Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 11/10 pp. 1-2
  • Gonaki Sun Yi Fari Sun Isa Girbi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gonaki Sun Yi Fari Sun Isa Girbi
  • Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Ci Gaba A Aikin Girbi!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ku Zama Magirba Masu Farin Ciki!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Sakamakon Yin Wa’azi​—“Gonaki Sun Riga Sun Yi Fari Kuma Sun Isa Girbi”
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Ka Sa Hannu Sosai A Yin Babban Girbi Na Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hidimarmu Ta Mulki—2010
km 11/10 pp. 1-2

Gonaki Sun Yi Fari Sun Isa Girbi

1. Wane aiki mai muhimmanci ne ake yi yanzu?

1 Bayan da ya yi wa wata Basamariya wa’azi, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Ku tāda idanunku, ku duba gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi.” (Yoh. 4:35, 36) Ana kan yin girbi na ruhaniya kuma Yesu ya san yawan yadda za a cim ma wannan aiki a dukan duniya. Daga matsayinsa a sama, Yesu ya ci gaba da sa hannu sosai a wannan girbin. (Mat. 28:19, 20) Waɗanne abubuwa ne suka nuna cewa za a ci gaba da yin wannan aikin da gaggawa yayin da yake kai ƙarshensa?

2. Waɗanne abubuwa ne suka nuna cewa ana shagalawa a yin wannan aikin girbi sosai a dukan duniya?

2 Girbi na Dukan Duniya: A shekarar hidima ta 2009, an samu ƙarin kashi 3.2 na masu shela a dukan duniya. Ƙasashe da aka hana aikin wa’azi sun samu ƙarin kashi 14. Adadin nazarorin Littafi Mai Tsarki da aka ba da rahotonsu a kowane wata ya wuce 7,619,000, wato, adadin da ya wuce ƙolin masu shela da kuma kusan rabin miliyan fiye da adadin nazarori da aka ba da rahotonsu shekarar da ta wuce. Yayin da aikin yake faɗaɗawa a yankuna masu yawa, ana bukatan waɗanda suka sauke karatu a makarantar Giliyad da kuma Makarantar Koyar da Masu Hidima. Yankuna na yaren ƙasashen waje suna ba da amfani sosai a ƙasashe da yawa. A bayane yake cewa Jehobah yana hanzarta aikin a lokacin da ake kammala girbin. (Isha. 60:22) Kana da ra’ayin da ya dace game da “gonaki” na wa’azi a yankinku?

3. Mene ne wasu za su iya kammalawa game da yankinsu?

3 Girbi a Yankinku: Wasu suna iya cewa: “Ba a samun ƙaruwa sosai a yankinmu.” Gaskiya ne cewa ba a samun ƙaruwa a wasu yanki yadda ake samu a wasu ko kuma ba a samun ƙaruwa kamar dā. Saboda haka, wasu Shaidu suna iya kammala cewa yawancin waɗanda ya kamata su saurari saƙon a waɗannan wuraren sun riga sun yi hakan, don haka ayyukan da suka rage ba su da yawa. Shin hakan gaskiya ne?

4. Wane ra’ayi mai kyau ne ya kamata mu kasance da shi game da hidimarmu, kuma me ya sa?

4 Daga farko zuwa ƙarshe, lokacin girbi lokaci mai cike da ayyuka ne sosai. Ka lura da azancin gaggawa a waɗannan kalaman Yesu: “Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aiko ma’aikata cikin girbinsa.” (Mat. 9:37, 38) Jehobah, Ubangijin girbi ne yake tsara yadda da kuma inda za a samu amfani. (Yoh. 6:44; 1 Kor. 3:6-8) Mene ne hakkinmu? Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa: “Da safe sai ka shuka irinka, da yamma kuma kada ka ja hannunka.” (M. Wa. 11:4-6) Bai kamata mu karaya ba, yayin da aikin girbi yake kai ƙarshensa!

5. Me ya sa ya kamata mu ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo a yankin da mutane ba sa na’am da saƙonmu sosai?

5 Ku Ci Gaba da Yin Girbi: Idan mun yi wa’azi a yankinmu sau da yawa kuma mutane ba sa yin na’am da saƙon, akwai dalili mai kyau na kasancewa da ƙwazo da kuma azancin gaggawa. (2 Tim. 4:2) Abubuwa da suke faruwa a duniya suna sa mutane su canja halinsu kuma su yi tunani sosai game da rayuwarsu ta nan gaba. Yayin da matasa suke zama manya, za su iya ganin amfanin samun kāriya da kwanciyar hankali. Yin naciya zai iya taɓa zuciyar wasu mutane. Hakika, waɗanda ba su saurara ba a dā za su iya yin hakan. Har ma waɗanda suka ƙi saƙonmu da gangan suna bukatar gargaɗi.—Ezek. 2:4, 5; 3:19.

6. Idan akwai ƙalubale sosai a yankinmu, mene ne zai taimaka mana mu kasance da ƙwazo?

6 Idan akwai ƙalubale sosai a yankinmu, mene ne zai taimaka mana mu kasance da ƙwazo? Ƙari ga hidimar gida gida, wataƙila za mu iya saka hannu a wasu fannonin hidima, kamar yin wa’azi a wurin kasuwanci ko kuma da tarho. Ko kuma za mu iya bambanta gabatarwarmu domin mu samu sabuwar hanyar yin mahawwara. Za mu iya canja tsarin ayyukanmu kuma mu saka hannu a yin hidima da yamma ko kuma a wasu lokatai da za mu samu mutane a gidajensu. Wataƙila za mu iya koyon sabon yare don mu samu yi wa mutane da yawa wa’azi. Za mu iya faɗaɗa hidimarmu ta yin hidimar majagaba na kullum. Ko kuma za mu iya ƙaura zuwa inda babu masu girbi da yawa. Idan muna da ra’ayi mai kyau game da hidimarmu, za mu yi ƙoƙari mu saka hannu sosai a wannan muhimmin aikin.

7. Har yaushe ya kamata mu ci gaba da yin aikin girbi?

7 Manoma suna da ayanannen lokaci na girbe amfanin gonarsu, saboda hakan ba sa hutawa ko kuma kasala sai sun ƙarasa aikin. Girbi na ruhaniya ma yana bukatar irin wannan azancin gaggawa. Har wane lokaci ne ya kamata mu ci gaba da yin aikin girbi? A gabaki ɗayan “matuƙar zamani” har ‘ƙarshe.’ (Mat. 24:14; 28:20) Kamar mai yin hidima Mafi Girma na Jehobah, muna son mu kammala aikin da aka ɗanka mana. (Yoh. 4:34; 17:4) Bari mu ci gaba da yin hidimarmu da ƙwazo da farin ciki da kuma ra’ayi mai kyau har ƙarshe. (Mat. 24:13) Ba a kammala girbin ba tukun!

[Bayanin da ke shafi na 2]

Daga farko zuwa ƙarshe, lokacin girbi lokaci mai cike da ayyuka ne sosai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba