Abubuwan Da Za Su Sa Iyali Farin Ciki
Magance Matsaloli
Ya ce: “Ina ’ya’yanmu mata suke?”
Ta ce: “Suna kasuwa suna sayan sababbin tufafi.”
Ya ce: [Da fushi da babbar murya] “Me ki ke nufi da ‘sayan sababbin tufafi’? Sun sayi sababbin tufafi watan da ya shige fa!”
Ta ce: [Tana kāre kanta, cike da fushi don yana ganin laifinta ne] “Ai kayan suna da araha. Ban da haka, sun tambaye ni kuma na ce su tafi.”
Ya ce: [Ya yi fushi sosai kuma ya soma magana da babbar murya] “Kin san ba na son ’ya’yanmu suna kashe kuɗi ba tare da sun gaya mini ba! Me ya sa za ki yanke irin wannan shawarar da sauri ba tare da kin gaya mini ba?”
WAƊANNE matsaloli ne kake ganin ma’auratan da aka ambata a baya suke bukatar su magance? Babu shakka mijin yana da matsalar zafin zuciya. Ban da haka, kamar ma’auratan suna jayayya game da yawan ’yancin da ya kamata su ba yaransu. Kuma kamar suna da matsala wajen tattaunawa da juna.
Babu auren da ba shi da matsala. Dukan ma’aurata za su fuskanci wasu irin matsaloli. Ko da matsalolin masu tsanani ne ko marasa tsanani, yana da muhimmanci miji da mata su san yadda za su magance su. Me ya sa?
Da shigewar lokaci, matsalolin da ba a magance ba za su hana sadarwa. Sarki Sulemanu mai hikima ya lura: “Irin waɗannan tantankawa kuma suna kama da gardunan kagara.” (Misalai 18:19) Ta yaya za ku iya tattaunawa sosai sa’ad da ku ke son ku magance matsaloli?
Kamar yadda ake bukatar zuciya da huhu idan ana son jini ya bi jiki sosai, ana bukatar ƙauna da nuna daraja idan ana son a amfana sosai a aure ta wajen sadarwa. (Afisawa 5:33) Idan ya zo ga magance matsaloli, ƙauna za ta motsa ma’aurata su mance da kuskuren da suka yi a dā, da kuma baƙin cikin da hakan ya jawo, kuma su mai da hankali a kan ainihin matsalar da suke fuskanta a yanzu. (1 Korinthiyawa 13:4, 5; 1 Bitrus 4:8) Ma’auratan da suke daraja juna suna tattaunawa da juna sosai kuma suna ƙoƙarin jin abin da ɗayan yake nufi, ba abin da aka faɗa ba kawai.
Matakai Huɗu na Magance Matsaloli
Ka yi la’akari da matakai huɗu da aka jera a gaba, kuma ka lura da yadda ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimakonka ka magance matsaloli a hanya mai kyau.
1. Ku keɓe lokaci don tattauna matsalar. “Ga kowane abu akwai nasa kwanaki, . . . akwai lokacin shuru da lokacin magana.” (Mai-Wa’azi 3:1, 7) Kamar yadda aka nuna a gardamar da aka yi ƙaulinsa a baya, wasu matsaloli suna iya sa fushi ƙwarai. Idan hakan ya faru, ku kame kanku kuma ku ƙyale batun, wato, ku yi “shiru” kafin ku yi fushi sosai. Ba za ku ɓata dangantakarku ba idan ku ka yi biyayya da shawarar Littafi Mai Tsarki da ta ce: “Mafarin jayayya kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, sai a tsai da ita tun ba ta haɓaka ba.”—Misalai 17:14, Littafi Mai Tsarki.
Amma, da akwai “lokacin magana.” Kamar ciyayi, matsaloli suna iya yaɗuwa idan ba a magance su ba. Saboda haka, kada ku ƙyale matsalar, domin kuna tunanin cewa za a mance da ita. Idan ka ce a daina maganar wani batu, ka daraja abokiyar aurenka ta wajen zaɓan lokaci a nan gaba da za ku tattauna matsalar. Irin wannan alkawarin zai taimake ku ku bi gargaɗin Littafi Mai Tsarki: “Kada rana ta faɗi kuna kan fushinku.” (Afisawa 4:26) Hakika, kuna bukatar ku cika alkawarin da ku ka yi.
KU GWADA WANNAN: Ku zaɓi lokaci a kowane mako da za ku riƙa tattauna matsalolin iyali. Idan kuka lura cewa akwai ainihin lokacin da kuke yin musu, alal misali, a lokacin da kuka dawo gida daga wajen aiki ko kuwa kafin ku ci abinci, kada ku tattauna game da matsalolin a waɗannan lokuttan. Maimakon haka, ku zaɓi lokacin da hankalinku ya fi kwanciya.
2. Ku faɗi ainihin ra’ayinku amma cikin daraja. “Saboda haka sai . . . kowa ya riƙa faɗar gaskiya ga maƙwabcinsa.” (Afisawa 4:25, Littafi Mai Tsarki.) Idan kana da aure, matarka ita ce maƙwabciyarka mafi kusa. Saboda haka, ka faɗi gaskiya da kuma ainihin yadda kake ji sa’ad da kake tattaunawa da matarka. Margareta,a wadda ta yi aure shekaru 26 da suka shige ta ce: “A lokacin da aka ɗaura mini aure, ina tunanin cewa mijina zai san ainihin yadda nike ji sa’ad da matsala ta taso. Na zo na gane cewa hakan ba zai yiwu ba. A yanzu ina ƙoƙarin faɗin abin da ke zuciyata da kuma ainihin yadda nike ji.”
Ka tuna cewa makasudinka a duk lokacin da kuke tattaunawa game da matsala shi ne, barin abokiyar aurenka ta san abin da ke zuciyarka ba wai kama maƙiyi ko cin yaƙi ba. Don ka yi hakan yadda ya kamata, ka faɗi abin da kake ganin cewa shi ne matsalar, ka faɗi lokacin da hakan ya faru, bayan haka, ka bayyana yadda ka ji. Alal misali, idan rashin tsabtar mijinki yana ba ki haushi, cikin bangirma kina iya cewa, ‘Idan ka dawo gida daga wurin aiki kuma ka tuɓe kayanka ka bar su a ƙasa [lokaci da kuma matsalar], ina jin kamar ba ka son yadda nike tsabtace da kuma gyara gida [hakan ya bayyana ainihin yadda ki ke ji].’ Bayan haka, a cikin basira ki ba da shawarar abin kike ganin cewa zai magance matsalar.
KU GWADA WANNAN: Don ki tuna abin da kike son ki tattauna da mijinki, ki rubuta ainihin abin da kike ganin cewa shi ne matsalar, da kuma yadda kike son a magance ta.
3. Ka saurara kuma ka nuna cewa ka fahimci yadda matarka take ji. Almajiri Yaƙubu ya rubuta cewa Kiristoci su ‘yi hanzarin ji, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi.’ (Yaƙubu 1:19) Abin da ya fi jawo baƙin ciki a aure shi ne matarka ta yi tunanin cewa ba ka fahimci yadda take ji game da wata matsala ba. Saboda haka, ka ƙudurta cewa ba za ka sa matarka ta ji hakan ba!—Matta 7:12.
Wolfgang, wanda ya yi aure shekaru 35 da suka shige ya ce, “Sa’ad da muke tattaunawa game da matsaloli, na kan damu sosai, musamman sa’ad da na ga cewa matata ba ta fahimci abin da nike cewa ba.” Dianna, wadda ta yi aure shekaru 20 da suka shige ta ce, “A yawancin lokaci na kan gaya wa mijina cewa ba ya sauraron abin da nike cewa sosai sa’ad da muke tattaunawa game da matsaloli.” Ta yaya za ka iya magance wannan matsalar?
Kada ka yi zaton cewa ka san abin da matarka take tunani ko yadda take ji. Kalmar Allah ta ce: “Ta hanyar girman kai babu abin da ke zuwa sai husuma: amma hikima tana wurin masu karɓa shawarar kirki.” (Misalai 13:10) Ka daraja abokiyar aurenka ta wajen barin ta ta faɗi ra’ayinta ba tare da ka katse ta ba. Don ka tabbatar da cewa ka fahimci abin da matarka ta ce, ka bayyana wa matarka abin da ta ce ba tare da gatse ko fushi ba. Ka ƙyale matarka ta yi maka gyara idan ba ka fahimci abin da take nufi ba. Kada ka yi maganar kai kaɗai. Ku tattauna har sai kun fahimci juna sosai da kuma yadda kuke ji game da batun.
Hakika, kuna bukatar tawali’u da haƙuri don ku saurari juna sosai kuma ku fahimci ra’ayin juna. Amma, idan ka daraja matarka, hakan zai motsa ta ta daraja ka sosai.—Matta 7:2; Romawa 12:10.
KU GWADA WANNAN: Sa’ad da kike maimaita abin da mijinki ya ce, kada ki maimaita ainihin kalamansa. A hanya mai kyau, ki kwatanta abin da mijinki yake cewa da kuma yadda yake ji.—1 Bitrus 3:8.
4. Ku yarda da shawarar da kuka bayar na magance matsalar. “Gwamma biyu da ɗaya; domin suna da arziki cikin aikinsu. Gama idan sun fāɗi, ɗaya za ya ɗaga ɗan’uwansa.” (Mai-Wa’azi 4:9, 10) Ba za a iya magance matsaloli ba a aure idan mata da miji suka ƙi haɗa kai da kuma taimaka wa juna.
Hakika, Jehobah ya naɗa miji ya zama shugaban iyali. (1 Korinthiyawa 11:3; Afisawa 5:23) Amma shugabanci ba ya nufin cin zali. Miji mai hikima ba zai yanke shawara ba tare da ya ji ra’ayin matarsa ba. David, wanda ya yi aure shekaru 20 da suka shige ya ce, “Na kan yi ƙoƙari na nemi batun da ni da matata za mu yarda da shi, kuma mu yanke shawarar da mu biyu za mu amince da shi.” Tanya, wadda ta yi aure shekaru bakwai da suka shige ta ce, “Wannan ba batun wanda ke da gaskiya ko wanda ya yi laifi ba ne. A wasu lokatai ra’ayoyinku na magance matsala zai bambanta. Amma na ga cewa abin da zai sa a yi nasara shi ne, kasancewa mai sauƙin hali da tunani.”
KU GWADA WANNAN: Ku haɗa kai ta wajen rubuta hanyoyi dabam dabam da kuke ganin cewa za ku iya magance matsalarku. Sa’ad da kuka gama rubuta ra’ayoyinku gabaki ɗaya, ku bincika abubuwan da kuka rubuta kuma ku yi amfani da wanda kuka ga cewa ya fi dacewa. Bayan haka, sai ku zaɓi lokaci a nan gaba da za ku duba ku gani ko kun bi shawarar da kuka tsai da da kuma yadda kuka amfana.
Ku Yi Aiki Tare, Ba Dabam Dabam Ba
Yesu ya kwatanta aure da karkiya. (Matta 19:6) A zamaninsa, ana amfani ne da karkiya don a haɗa dabbobi biyu su yi aiki tare. Idan dabbobin suka ƙi haɗa kai da juna, ba za su yi aikin yadda ya kamata ba kuma karkiyar za ta ji masu rauni a wuya. Amma idan suka yi aiki tare, za su iya jan kaya mai nauyi ko su yi huɗa.
Hakazalika, mata da mijin da suka ƙi haɗa kai suna iya raunata kansu a ƙarƙashin karkiyar aure. A wani ɓangaren kuwa, idan suka yi aiki tare, za su iya magance kusan dukan matsaloli kuma su cim ma abubuwa masu kyau da yawa. Wani ma’auraci mai suna Kalala wanda ke jin daɗin aurensa, ya kammala batun da cewa, “Shekaru 25 ke nan ni da matata muke magance matsaloli ta wajen gaya wa juna gaskiya, ta wajen saka kanmu a cikin yanayin da ɗayan yake, ta neman taimakon Jehobah, da kuma yin amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki.” Za ka iya yin hakan?
KU TAMBAYI KANKU . . .
▪ Wace matsala ce zan fi so na tattauna da matata ko mijina?
▪ Ta yaya zan tabbata cewa na fahimci ainihin yadda matata ko mijina yake ji game da wannan batun?
▪ Idan na nace cewa zan yi abubuwa yadda na ga dama, waɗanne matsaloli ne zan iya jawowa?
[Hasiya]
a An canja wasu sunaye.