-
Dukan Kiristoci Ne Suke Bin Umurnin Kristi?Hasumiyar Tsaro—2012 | 1 Yuli
-
-
Dukan Kiristoci Ne Suke Bin Umurnin Kristi?
KIRISTOCI guda nawa ne suke duniya? Littafin nan Atlas of Global Christianity ya nuna cewa a shekara ta 2010, akwai Kiristoci wajen biliyan 2.3 a faɗin duniya. Wannan littafin ya kuma nuna cewa waɗannan Kiristocin sun kasu ne zuwa ɗarika sama da 41,000, kuma dukansu suna da tasu koyarwa da kuma irin ɗabi’ar da suke bi. Shi ya sa mutane da dama suka rikice ko kuma suka daina bin addini domin akwai ɗariku dabam-dabam masu kiran kansu “Kirista.” Wasu suna mamaki, ‘Shin dukan mutanen da suke da’awar cewa su Kiristoci ne suke bin umurnin Kristi?’
Bari mu duba batun daga wani ɓangare dabam. Matafiyin da zai shiga ƙasarsu daga wata ƙasa yana bukatar ya nuna wa ma’aikacin gwamnati cewa shi ɗan ƙasa ne. Zai yi hakan ne ta wajen nuna katin shaida ko fasfo. Hakazalika, Kirista na gaskiya yana bukatar ya tabbatar da bangaskiyarsa ga Kristi ba da baki kawai ba. Yana bukatar ƙarin shaida. Mece ce shaidar?
An soma amfani da kalmar nan “Kirista” bayan shekara ta 44 A.Z. Ɗan tarihi Luka ya rubuta cewa: “A cikin Antakiya fa aka fara ce da masu-bi Krista.” (Ayyukan Manzanni 11:26) Waɗannan mutanen da aka kira Kiristoci almajiran Kristi ne. Ta yaya mutum yake zama almajirin Yesu Kristi? Littafin nan The New International Dictionary of New Testament Theology ya yi bayani: “Bin Yesu a matsayin almajiri yana nufin cewa mutum zai sadaukar da ransa ba tare da wani sharaɗi ba . . . har iyakacin rayuwar[sa].” Saboda haka, Kirista na gaskiya shi ne mutumin da ke bin koyarwa da umurnin Yesu, sawu da kafa.
Zai yiwu ne a sami irin waɗannan mutanen a tsakanin mutane da yawa da suke da’awar cewa su Kiristoci ne a yau? Mene ne Yesu da kansa ya ce zai zama alamar da zai sa a gane mabiyansa na gaskiya? Muna gayyatarka ka bincika yadda Littafi Mai Tsarki ya amsa waɗannan tambayoyin. A talifofi na gaba, za mu bincika furuci guda biyar da Yesu Kristi ya yi waɗanda za su taimaka mana mu gane mabiyansa na gaskiya. Za mu bincika yadda Kiristoci a ƙarni na farko suka nuna cewa suna da irin waɗannan halayen. Za mu kuma bincika ko su wane ne suke nuna irin waɗannan halayen a cikin mutane masu yawa da suke da’awar cewa su Kiristoci ne a yau.
-
-
‘Ku Zauna Cikin Maganata’Hasumiyar Tsaro—2012 | 1 Yuli
-
-
‘Ku Zauna Cikin Maganata’
‘Idan kun zauna cikin maganata, ku ne almajiraina na gaske; za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ’yantar da ku.’—YOHANNA 8:31, 32.
Abin da Hakan Yake Nufi: ‘Maganar’ Yesu tana nufin koyarwarsa wadda ta fito daga wurin Allah. Yesu ya ce: “Amma Uba wanda ya aiko ni, shi ne ya ba ni umurni, abin da zan faɗi, da magana da zan yi kuma.” (Yohanna 12:49) Sa’ad da yake yin addu’a ga Ubansa da ke sama, Jehobah Allah, Yesu ya ce: “Maganarka ita ce gaskiya.” Yana yawan kaulin Kalmar Allah don ya goyi bayan abin da yake koyarwa. (Yohanna 17:17; Matta 4:4, 7, 10) Saboda haka, Kiristoci na gaskiya suna ‘zaune cikin maganarsa,’ wato sun karɓi Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, a matsayin “gaskiya” da kuma tushen imaninsu har da abubuwan da suke yi.
Yadda Kiristoci na Farko Suka Yi Abin da Yesu Ya Ce: Kamar Yesu, manzo Bulus ya daraja Kalmar Allah. Ya rubuta: “Kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne.” (2 Timotawus 3:16) Mazan da aka naɗa su koyar da ’yan’uwansu Kiristoci suna bukatar su riƙe ‘tabbatacciyar maganar Allah kankan.’ (Titus 1:7, 9, Littafi Mai Tsarki) An gargaɗi Kiristoci na farko su ƙi ‘ilimi da ruɗi na banza, bisa al’adar mutane, bisa ga al’adun duniya, ba bisa ga koyarwar Kristi ba.’—Kolosiyawa 2:8.
Su Wane Ne Suke Bin Wannan Misalin a Yau? Dogmatic Constitution on Divine Revelation, na Batikan wanda aka soma amfani da shi a shekara ta 1965 kuma aka yi kaulinsa a littafin nan Catechism of the Catholic Church, ya ce: “Ba daga Nassi Mai Tsarki kaɗai ba ne aka ɗauko dukan abubuwan da Cocin [Katolika] ta gaskata da su ba. Saboda haka, dole ne a ɗauki al’ada mai tsarki da muhimmanci kamar yadda aka ɗauki Nassi Mai Tsarki da muhimmanci.” Wani talifi a cikin jaridar Maclean’s ya yi kaulin wata fasto a Toronto, tana cewa: “Me za mu yi da ja-gorancin wani mai ‘neman sauyi’ da ya rayu shekaru dubu biyu da suka shige? Muna da namu ra’ayoyin masu kyau sosai amma koyarwar Yesu da kuma Nassi suna yi musu zagon ƙasa.”
Game da Shaidun Jehobah, littafin New Catholic Encyclopedia ya ce: “Sun ɗauki Littafi Mai Tsarki a matsayin ainihin tushen imaninsu da abubuwan da suke yi.” Kwanan baya, wani mutumi a ƙasar Kyanada ya katse maganar wata Mashaidiyar Jehobah sa’ad da take son ta gabatar da kanta. Ya nuna Littafi Mai Tsarki da ke hannunta, kuma ya ce, “Na san ko ke wace ce, domin tambarinku.”
-
-
“Su Ba na Duniya Ba Ne”Hasumiyar Tsaro—2012 | 1 Yuli
-
-
“Su Ba na Duniya Ba Ne”
“Duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne.”—YOHANNA 17:14.
Abin da Hakan Yake Nufi: Babu ruwan Yesu da siyasa da kuma rikicin da mutane ke yi a zamaninsa, domin shi ba na duniya ba ne. Yesu ya ce, ‘da mulkina na wannan duniya ne, da ma’aikatana za su yi yaƙi, domin kada a bashe ni cikin hannun Yahudawa, amma yanzu mulkina ba daga nan yake ba.’ (Yohanna 18:36) Ya kuma umurci mabiyansa su guji halaye da maganganun da Kalmar Allah ta yi tir da su.—Matta 20:25-27.
Yadda Kiristoci na Farko Suka Yi Abin da Yesu Ya Ce: Jonathan Dymond, marubucin batutuwan da suka shafi addini, ya ce Kiristoci a ƙarni na farko sun “ƙi yin [yaƙi]; ko da hakan zai sa a kunyata su, a jefa su kurkuku, ko kuma a kashe su.” Sun gwammace su sha wahala da su yi yaƙi. Ɗabi’arsu ta kuma bambanta su da sauran mutane. An gaya wa Kiristoci: “Wannan kuwa suna maishe shi abin mamaki da ba ku yi gudu tare da su zuwa cikin haukar lalata irin tasu, suna aibatanku.” (1 Bitrus 4:4) Will Durant wani ɗan tarihi ya rubuta cewa “arna masu hauƙan son annashuwa suna jin haushin [Kiristoci] domin suna yin nagarta kuma suna da tsoron Allah.”
Su Wane Ne Suke Bin Wannan Misalin a Yau? Game da tsaka-tsakanci na Kirista, littafin nan New Catholic Encyclopedia ya ce: “Ƙin ɗaukan makami laifi ne.” Wani talifi a cikin jaridar Reformierte Presse ya ambata cewa rahoton da aka samo daga Hakkin ’Yan Afirka, wadda ƙungiya ce ta kāre hakkin ’yan Adam, ta tabbatar da cewa dukan coci ne suke da hannu a kisan ƙare-dangi da aka yi Ruwanda a shekara ta 1994, amma “ban da Shaidun Jehobah.”
Sa’ad da yake tattauna kisan ƙare-dangi da Nazi ta yi wa Yahudawa, malamin wata babbar makaranta ya koka cewa “babu wani rukuni ko ƙungiyar mutanen da ta fito ta yi Allah-wadai da irin ƙarya da rashin imani da kuma ayyukan masha’a da aka tabka.” Amma bayan ya tuntuɓi Gidan Tuna Tarihin Kisan Ƙare Dangi da ke Amirka, malamin ya rubuta cewa: “Na samu amsar tambayata.” Ya samu labarin cewa Shaidun Jehobah sun riƙe imaninsu duk da wahalar da suka sha.
Ɗabi’arsu a matsayin Kiristoci kuma fa? Jaridar nan U.S. Catholic ta ce: “Yawancin matasan da ke Katolika ba su amince ba da koyarwar cocinsu wadda ta ce laifi ne mutum ya yi jima’i kafin ya yi aure da kuma zama tare tsakanin mace da namiji ba tare da sun yi aure ba.” Ya yi kaulin wani dikon da ya ce: “Fiye da kashi 50 daga cikin mutanen da suka zo don a ɗaura musu aure, suna zama ne tare kafin a ɗaura musu aure.” Littafin nan The New Encyclopædia Britannica ya lura cewa Shaidun Jehobah “ba sa sakaci da batun kasancewa da ɗabi’a mai kyau.”
-
-
‘Ku Ƙaunaci Juna’Hasumiyar Tsaro—2012 | 1 Yuli
-
-
‘Ku Ƙaunaci Juna’
“Sabuwar doka na ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna. Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.”—YOHANNA 13:34, 35.
Abin da Hakan Yake Nufi: Kristi ya gaya wa mabiyansa su ƙaunaci juna kamar yadda ya ƙaunace su. Ta yaya Yesu ya ƙaunace su? Ya so dukan mutane duk da cewa nuna bambanci ga mata da kuma mutanen wata ƙasa ya zama ruwan dare a zamaninsa. (Yohanna 4:7-10) Ƙauna ce ta sa Yesu ya sadaukar da lokacinsa da kurazarinsa da annashuwarsa don ya taimaki mutane. (Markus 6:30-34) A ƙarshe, Kristi ya nuna ƙauna a hanya mafi girma. Ya ce: “Ni ne makiyayi mai-kyau: makiyayi mai-kyau yakan bada ransa domin tumaki.”—Yohanna 10:11.
Yadda Kiristoci na Farko Suka Yi Abin da Yesu Ya Ce: A ƙarni na farko, Kiristoci sun kira junansu “ɗan’uwa” ko “’yar’uwa.” (Filimon 1, 2) Akwai mutanen al’umma iri-iri a cikin ikilisiyar Kirista, domin sun gaskata cewa “ba wani bambanci tsakanin Bayahude da Ba’al’umme. Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa.” (Romawa 10:11, 12) Bayan Fentakos 33 A.Z., almajiran da ke Urushalima “suka sayar da abin mulkinsu, da dukiyarsu, suka rarraba wa jama’a bisa ga bukatar kowa.” Me ya sa? Saboda sababbin da suka yi baftisma su zauna a Urushalima don su “lizima a cikin koyarwar manzanni.” (Ayyukan Manzanni 2:41-45) Me ya sa suka yi hakan? Kusan shekara 200 bayan mutuwar manzanni, Tertullian ya yi kaulin abin da wasu suka ce game da Kiristoci: “Suna ƙaunar juna . . . kuma a shirye suke su mutu domin junansu.”
Su Wane Ne Suke Bin Wannan Misalin a Yau? Littafin nan The History of the Decline and Fall of the Roman Empire (1837) ya lura cewa tun ƙarnuka da dama, waɗanda suke da’awar cewa su Kiristoci ne sun “tsananta wa junansu sosai fiye da yadda arna [marasa bi] suka tsananta musu.” Wani bincike na kwanan nan a Amirka ya gano cewa mutane da yawa da suka ce suna bin addini sawu da kafa, kuma yawancinsu suna da’awar cewa su Kiristoci ne, suna nuna wariyar al’umma. A yawancin lokaci, masu zuwa coci ɗaya ba sa cuɗanya da ’yan ɗarikarsu da ke wata ƙasa, kuma sa’ad da bukata ta taso, ba sa taimaka wa juna.
A shekara ta 2004 bayan jerin mahaukaciyar gugguwa da ruwan sama da aka yi a Florida sau huɗu a cikin wata biyu, shugaban Kwamitin Ba da Agaji na Florida ya kai ziyara don ya tabbatar da cewa an yi amfani da kayan da suka kai yadda ya kamata. Ya ce babu wata rukuni da take da tsari mai kyau kamar Shaidun Jehobah, kuma ya yi alkawarin yi musu tanadin duk wani abin da suke bukata. A shekara ta 1997, rukunin ’yan agaji na Shaidun Jehobah sun kai wa ’yan’uwansu Kiristoci mabukata tare da wasu mutanen da ke Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango magani da abinci da tufafi. Shaidu a ƙasar Turai sun ba da gudummawar kayayyaki da suka kai dala miliyan ɗaya na Amirka.
-
-
‘Na Bayyana Sunanka ga Mutane’Hasumiyar Tsaro—2012 | 1 Yuli
-
-
‘Na Bayyana Sunanka ga Mutane’
‘Na bayyana sunanka ga mutane waɗanda ka ba ni daga cikin duniya; na sanar masu da sunanka, zan kuma sanar da shi.’—YOHANNA 17:6, 26.
Abin da Hakan Yake Nufi: Yesu ya sanar da sunan Allah ta wajen yin amfani da shi a hidimarsa. Sa’ad da Yesu ya karanta Nassi, kamar yadda ya saba, ya ambata sunan Allah. (Luka 4:16-21a) Ya koya wa mabiyansa su yi addu’a cewa “Uba, a tsarkake sunanka mulkinka shi zo.”—Luka 11:2.
Yadda Kiristoci na Farko Suka Yi Abin da Yesu Ya Ce: Manzo Bitrus ya gaya wa dattawan da ke Urushalima cewa Allah ya jawo jama’a daga cikin al’ummai “domin sunansa.” (Ayyukan Manzanni 15:14) Manzanni da sauran Kiristoci sun yi wa’azi cewa “dukan wanda za ya kira bisa sunan Ubangiji za ya tsira.” (Ayyukan Manzanni 2:21; Romawa 10:13) Kuma sun yi amfani da sunan Allah a rubutunsu. Wani tarin dokokin Yahudawa da aka kammala rubutawa wajen shekara ta 300 A.Z. ya ce game da littattafan Kiristoci da masu hamayya suka ƙona: “Sun ƙona dukan littattafan marubutan Linjila da kuma littattafan minim [waɗanda ake tunanin cewa Kiristoci ne Yahudawa]. Sun ƙona su ƙurmus . . . har da sunan Allah da ke cikin littattafan.”
Su Wane Ne Suke Bin Wannan Misalin a Yau? Revised Standard Version, wanda Littafi Mai Tsarki ne da aka wallafa da izinin National Council of the Churches of Christ in the United States ya ambata a gabatarwarsa cewa: “Kafin zamanin Kristi, masu bin Yahudanci sun daina amfani da sunan Allah domin shi kaɗai ne Allah, saboda haka babu wani muhimmancin yin amfani da sunan da zai bambanta shi da wasu alloli; kuma hakan bai da wani amfani ga bangaskiyar Cocin Kirista.” Saboda haka, suka sauya sunan Allah da lakabin nan “UBANGIJI.” Kwanan baya, Paparoma ya umurci limamansa cewa: “Kada ku yi amfani ko kuma ku furta sunan Allah da aka rubuta da baƙaƙe huɗu, wato, YHWHb a waƙoƙi da kuma addu’o’i.”
Su wane ne suke amfani da sunan Allah kuma suke gaya wa mutane game da shi a yau? Sa’ad da Sergey yake matashi a ƙasar Kyrgyzstan, ya kalli wani fim ɗin da ya nuna cewa Jehobah ne sunan Allah. Amma bai sake jin sunan ba har tsawon shekara 10. Bayan Sergey ya kaura zuwa Amirka, Shaidun Jehobah biyu suka ziyarce shi a gidansa kuma suka nuna masa sunan Allah a Littafi Mai Tsarki. Sergey ya yi farin cikin samun rukunin da ke amfani da sunan nan Jehobah. A ƙamus ɗin Webster’s Third New International Dictionary, a ƙarƙashin “Jehovah God” (Jehobah Allah) an bayyana cewa “shi kaɗai ne mafi iko da Shaidun Jehobah suka sani kuma shi kaɗai ne suke bauta wa.”
[Hasiya]
a A Luka 4:18, Yesu ya yi kaulin Ishaya 61:1 wadda ta yi amfani da sunan Allah Yahweh, wato Jehobah.
b A Hausa, ana kiran sunan Allah “Jehobah.”
-
-
“Wannan Bishara Kuwa ta Mulki Za a Yi Wa’azinta”Hasumiyar Tsaro—2012 | 1 Yuli
-
-
“Wannan Bishara Kuwa ta Mulki Za a Yi Wa’azinta”
“Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.”—MATTA 24:14.
Abin da Hakan Yake Nufi: Luka, marubucin Linjila ya ba da rahoto cewa Yesu “ya yi ta yawo a cikin birane da ƙauyuka, yana wa’azi, yana kawo bishara ta mulkin Allah.” (Luka 8:1) Yesu da kansa ya ce: “Dole in kai bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luka 4:43) Ya tura almajiransa su kai bishara zuwa garuruwa da ƙauyuka kuma daga baya ya umurce su: ‘Za ku zama shaiduna cikin iyakan duniya.’—Ayyukan Manzanni 1:8; Luka 10:1.
Yadda Kiristoci na Farko Suka Yi Abin da Yesu Ya Ce: Almajiran Yesu ba su ɓata lokaci ba wajen yin abin da Yesu ya gaya musu su yi. “Kowace rana fa, cikin haikali da cikin gida, ba su fāsa koyarwa da yin wa’azi kuma Yesu Kristi ne.” (Ayyukan Manzanni 5:42) Babu wanda ke cikin ikilisiya da bai yi wa’azi ba. Ɗan tarihi mai suna Neander ya lura cewa “Celsus wanda shi ne marubuci na farko da ya yi sūkar Kiristanci, ya yi ba’a domin mutanen da suka yi wa’azin linjila da himma sun haɗa da masu yin saka, masu gyaran takalma, dukawa, tare da jahilai.” A cikin littafinsa The Early Centuries of the Church, Jean Bernardi ya rubuta: Ya kamata “[Kiristoci] su riƙa yin wa’azi ga dukan mutane a ko’ina. A tituna da birane da gidaje. Suna yin wa’azin ne ko an saurare su ko a’a. . . . A duk faɗin duniya.”
Su Wane Ne Suke Bin Wannan Misalin a Yau? “Mutane da yawa a yau ba sa sha’awar bauta wa Allah domin coci-coci ba su ɗauki yin wa’azi da koyarwa da muhimmanci ba,” in ji firist ɗin cocin Anglican, David Watson. A cikin littafin da ya rubuta Why Are the Catholics Leaving?, José Luis Pérez Guadalupe ya yi rubutu a kan ayyukan ’yan cocin Evangelical da Adventist da dai sauran su kuma ya lura cewa “ba sa wa’azi gida-gida.” Amma ya rubuta game da Shaidun Jehobah, cewa: “Suna wa’azi gida-gida bisa tsari.”
Wani bayani mai muhimmanci kuma na gaskiya wanda Jonathan Turley wanda ke rubuce a littafin nan Cato Supreme Court Review, 2001-2002 ya ce: “Da zarar ka ambata Shaidun Jehobah, abin da zai zo zuciyar yawancin mutane shi ne masu wa’azi da suke zuwa gidajenmu a lokacin da ba ma so. Ga Shaidun Jehobah, yin wa’azi ƙofa-ƙofa don su rinjayi mutane su dawo addininsu ba batun ƙara yawan mabiya ba ne ba kawai, amma yin hakan yana da muhimmanci ga bangaskiyarsu.”
[Akwati a shafi na 9]
Su Wane Ne Suke da Alamun a Yau?
Daga ƙa’idodin Nassi da aka tattauna a jerin talifofin nan, a ganinka, su wa suke da alamun Kiristanci na gaskiya a yau? Ko da yake akwai dubban rukunoni da dariku da suke da’awar cewa su Kiristoci ne, kada ka mance abin da Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Ba dukan mai-ce mani, Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga cikin mulkin sama ba; sai wanda ke aikata nufin Ubana wanda ke cikin sama.” (Matta 7:21) Sanin waɗanda suke yin nufin Allah, wato, waɗanda suke da alamun Kiristanci na gaskiya, da kuma yin tarayya da su zai kai ga samun albarka na har abada a Mulkin Allah. Don Allah ka tuntuɓi Shaidun Jehobah da suka kawo maka wannan mujallar, don ka samu ƙarin bayani game da Mulkin Allah da albarkar da zai kawo.—Luka 4:43.
-