Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 8/15 pp. 18-21
  • Taron da Ba Za a Taɓa Mantawa Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Taron da Ba Za a Taɓa Mantawa Ba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Rahotanni Masu Ban Ƙarfafa da kuma Ganawa Masu Daɗaɗa Zuciya
  • Wasu Jawabai da ’Yan Hukumar Mulki Suka Ba Da
  • Sababbi da Aka Haɗa Cikin Hukumar Mulki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Sababbi Waɗanda Aka Daɗa Cikin Hukumar Mulki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Taron da Ya Bayyana Haɗin Kanmu da Kuma Shirye-Shirye Masu Ban Sha’awa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta Samu Ƙaruwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 8/15 pp. 18-21

Taron da Ba Za a Taɓa Mantawa Ba

“SA’AD DA aka idar da wannan taron, za ka ce, ‘Hakika ba za a taɓa mantawa da wannan taro na shekara-shekara ba!’” Ta wajen faɗan waɗannan kalaman, ɗan’uwa Stephen Lett na Hukumar Mulki na Shaidun Jehobah ya daɗa sa taron jama’ar su yi ɗokin abin da za a yi a taron. Sun taru don taron shekara-shekara na 126 na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania da aka yi a ranar 2 ga Oktoba, 2010, a Majami’ar Taro na Shaidun Jehobah da ke birnin Jersey, New Jersey a Amirka. Waɗanne abubuwa masu muhimmanci ne aka nanata a wannan taro na musamman?

Ɗan’uwa Lett ya ba da jawabin buɗewa mai daɗaɗawa game da karusa na samaniya na Jehobah kamar yadda aka bayyana a littafin Ezekiel. Wannan babbar mota mai daraja tana alamta ƙungiyar Allah, kuma Jehobah ne yake ja-gorarta. Ɗan’uwa Lett ya ce, sashenta na samaniya da ya haɗa da halittu na ruhu yana gudu kamar saurin walƙiya, wato, sauri na tunanin Jehobah. Hakanan ma, sashen ƙungiyar Jehobah Allah na duniya yana samun ci gaba. Ɗan’uwa Lett ya ambata wasu abubuwa da suke faruwa a sashe na zahiri na ƙungiyar Allah a kwana kwanan nan.

Alal misali, an haɗa wasu ofisoshin rassa, kuma hakan zai sa mutane da yawa da suke hidima a Bethel a dā a waɗannan ƙasashen su mai da hankali ga yin wa’azi. Ɗan’uwa Lett ya aririci masu sauraro su ci gaba da yin addu’a cewa Hukumar Mulki ta ci gaba da kasancewa da aminci da kuma hikima a matsayin wakilan rukunin bawa.—Mat. 24:45-47.

Rahotanni Masu Ban Ƙarfafa da kuma Ganawa Masu Daɗaɗa Zuciya

Ɗan’uwa Tab Honsberger wanda yake hidima a cikin Kwamitin Reshe na Haiti, ya ba da rahoto mai taɓa zuciya a kan sakamakon girgizar ƙasa wadda aka yi a ranar 12 ga Janairu, 2010, wadda aka kimanta ta kashe mutane 300,000 a wannan ƙasar. Ya faɗa cewa limamai suna gaya wa mutane cewa Allah yana wa waɗanda suka mutu horo domin rashin bangaskiyarsu kuma ya kāre nagargarun mutane. Duk da haka, dubban masu aikata laifi da aka kama sun gudu sa’ad da garukan fursunan suka rushe don girgizar ƙasar. Mutanen Haiti da yawa masu zukatan kirki suna samun ta’aziyya wajen koyon gaskiya game da dalilin da ya sa ake wahala sosai a zamaninmu. Ɗan’uwan Honsberger ya yi ƙaulin wani ɗan’uwan ɗan Haiti mai aminci wanda ya yi rashin matarsa a wannan bala’in yana cewa: “Ina kuka har yau. Ban san tsawon lokacin da zan yi makoki ba, amma ina farin cikin ganin ƙauna ta ƙungiyar Jehobah. Ina da bege, kuma na ƙuduri aniya na taimaka wa mutane su samu wannan begen.”

Ɗan’uwa Mark Sanderson, wanda yanzu yana cikin iyalin Bethel da ke Brooklyn, ya ba da rahoto game da ƙasar Filifin. Da yake shi a dā yana cikin Kwamitin Reshe a ƙasar, ya yi farin cikin yin magana game da ƙolin 32 na masu shelar Mulki da ƙasar ke samu a kai a kai da kuma yadda nazarin Littafi Mai Tsarki ya ɗara adadin masu shela. Ya yi magana game da ɗan’uwa mai suna Miguel wanda aka kashe ɗan ɗansa. Miguel ya yi fama don ya ga an hukunta wanda ya yi kisan kuma an saka shi a gidan yari. Bayan haka, Miguel ya haɗu da mai kisan sa’ad da yake wa’azi a kurkuku. Ko da yake Miguel bai saki jiki ba, sai ya yi wa mutumin magana da hankali da kuma kirki. Daga baya ya yi nazari da mutumin, wanda ya samu ci gaba kuma yana ƙaunar Jehobah. Yanzu ya yi baftisma. Miguel abokinsa ne na kud da kud kuma yana ƙoƙari ya ga cewa an sake sabon ɗan’uwansa daga kurkuku.a

A tsarin ayyuka na gaba, ɗan’uwa Mark Noumair wanda malami ne a Sashen Makarantun Hidima ta Allah ya gudanar da ganawa. Ya gana da ma’aurata guda uku Alex da Sarah Reinmueller, David da Krista Schafer da kuma Robert da Ketra Ciranko. Alex Reinmueller, mataimakin Kwamitin Buga Littattafai ya ba da labarin yadda ya mai da gaskiya tasa a sa’ad da yake hidimar majagaba a Kanada a lokacin da yake ɗan shekara 15, sau da yawa yana tafiya wa’azi shi kaɗai. Sa’ad da aka ce ya faɗi wanda ya fi kasancewa da tasiri mai kyau a gare shi a Bethel, Ɗan’uwa Reinmueller ya ambata mazaje uku masu aminci, kuma ya nuna yadda kowannensu ya taimaka masa ya yi girma a ruhaniya. Matarsa, Sarah ta faɗi game da abuta da ta yi da wata ’yar’uwa wadda ta jimre shekaru da yawa a kurkuku a ƙasar Sin don imaninta. Sarah ta ce ta koya yin dogara ga Jehobah ta addu’a na kanta.

David Schafer, wanda mataimakin Kwamitin Koyarwa ne, ya yaba wa mahaifiyarsa don bangaskiyarta mai ƙarfi kuma ya faɗi game da ’yan’uwa a cikin ikilisiya masu aikin katako da suka taimaka masa ya yi hidimar majagaba na ɗan lokaci sa’ad da yake matashi. Matarsa, Krista ta yi magana da farin ciki game da yadda tsofaffi da suke Bethel masu “aminci cikin ƙanƙanin abu” kamar yadda Yesu ya ce, sun kasance da tasiri mai kyau a gare ta.—Luk 16:10.

Robert Ciranko, mataimakin Kwamitin Rubuce-Rubuce, ya tuna da kakanninsa huɗu, waɗanda bakin haure ne a ƙasar Hungary da kuma Kiristoci shafaffu. Sa’ad da yake yaro, manyan tarurruka da ya halarta a shekarun 1950 zuwa 1959 sun burge shi sosai kuma ya koya cewa ƙungiyar Jehobah ta fi ikilisiyarsu girma sosai. Matarsa Ketra, ta faɗi yadda ta koyi kasancewa da aminci sa’ad da take hidimar majagaba a cikin ikilisiyar da ke cike da ’yan ridda da wasu matsaloli. Ta jimre kuma daga baya aka tura ta hidima a matsayin majagaba na musamman zuwa ikilisiya inda haɗin kansu ya taɓa zuciyarta sosai.

Sai ɗan’uwa Manfred Tonak ya ba da rahoto game da ƙasar Habasha. Wannan ƙasar ta kasance tun zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, kuma yanzu an yi mata albarka da masu shelar bishara fiye da 9,000. Yawancinsu suna zama a ko kuma kusa da babban birnin, Addis Ababa. Saboda haka, ƙauyuka suna bukatar ƙarin taimako. Don a biya wannan bukatar, an gayyaci Shaidu ’yan Habasha da suke zaune a wasu ƙasashe su zo don su yi wa’azi a wasu ƙauyuka na ƙasar. Mutane da yawa sun zo, sun ƙarfafa Shaidu da suke yankin, kuma sun samu waɗanda suka saurari saƙon.

Wani tsari na musamman shi ne magana daki-daki da aka yi game da Shaidun Jehobah a ƙasar Rasha da kuma shari’o’i da suka yi shekaru da yawa. Aulis Bergdahl wanda yake Kwamitin Reshe a ƙasar Rasha ya ba da tarihin tsananta wa Shaidu da aka yi a ƙasar Rasha, musamman a birnin Moscow. Philip Brumley wanda yake Sashen Shari’a a reshen Amirka ya ba da labarin abubuwa masu ban mamaki da suka faru kwanan nan sa’ad da Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam ya yi hukunci tara da aka kai game da Shaidu. Kotun ya ga cewa duk hukunci tara da aka kai ba gaskiya ba ce, kuma a shari’o’i da yawa da kotun ya yi sun yi ƙoƙari sosai su bayyana dalilin da ya sa ƙarar da suka kai ba daidai ba ne. Ko da yake har ila ana jiran sakamakon, Ɗan’uwa Brumley ya sa rai cewa hukunci da Kotun ya yanke zai iya shafan shari’o’in da ake yi a wasu ƙasashe.

Bayan wannan labarai masu ban farin ciki, Ɗan’uwa Lett ya sanar cewa Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam ya ga ya dace ya yi hukunci a kan ƙarar gwamnatin ƙasar Faransa da Shaidun Jehobah suka kai game da haraji mai yawa da Shaidu suka daɗe suna biya. Wannan Kotun da ake daraja sosai yana saurarar kaɗan cikin ƙara da aka kai masa. Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam ya yi shari’o’i 39 da suka shafi Shaidun Jehobah, kuma Shaidun sun ci nasarori 37 a cikinsu. Ɗan’uwa Lett ya ƙarfafa dukan mutanen Allah su yi addu’a ga Jehobah Allah saboda wannan batun.

Richard Morlan, mai koyarwa a Makaranta na Dattawan Ikilisiya ne ya ba da rahoto na ƙarshe. Ya yi magana da ƙwazo game da makarantar da kuma yadda dattawa da suka halarta suka nuna godiya.

Wasu Jawabai da ’Yan Hukumar Mulki Suka Ba Da

Ɗan’uwa Guy Pierce na Hukumar Mulki ya ba da jawabi da ya motsa zuciya da ya mai da hankali ga jigon shekara ta 2011, ‘Ka Nemi Mafaka a Sunan Jehobah.’ (Zaf. 3:12) Ya bayyana cewa ko da yake a hanyoyi da yawa yanzu lokacin farin ciki ne ga mutanen Jehobah, amma lokaci ne kuma na mai da hankali da kuma natsuwa. Babbar ranar Jehobah ta kusa, duk da haka, mutane sun ci gaba da neman mafaka a addinin ƙarya da ƙungiyoyin siyasa da arziki da rashin mai da hankali ga abubuwa da ke faruwa a duniya da kuma sauransu. Don mu sami mafaka ta gaske, muna bukatar mu kira sunan Jehobah, wanda ya haɗa da saninsa da ba shi ladabi sosai da dogara ga Wanda sunan nan yake wakilta da kuma ƙaunarsa da kome da muke da shi.

Sai Ɗan’uwa David Splane na Hukumar Mulki ya ba da jawabi mai sa tunani, mai jigo “Ka Shiga Cikin Hutun Allah Kuwa?” Ya nuna cewa hutun Allah ba ya nufin rashin aiki, tun da yake Jehobah da Ɗansa suna “aiki” a dukan ranar hutun nan ta alama domin su yi nasara wajen cika nufin Allah don abubuwa da aka halitta game da duniya. (Yoh. 5:17) To, ta yaya za mu iya shiga cikin hutun Allah? Ƙin yin zunubi da kafa adalci namu maimako na Yesu Kristi da kuma hadayarsa ta fansa suna cikin abubuwan da za mu yi. Muna bukatar mu kasance da imani kuma mu yi rayuwa da ta jitu da nufin Allah, mu kuma yi kome da za mu iya don mu cika wannan nufin. A wasu lokatai, hakan yana iya kasancewa da ƙalubale, amma muna bukatar mu amince da wannan gargaɗin kuma mu ba da haɗin kai ga ja-gorar da muke samu daga ƙungiyar Jehobah. Ɗan’uwa Splane ya aririce masu sauraro su yi kome da za su iya yi don su shiga cikin hutun Allah.

Jigon jawabi na ƙarshe da ɗan’uwa Anthony Morris na Hukumar Mulki ya ba da shi ne, “Mene ne Muke Jira?” Ɗan’uwa Morris, da gaggawa da kuma daɗaɗawa ya tuna wa masu sauraro game da cikar annabce-annabce da za su faru nan gaba, kuma dukan ’yan’uwa masu aminci suna ɗokin jiran hakan ya faru. Wannan ya haɗa da kukar “kwanciyar rai da lafiya” da kuma halakar addinin ƙarya. (1 Tas. 5:2, 3; R. Yoh. 17:15-17) Ɗan’uwa Morris ya ba da kashedi cewa kada mu ce, “Wannan Armageddon ne,” ga abubuwa da muke gani a ƙofofin labarai da ba sa cika irin waɗannan annabce-annabce. Ya ce mu kasance da farin ciki da haƙuri da kuma halin jira da aka kwatanta a Mikah 7:7. “Amma, ya aririce kowa ya kasance da dangantaka na kud da kud da Hukumar Mulki, yadda sojoji za su shiga cikin filin daga.” Ya ce “bari zuciyarku ta yi gaba gaɗi, dukanku masu-sauraro ga Ubangiji.”—Zab. 31:24.

Da aka kammala, an yi wasu sanarwa da ba za a taɓa mantawa ba. Ɗan’uwa Geoffrey Jackson na Hukumar Mulki ya sanar cewa za a gwada Fitowar Hasumiyar Tsaro ta Nazari a Turanci Mai Sauƙi, don waɗanda ba su iya karanta Turanci sosai ba. Sai Ɗan’uwa Stephen Lett ya sanar cewa Hukumar Mulki za ta shirya a riƙa yi wa masu kula da gunduma da matansu a ƙasar Amirka ziyarar ƙarfafa. Ya kuma sanar cewa Makarantar Koyar da Masu Hidima za ta zama Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure. Ya kuma sanar da sabuwar makaranta da aka kira Makarantar Littafi Mai Tsarki Don ’Yan’uwa Ma’aurata. Wannan makaranta za ta ba ma’aurata ƙarin koyarwa don su ƙara kasancewa da amfani ga ƙungiyar Jehobah. Ɗan’uwa Lett ya kuma sanar cewa za a riƙa yin Makaranta don Masu Kula Masu Ziyara da Matansu da kuma Makaranta don ’Yan Kwamitin Reshe da Matansu sau biyu kowace shekara a Patterson don waɗanda suka halarci a dā su sake halarta.

Ɗan’uwa John E. Barr, mai shekara 97, wanda ya daɗe yana cikin Hukumar Mulki ya yi addu’ar kammalawa mai taɓa zuciya.b A ƙarshen taron, kowa ya ji cewa wannan taro ne da ba za a taɓa mantawa ba.

[Hasiya]

a Ka duba 2011 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 62-63.

b Ɗan’uwa Barr ya gama hidimarsa a duniya a ranar 4 ga Disamba, 2010.

[Bayanin da ke shafi na 19]

Dukan waɗanda suka halarci taron sun more ganawa da aka yi

[Bayanin da ke shafi na 20]

Jehobah ya albarkaci aikin wa’azi a ƙasar Habasha

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba