’uwa suka tattauna nasarar da muka yi a sashen shari’a a kwanan baya bayan nan. Alal misali, gwamnatin ƙasar Faransa ta ce dole ne ofishin reshenmu da ke ƙasar su biya harajin dala miliyan 82, wato, naira biliyan 12. Amma, Kotun Turai na Kāre Hakkin Ɗan Adam ya ce hakan ba bisa doka ba ne. Kotun ya ce gwamnatin Faransa ta saɓa wa talifi na 9 na Kotun Turai wanda ke kāre ’yancin addini. Hukuncin da aka yanke ya nuna cewa wannan ba batun kuɗi ba ne don gwamnatin ba ta yarda cewa Shaidun Jehobah addini ne, saboda haka, tana so ta rufe ofishin reshen da ke wajen kuma ta hana Shaidun Jehobah yin wa’azi a ƙasar kuma tana kiran Shaidun Jehobah da wani mugun suna.
Kotun Turai na Kāre Hakkin Ɗan Adam ya ƙara yanke wani hukunci game da mu da ƙasar Armenia. Tun shekara ta 1965, Kotun ya ce kwamitin tsara dokar Kotun Turai bai ba wa mutane ’yancin ƙin shiga soja ba. Hukuma mafi iko a Kotun Turai, wato, Grand Chamber ta yanke hukunci cewa ya kamata kwamitin ya tsara dokar ’yancin ƙin shiga soja saboda dalilai na addini. Saboda sabuwar dokar, gwamnatocin ƙasashen Armenia da Azerbaijan da kuma Turkiya za su yi amfani da wannan dokar.
AIKIN GINE-GINE
Ɗan’uwa Guy Pierce na Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya ce duk waɗanda suka hallara suna marmarin jin labarin gine-gine da ke tafe a Jihar New York. Ya gabatar da bidiyo da ke nuna abubuwan da aka cim ma a birnin Wallkill na Patterson da kuma fili da aka saya a Birnin Warwick da kuma Tuxedo, a jihar New York. Za a kammala ginin wasu ɗakuna 300 a shekara ta 2014 a birnin Wallkill.
Ana shirye-shiryen fara gini a fili mai girman eka 248 da ke Warwick. Ɗan’uwa Pierce, ya ce: “Ko da yake ba mu san lallai mene ne nufin Jehobah game da Warwick ba, za mu fara gine-ginen a filin da niyyar mai da hedkwata na Shaidun Jehobah zuwa wurin.” Akwai shirye-shirye da ake yi na ajiye injuna da kuma kayan gine-gine a arewacin Warwick da ke da nisan mil shida daga ainihin filin ginin. “Muddin an ba mu izinin yin gini kuma muka fara, muna fata za mu gama ginin a cikin shekara huɗu. Sai kuma mu sayar kadararmu da ke Brooklyn,” in ji Ɗan’uwa Pierce.
Ɗan’uwa Pierce ya yi wannan tambayar: “Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta canja ra’ayinta ne game da kusatowar ƙunci mai girma ne?” Sai ya ba da amsar: “Sam.” Ya kuma ci gaba da cewa, “Idan ƙunci mai girma ya katse mana shirye-shiryenmu, abin farin cikin ne sosai!”
KA YI HANKALI DA ZAKI MAI RURI
Ɗan’uwa Stephen Lett, da shi ma ɗaya daga cikin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ne, ya tattauna 1 Bitrus 5:8 da ta ce: “Ku yi hankali shinfiɗe, ku yi zaman tsaro: magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” Ɗan’uwa Lett ya bayyana cewa idan muka san yadda zaki yake, za mu ƙara fahimtar kwatancin da Bitrus ya yi game da Iblis.
Tun da zakoki sun fi ’yan Adam ƙarfi da kuma sauri, kada mu yi ƙoƙarin faɗa ko kuma guje wa Shaiɗan ba tare da taimakon Allah ba. Muna bukatar taimakon Jehobah. (Isha. 40:31) A yawancin lokaci, zaki yana farauta da dare domin ya kama dabba cikin sauƙi, saboda haka, idan ba ma son Shaiɗan ya kama mu muna bukata mu buɗe idanunmu kuma mu fahimci yadda yake ƙoƙarin kawo mana hari. Shaiɗan ba shi da tausayi kuma zai so ya kashe mu kamar yadda zaki yake kashe barewa ko kuma maraƙin jakin dawa. Bayan ya ƙoshi da nama, ba za a ƙara gane dabbar kuma ba don yadda ya yayyaga ta. Hakazalika “ƙarshen” waɗanda Shaiɗan ya yaudara yakan “fi na farko muni.” (2 Bit. 2:20) Saboda haka, muna bukata mu daddage wa Shaiɗan sosai kuma mu manne wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da muka koya.—1 Bit. 5:9.
KA NUNA GODIYA DON GATAN DA KAKE DA SHI A ƘUNGIYAR JEHOBAH
Wanda ya ba da jawabi na gaba, Ɗan’uwa Samuel Herd na Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya ce, “Kowannenmu yana da gata a cikin ƙungiyar Jehobah.” Hakan yana nufin cewa dukan Kiristoci da suka ba da gaskiya ga hadayar fansa na Yesu suna iya bauta wa Allah a hanyar da zai amince. Ya kamata dukanmu mu nuna godiya don gatar da muke da shi a ƙungiyar Jehobah. Kamar Dauda, muna son mu “zauna cikin gidan Ubangiji dukan kwanakin [ranmu].”—Zab. 27:4.
Ɗan’uwa Herd ya ambata abin da ke cikin Zabura 92:12-14 kuma ya yi tambaya, “Ta yaya Jehobah yake sa mutanensa su yi nasara a rayuwa?” Sai kuma ya ba da amsar: “Allah yana tanadar mana da ƙarfafa da kāriya da kuma koyarwar gaskiya da ke kamar ruwa mai wartsake mutum. Ya kamata mu nuna godiya da gamsuwa saboda wannan kuma mu kuɗiri aniyar kasancewa a ƙungiyarsa har abada.”
KIRISTOCI NA GASKIYA SUNA DARAJA KALMAR ALLAH
Ɗan’uwa David Splane wanda shi ma yana cikin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya bayyana a jawabi na gaba cewa Kiristoci na gaskiya suna daraja Kalmar Allah. A ƙarni na farko, sun yi amfani da Nassosi don su magance matsalar da ta taso game da kaciya. (A. M. 15:16, 17) Amma a ƙarni na biyu, wasu da suke da’awa cewa su Kiristoci ne suka soma daraja falsafa na Girka fiye da Littafi Mai Tsarki. Daga baya, wasu suka koyar da ra’ayin sarakunan Roma da kuma waɗanda suka kira Ubanni na Coci maimakon koya wa mutane Littafi Mai Tsarki. Da hakan ne koyarwar ya soma yaɗuwa.
Ɗan’uwa Splane ya kuma yi magana a kan ɗaya cikin kwatance-kwatancen Yesu inda ya nuna cewa za a ci gaba da samun shafaffun Kiristoci a duniya don kāre bauta ta gaskiya. (Mat. 13:24-30) Alal misali, a ƙarnuka da yawa akwai waɗanda suka yi watsi da koyarwa da al’adun ƙarya, ko da yake, ba mu san lallai ko su wane ne ba. Waɗannan sun haɗa da Archbishop Agobard na Lyons na ƙarni na 9 da Peter na Bruys da Henry na Lausanne da Valdès (ko kuma Waldo) na ƙarni na 12 da John Wycliffe na ƙarni na 14 da William Tyndale na ƙarni na 16 da Henry Grew da kuma George Storrs na ƙarni na 19. A yau, Shaidun Jehobah sun ci gaba da ɗaukaka ƙa’idodin nassi kuma sun fahimci cewa Littafi Mai Tsarki ne tushen gaskiya. Shi ya sa Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta zaɓi Yohanna 17:17 wadda ta ce: “Maganarka ita ce gaskiya,” a matsayin jigon shekara ta 2012.
GYARE-GYARE MASU BAN SHA’AWA A MAKARANTUN LITTAFI MAI TSARKI
Ɗan’uwa Anthony Morris na Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya yi wata sanarwa da ta bayyana wasu gyare-gyaren da aka yi game da masu wa’azi a ƙasashen waje da kuma majagaba na musamman. Za a fara gudanar da Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata a wasu ƙasashe daga watan Satumba na 2012. An canja manufar Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead. Farawa daga watan Oktoba na bara, waɗanda ke hidima ta cikakken lokaci na musamman ne za su halarci Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead. Waɗannan sun haɗa da masu wa’azi a ƙasashen waje da ba su halarci makarantar ba tukuna da majagaba na musamman da masu kula masu ziyara da kuma masu hidima a Bethel. Za a tura waɗanda suke sauke karatu a makarantar su yi hidima a ofisoshin rassa ko su yi hidimar masu kula masu ziyara ko kuma a aika su yin wa’azi a manyan birane tare da ikilisiyoyi. Za su iya ƙarfafa da tallafa da kuma koyar da ’yan’uwa maza da mata da suke aiki tare da su a wuraren.
An sanar cewa daga 1 ga watan Janairu, 2012, wasu da suka halarci Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure da kuma Makarantar Littafi Mai Tsarki don Kiristoci Ma’aurata za su zama majagaba na musamman na ɗan lokaci. Don su yi wa’azi a yankunan da babu masu shela ko kuma ba su da yawa. Za su zama majagaba na musamman na shekara ɗaya. Bayan shekara uku, za a gaya wa waɗanda suka yi ƙoƙari sosai su ci gaba da hidimar majagaba na musamman.
An yi farin ciki sosai a lokacin taron shekara-shekara na 2011. Ƙungiyar Allah tana aiki tuƙuru don a yi aikin wa’azi a wurare da yawa a dukan duniya kuma don ta sa ’yan’uwa su kasance da haɗin kai a faɗin duniya. Addu’armu ita ce Jehobah ya albarkaci aikinmu kuma hakan ya sa a ɗaukaka kuma a yabe shi sosai.
[Akwati/Hotona a shafi na 18, 19]
GANAWA
An gana da mata biyar na mambobin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah da suka rasu. ’Yar’uwa Marina Sydlik da Edith Suiter da Melita Jaracz da Melba Barry da kuma Sydney Barber sun bayyana yadda suka soma bauta wa Jehobah kuma suka soma hidima ta cikakken lokaci. Kowannensu ta yi magana a kan abubuwa da halaye masu kyau da ta tuna game da mai-gidanta da yadda suka ji daɗin yin hidima tare. Bayan ganawar, waɗanda suka hallara suka rera musu waƙa ta 86, mai jigo “Faithful Women, Christian Sisters.”
[Hotona]
(A sama) Daniel da Marina Sydlik; Grant da Edith Suiter; Theodore da Melita Jaracz
(A ƙasa) Lloyd da Melba Barry; Carey da Sydney Barber
[Taswira a shafi na 16]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
Ofishin reshe na ƙasar Meziko ne ke kula da aikin wa’azi a ƙasashe guda shida
MEZIKO
GUATEMALA
HONDURAS
EL SALVADOR
NICARAGUA
COSTA RICA
PANAMA
[Hoto a shafi na 17]
Hoton hedkwata na Shaidun Jehobah da za a gina a Warwick, New York