WAƘA TA 64
Mu Riƙa Yin Wa’azi da Farin Ciki
Hoto
	- 1. Yanzu muna lokacin girbi, - Domin shukarmu ta nuna. - Jehobah Ubanmu a sama, - Yana so mu yi wa’azi. - Yesu Kristi shi ne ja-gora, - Ya kafa misali mai kyau. - Muna murna sosai a koyaushe. - Don muna shelar bishara. 
- 2. Muna yin wa’azin bishara - Don muna ƙaunar mutane. - Wa’azi na da muhimmanci - Domin ƙarshe yana tafe. - Jehobah na mana albarka, - Yana sa mu murna sosai. - Za mu riƙe aminci har ƙarshe - Muna wa’azi da himma. 
(Ka kuma duba Mat. 24:13; 1 Kor. 3:9; 2 Tim. 4:2.)