Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 8/1 pp. 13-18
  • Ku Ci Gaba A Aikin Girbi!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Ci Gaba A Aikin Girbi!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Abin Ƙi”
  • Saƙo Mai Ceton Rai
  • Ana Tsananta Musu duk da Haka Suna Farin Ciki
  • Ka Jimre a Aikin Girbi
  • Ku Zama Magirba Masu Farin Ciki!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Gonaki Sun Yi Fari Sun Isa Girbi
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Sakamakon Yin Wa’azi​—“Gonaki Sun Riga Sun Yi Fari Kuma Sun Isa Girbi”
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Ka Sa Hannu Sosai A Yin Babban Girbi Na Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 8/1 pp. 13-18

Ku Ci Gaba A Aikin Girbi!

“Masu-shuka da hawaye za su yi girbi da murna.”—ZABURA 126:5.

1. Me ya sa za a “yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aike ma’aikata” a yau?

BAYAN tafiyar wa’azi na uku na Yesu Kristi zuwa Galili, ya gaya wa almajiransa: “Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne.” (Matta 9:37) Yanayin haka yake a Yahudiya. (Luka 10:2) Tun da wannan gaskiya ne kusan shekara 2,000 da ta shige, yaya yanayin yake a yau? A shekarar hidima da ta shige, Shaidun Jehovah fiye da 6,000,000 suka ci gaba a wannan aikin girbi na alama tsakanin mutane 6,000,000,000 da suke duniya, da yawa cikinsu “suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” Saboda haka, shawarar Yesu “ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aike ma’aikata cikin girbinsa,” tana da muhimmanci a yau kamar yadda take ƙarnuka da suka shige.—Matta 9:36, 38.

2. Me ke jawo hankalin mutane gare mu?

2 Jehovah Allah, Ubangijin girbin, ya amsa wannan addu’ar ya ƙara aika da ma’aikata. Kuma abin farin ciki ne ƙwarai a saka hannu cikin wannan aikin girbi da Allah yake ja-gorarsa! Ko da yake adadinmu kaɗan ne idan aka gwada da al’ummai, amma himmarmu wajen wa’azin Mulki da kuma almajirantarwa ya sa mun jawo hankalin mutanen duniya. A ƙasashe da yawa a kai a kai ana ambatarmu a hanyoyin sadarwa. Ƙwanƙwasar ƙofa a wasan kwaikwayo na telibijin sai a ce Shaidun Jehovah ne suke ziyara. Hakika, ayyukanmu na Kirista na magirba na alama sanannu ne ƙwarai a ƙarni na 21.

3. (a) Ta yaya muka sani cewa an lura da aikin wa’azin Mulki na ƙarni na farko? (b) Me ya sa za mu iya ce mala’iku suna taimaka mana a hidimarmu?

3 Duniya ta lura da ayyukan wa’azin Mulki na ƙarni na farko da kuma tsananta wa masu shelar bishara. Saboda haka, manzo Bulus ya rubuta: “Ga ganina, Allah ya nuna mu manzanni daga bayan duka, sai ka ce mutane hukumtattu ga mutuwa: gama an maishe mu abin kallo ga duniya, da mala’iku, da mutane kuma.” (1 Korinthiyawa 4:9) Hakanan, jimirinmu na masu shelar Mulki duk da tsanantawa ya jawo hankalin duniya a garemu kuma yana da muhimmanci ga mala’iku. Ru’ya ta Yohanna 14:6 ta ce: “[Manzo Yohanna ya] ga wani mala’ika kuma yana firiya a tsakiyar sararin sama, yana da bishara ta har abada wadda za ya yi shelarta ga mazaunan duniya, ga kowane iri da ƙabila da harshe da al’umma.” Hakika, mala’iku suna taimakonmu a hidimarmu—aikinmu na girbi!—Ibraniyawa 1:13, 14.

“Abin Ƙi”

4, 5. (a) Wane gargaɗi Yesu ya ba almajiransa? (b) Me ya sa bayin Jehovah na zamani “abin ƙi” ne?

4 Lokacin da aka aike manzannin Yesu su zama magirba, sun bi umurninsa su “zama masu-azanci fa kamar macizai, marasa-ɓarna kamar kurciyoyi.” Yesu ya daɗa cewa: “Ku yi hankali da mutane: gama za su bashe ku ga majalisai, cikin majami’unsu kuma za su yi muku bulala; i, kuma a gaban mahukunta da sarakuna za a kawo ku sabili da ni, domin shaida garesu da Al’ummai . . . Za ku zama abin ƙi ga dukan mutane sabili da sunana: amma wanda ya jimre har matuƙa, shi ne za ya tsira.”—Matta 10:16-22.

5 Mu “abin ƙi” ne a yau domin “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan,” Iblis wanda shi ne babban abokin gaban Allah da kuma mutanensa. (1 Yohanna 5:19) Abokan gabanmu sun lura da ci gabanmu ta ruhaniya amma suka ƙi su yaba wa Jehovah dominsa. ’Yan adawa suna ganin fuskokinmu na farin ciki, muna murmushi yayin da muke saka hannu cikin aikinmu na girbi da farin ciki. Suna mamakin haɗin kanmu! Hakika, za su yarda da ƙyar lokacin da suka je wata ƙasa suka ga Shaidun Jehovah suna yin wannan aikin da suka san da shi a ƙasarsu. Babu shakka, mun san cewa a lokaci na Jehovah, mai goyon bayanmu kuma tushen haɗin kanmu, za a sanar da shi har ga abokan gabanmu.—Ezekiel 38:10-12, 23.

6. Wane tabbaci muke da shi yayin da muke yin aikin girbi, kuma waɗanne tambayoyi suka taso?

6 Ubangijin girbin ya ba wa Ɗansa, Yesu Kristi, “dukan hukunci a cikin sama da ƙasa.” (Matta 28:18) Saboda haka, Jehovah ya yi amfani da Yesu ya ja-goranci aikin girbi ta wajen mala’ikun sama da kuma shafaffu “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” a nan duniya. (Matta 24:45-47; Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7) Amma ta yaya za mu jure wa hamayyar abokan gaba kuma mu riƙe farin cikinmu yayin da muke ci gaba a aikinmu na girbi?

7. Wane hali ya kamata mu yi ƙoƙari mu riƙe lokacin da ake hamayya da mu ko kuma ake tsananta mana?

7 Lokacin da muke fuskantar hamayya ko kuma tsanantawa kai tsaye, mu nemi taimakon Allah saboda mu riƙe farin ciki kamar irin na Bulus. Ya rubuta: “Ana zaginmu, muna sa albarka; ana tsanantanmu, muna haƙuri; ana yi mana ƙire, muna bada haƙuri.” (1 Korinthiyawa 4:12, 13) Farin ciki da kuma basira a hidimarmu ga jama’a, wasu lokatai suna canja halin masu hamayya da mu.

8. Wace ƙarfafa muka samu daga kalmomin Yesu da suke rubuce cikin Matta 10:28?

8 Ko razanar za a kashe mu ma ba ta rage himmarmu na magirba. Muna shelar saƙon Mulkin a fili babu tsoro. Mun samu ƙarfafa daga kalmomin Yesu: “Kada ku ji tsoron waɗannan da su ke kisan jiki, ba su kuwa da iko su kashe rai: gwamma dai ku ji tsoron wannan wanda yana da iko ya halaka rai duk da jiki cikin Jahannama.” (Matta 10:28) Mun san cewa Ubanmu na sama shi ne Mai Ba da rai. Zai ba da lada ga waɗanda suka riƙe amincinsu a gare sa kuma suka ci gaba da aikin girbi cikin gaskiya.

Saƙo Mai Ceton Rai

9. Yaya wasu suka yi game da maganar Ezekiel, kuma yaya abu kamar wannan yake faruwa a yau?

9 Lokacin da annabi Ezekiel ya sanar da saƙon Jehovah ba tare da tsoro ba ga “al’ummai masu tawaye”—masarautar Isra’ila da kuma ta Yahuda—wasu mutane sun yi murnar jin abin da ya ce. (Ezekiel 2:3) “Ga shi kuwa,” Jehovah ya ce, “kai a garesu kamar waƙar ƙauna ne, waƙar wanda ya ke da murya mai-daɗi, ya kuwa iya muzika ƙwarai.” (Ezekiel 33:32) Ko da yake suna son maganar Ezekiel, ba su yi amfani da ita ba. Me ke faruwa a yau? Lokacin da raguwan shafaffu da kuma abokan tarayyarsu suka sanar da saƙon Jehovah da gaba gaɗi, wasu suna so su ji game da albarkar Mulki, amma ba su yi godiya ba, su zama almajirai, kuma su haɗu wajen aikin girbi.

10, 11. A rabin farkon ƙarni na 20, menene aka yi don a yaɗa saƙonmu na ceton rai, kuma menene sakamakon haka?

10 A wata ɓangare kuma, mutane da yawa sun yi na’am da aikin girbin kuma sun saka hannu wajen shelar saƙonni na Allah. Lokacin taron gunduma dabam dabam na Kirista daga shekara ta 1922 zuwa ta 1928, alal misali, aka sanar da saƙon hukunci bisa mugun tsarin abubuwa na Shaiɗan a fili. Aka yi amfani da gidan rediyo a yaɗa wannan hukunci da aka sanar a waɗancan manyan taro. Bayan haka, mutanen Allah suka rarraba miliyoyin waɗannan sanarwa da aka buga.

11 A ƙarshen shekaru na 1930, wani salon aikin wa’azi ya fito—zagayar ba da saƙo. Da farko, mutanen Jehovah suna rataya kati da yake sanar da jawabi ga jama’a. Daga baya, suna ɗaukan kati da yake ɗauke da furci kamar su “Addini tarko ne kuma ruɗu” da kuma “Ka bauta wa Allah da Kristi Sarki.” Lokacin da suke tafiya a kan tituna, suna jawo hankalin mutane da suke wucewa. ‘Wannan ya sa aka san Shaidun Jehovah kuma ya ƙarfafa su,’ in ji wani ɗan’uwa wanda yake yin wannan aikin a kai a kai a kan titunan London, a Ingila.

12. Ƙari ga saƙon hukunci na Allah, menene muke sanarwa a hidimarmu, kuma su waye suka haɗa kai wajen wa’azin bisharar?

12 Yayin da muke shelar saƙon hukunci na Allah, muna kuma sanar da abubuwa masu kyau na saƙon Mulkin. Wa’azinmu da gaba gaɗi a duniya yana taimakonmu mu nemi waɗanda suka cancanta. (Matta 10:11) Yawancin waɗanda suke ajin shafaffu na ƙarshe sun yi na’am ga kira da aka yi da babbar murya na yin girbi a shekarun 1920 da shekarun 1930. Sai kuma, a taron gunduma a shekara ta 1935, aka samu labari mai ban sha’awa na albarka a nan gaba ga “taro mai girma” na “waɗansu tumaki” cikin aljanna a duniya. (Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:16) Sun bi saƙon hukunci na Allah suna haɗa kai da shafaffu wajen wa’azin bishara mai ceton rai.

13, 14. (a) Wace ta’aziyya za a iya samu daga Zabura 126:5, 6? (b) Idan muka ci gaba da shuki da kuma ban ruwa, menene zai faru?

13 Abin ƙarfafa ne kalmomin Zabura 126:5, 6 ga magirba na Allah, musamman kuma ga waɗanda suke shan tsanani: “Masu-shuka da hawaye za su yi girbi da murna. Ko da yana tafiya yana kuka, yana ɗauke da ƙwaryar iri; za ya dawo kuma da guɗa, yana kawo dammunansa.” Kalmomin mai Zabura game da shuka da kuma girbi ya kwatanta kula da kuma albarkar Jehovah bisa raguwar da suka komo daga bauta a Babila ta dā. Sun yi farin ciki ƙwarai lokacin da aka sake su, amma wataƙila sun yi hawaye lokacin da suke shuka iri a ƙasar da ba a yi aiki a kan ta ba na shekara 70 lokacin da suke hijira. Duk da haka, waɗanda suka ci gaba da shukinsu da kuma ayyukan gine-gine sun more ladar aikinsu.

14 Wataƙila mun yi hawaye lokacin da muke fuskantar gwaji ko kuma lokacin da mu ko kuma ’yan’uwanmu masu bi suna wahala domin adalci. (1 Bitrus 3:14) A aikinmu na girbi, da farko za mu wahala domin kamar dai ba mu da abin da za mu iya ambata da zai nuna mun yi ƙoƙari a hidimarmu. Amma idan muka ci gaba da shuki da kuma ban ruwa, Allah zai sa ya yi girma, sau da yawa fiye ma da yadda muka yi tsammani. (1 Korinthiyawa 3:6) Wannan an kwatanta sosai ta wajen sakamakon rarraba Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai daga Nassosi.

15. Ka ba da misalin amfanin littattafan Kirista a aikin girbi.

15 Ka yi la’akari da misalin wani mutum mai suna Jim. Lokacin da mamarsa ta mutu, a cikin kayayyakinta ya sami wani littafi Life—How Did It Get Here? By Evolution or by Creation? a Ya karanta shi da farin ciki. A wani tattaunawa da wata Mashaidiya da ta same shi a kan titi, Jim ya yarda a sake ziyartarsa, kuma wannan ya kai ga nazarin Littafi Mai Tsarki. Jim ya ci gaba a ruhaniya babu ɓata lokaci, ya keɓe kansa ga Jehovah kuma ya yi baftisma. Ya gaya wa wasu a iyalinsa abin da ya koya. Sakamakon haka, ’yarsa da kuma wansa suka zama Shaidun Jehovah, Jim daga baya ya samu gatar hidima na cikakken lokaci na ba da kai a Bethel a London.

Ana Tsananta Musu duk da Haka Suna Farin Ciki

16. (a) Me ya sa muke samun nasara a aikin girbi? (b) Wane gargaɗi Yesu ya bayar game da sakamakon bisharar, amma da wane hali za mu isa wajen mutane?

16 Me ya sa aka samu irin wannan nasarar a aikin girbi? Domin shafaffun Kiristoci da kuma abokan tarayyarsu sun bi umurnin Yesu: “Abin da ni ke faɗa muku cikin duhu, ku furta a sarari: abin da ku ke ji cikin kunne kuma, ku yi shelarsa a bisa soraye.” (Matta 10:27) Ko da yake za mu iya yin tsammanin wahala, domin Yesu ya yi gargaɗi: “Ɗan’uwa za ya bada ɗan’uwa ga mutuwa, uba kuma za ya bada ɗansa; ’ya’ya za su tasa ma iyayensu, su sa a kashe su.” Yesu ya daɗa cewa: “Kada ku yi tsammani na zo domin in koro salama bisa duniya: na zo ba domin in koro salama ba, amma takobi.” (Matta 10:21, 34) Yesu bai da niyyar ya raba iyalai da gangan. Amma bisharar a wasu lokatai takan yi haka. Haka yake ga bayin Allah a yau. Lokacin da muka ziyarci iyalai, ba niyyarmu ba ce mu kawo dalilin raba iyalan. Muradinmu ne kowa ya karɓi bisharar. Saboda haka, muke ƙoƙari mu isa dukan iyali a hanya ta ƙauna, da kuma tausayi da zai sa saƙonmu ya karɓu ga waɗanda ‘suke da zuciyar kirki domin rai madawwami.’—Ayukan Manzanni 13:48.

17. Ta yaya aka keɓe waɗanda suka ɗaukaka ikon mallaka na Allah, kuma su wanene misali ɗaya na wannan?

17 Saƙon Mulkin ya ware waɗanda suka karɓi ikon mallaka na Allah. Alal misali, ka dubi yadda ’yan’uwanmu masu bi suka kasance dabam domin sun ‘baiwa Kaisar abin da ke na Kaisar, kuma suka ba Allah abin da ke na Allah’ a zamanin Ɗaukaka Ƙasa a Jamus. (Luka 20:25) Dabam da shugabanan addinai da wasu Kiristoci da suke tarayya da cocin Kiristendam, bayin Jehovah sun dage, sun ƙi su taka mizanan Littafi Mai Tsarki. (Ishaya 2:4; Matta 4:10; Yohanna 17:16) Farfesa Christine King, mawallafiyar littafin nan The Nazi State and the New Religions, ta lura: Bisa Shaidu ne kawai gwamnatin [Nazi] ba ta yi nasara ba, ko da yake ta kashe dubbai, aikin ya ci gaba kuma a Mayu 1945, ƙungiyar Shaidun Jehovah tana nan, amma gwamnatin ba ta kasance ba kuma.”

18. Wane hali mutanen Jehovah suka nuna duk da tsanantawa?

18 Halin mutanen Jehovah yana da muhimmanci lokacin da suka fuskanci tsanantawa. Yayin da bangaskiyarmu tana burge ma’aikata, suna yin mamaki ba mu da wani ƙiyayya ko gāba. Alal misali, Shaidu da suka tsira daga Kisa na Nazi sau da yawa suna furta farin ciki da kuma gamsuwa yayin da suka tuna da abin da suka fuskanta. Sun san cewa Jehovah ya ba su “mafificin girman ikon.” (2 Korinthiyawa 4:7) Shafaffu tsakaninmu suna da tabbacin cewa ‘an rubuta sunayensu cikin sama.’ (Luka 10:20) Jimirinsu ya kai ga bege da ba ya kunyatarwa, kuma magirba masu aminci da suke da bege na duniya suna da irin wannan tabbacin.—Romawa 5:4, 5.

Ka Jimre a Aikin Girbi

19. Wane salo mai kyau aka yi amfani da shi a hidimar Kirista?

19 Tsawon lokacin da Jehovah zai ƙyale mu mu yi wannan aikin girbi na alama dai har yanzu muna jira mu gani. A yanzu, ya kamata mu tuna cewa magirba suna da takamaiman salon yin aikinsu. Hakazalika, za mu tabbata cewa amincinmu wajen yin amfani da salon da aka gwada na wa’azi zai kasance da nasara. Bulus ya gaya wa ’yan’uwa Kiristoci: “Ina roƙonku . . . ku zama masu-koyi da ni.” (1 Korinthiyawa 4:16) Da Bulus ya sadu da dattawa na Afisawa a Militus, ya tunasar da su cewa bai ji nauyin koyar da su ‘gida gida ba da kuma a sarari.’ (Ayukan Manzanni 20:20, 21) Abokin tafiyar Bulus Timothawus ya koyi salon manzon saboda haka ya koyar wa Korinthiyawa wannan. (1 Korinthiyawa 4:17) Allah ya albarkaci salon wa’azi na Bulus, kamar yadda zai albarkaci jimirinmu a wa’azin bishara a sarari da kuma gida gida, komawa ziyara, nazarin Littafi Mai Tsarki, da kuma a dukan inda za a samu mutane.—Ayukan Manzanni 17:17.

20. Ta yaya Yesu ya nuna cewa da akwai aikin girbi mai yawa, kuma ta yaya wannan ya kasance gaskiya a shekarun baya bayan nan?

20 Bayan ya yi wa’azi ga wata mata daga Samariya a kusa da Sukar a shekara ta 30 A.Z., Yesu ya yi maganar girbi na ruhaniya. Ya gaya wa almajiransa: “Ku tada idanunku, ku duba gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi. Mai-girbi ya kan sami hakki, yana kuwa tattara hatsi zuwa rai na har abada; domin mai-shuka da mai-girbi su yi farinciki tare.” (Yohanna 4:34-36) Wataƙila Yesu ya riga ya ga sakamakon saduwarsa da mace ’yar Samariya, domin da yawa sun ba da gaskiya a gare shi domin shaidar da ta bayar. (Yohanna 4:39) A shekarun baya bayan nan, ƙasashe da yawa sun ɗaga takunkuminsu bisa Shaidun Jehovah ko kuma sun ba su izini, ta haka sun buɗe filin yin girbi. Sakamakon haka shi ne ana kan aikin girbi na ruhaniya mai yawa. Babu shakka, a dukan duniya, an samu albarka ƙwarai yayin da muka ci gaba da farin ciki wajen aikin girbi na ruhaniya.

21. Me ya sa muke da dalilin ci gaba mu magirba masu farin ciki?

21 Lokacin da iri ya nuna yana jiran girbi, magirba dole ne su yi aiki da gaggawa. Dole ne su yi aiki babu ɓata lokaci. A yau, muna bukatar mu yi aiki da ƙwazo da kuma gaggawa domin muna rayuwa ne a “kwanakin ƙarshe.” (Daniel 12:4) Hakika, muna fuskantar gwaji, amma da akwai girbi na masu bauta wa Jehovah fiye da dā. Saboda haka wannan rana ce ta farin ciki. (Ishaya 9:3) Bari mu ci gaba cikin aikin girbi, mu magirba masu farin ciki!

[Hasiya]

a Shaidun Jehovah ne suka buga kuma suka rarraba.

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya Ubangijin girbi ya amsa roƙon aikawa da ƙarin ma’aikata?

• Ko da yake mu “abin ƙi” ne, wane hali muke kiyaye?

• Me ya sa muke farin ciki ko da ana tsananta mana?

• Me ya sa ya kamata mu jimre a aikinmu na girbi da gaggawa?

[Hotuna a shafi na 15]

Waɗanda suke saka hannu cikin girbi na ruhaniya mala’iku suna tallafa musu

[Hoto a shafi na 16]

Zagayar sanarwa ta jawo hankalin mutane da yawa ga saƙon Mulki

[Hoto a shafi na 16]

Muna shuki da ban ruwa, amma Allah yake sa ya yi girma

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba