WAƘA TA 125
Masu Jinƙai Suna Farin Ciki!
Hoto
	- 1. Jehobah na da tausayi - Kuma yana son mu sosai. - Shi mai son yin nagarta ne, - Yana biyan bukatunmu. - In muka yi kurakurai - Kuma muka yi addu’a. - Jehobah zai gafarce mu - Don ya san ajizai ne mu. 
- 2. In muka yi tuban gaske - In muna son gafartawa, - Yesu Kristi ya ce mana - In mun yi addu’a mu ce: - ‘Allah ka gafarta mana, - Yadda muke gafartawa.’ - In mun yafe wa mutane, - Za mu sami kwanciyar rai. 
- 3. In muna son ba da kyauta, - Muna yin koyi da Allah. - Mu taimaki mabukata, - Mu yi hakan da yardar rai. - Jehobah Allah mai ƙauna, - Zai albarkace mu sosai. - Masu jinƙai suna murna, - Allah yana daraja su. 
(Ka kuma duba Mat. 6:2-4, 12-14.)