WAƘA TA 74
Mu Rera Waƙar Mulkin Allah!
(Zabura 98:1)
1. Ku zo mu yi wannan sabuwar waƙa,
Waƙar na ɗaukaka Maɗaukaki.
Kalmomin waƙar na da ban ƙarfafa.
Waƙar tana ƙarfafa mu cewa:
(AMSHI)
‘Mu bauta wa Maɗaukaki!
Ɗansa shi ne Sarkin Mulkin.
Sai ku zo don mu koyi waƙar Mulkin,
Mu ɗaukaka Allah da sunansa.’
2. Da waƙar nan muke shelar Mulkinsa.
Yesu Kristi ne zai yi sarauta
Kuma akwai waɗansu mutane ma
Da za su yi sarauta da Yesu:
(AMSHI)
‘Mu bauta wa Maɗaukaki!
Ɗansa shi ne Sarkin Mulkin.
Sai ku zo don mu koyi waƙar Mulkin,
Mu ɗaukaka Allah da sunansa.’
3. Amintattu ne suke rera waƙar,
Kalmominta da sauƙin rerawa.
A duniya mutane sun koye ta,
Suna yi wa wasu shelar waƙar:
(AMSHI)
‘Mu bauta wa Maɗaukaki!
Ɗansa shi ne Sarkin Mulkin.
Sai ku zo don mu koyi waƙar Mulkin,
Mu ɗaukaka Allah da sunansa.’
(Ka kuma duba Zab. 95:6; 1 Bit. 2:9, 10; R. Yoh. 12:10.)