Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 8/1 pp. 8-13
  • Ku Zama Magirba Masu Farin Ciki!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Zama Magirba Masu Farin Ciki!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • An Aike Su Su Zama Magirba
  • Saƙonmu na Bege
  • Nema Mai Nasara
  • Ka Riƙe Salama a Aikin Girbi
  • Buri Mai Kyau ga Magirba
  • Ci Gaba da Farin Ciki a Girbin
  • Ku Ci Gaba A Aikin Girbi!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Gonaki Sun Yi Fari Sun Isa Girbi
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Sakamakon Yin Wa’azi​—“Gonaki Sun Riga Sun Yi Fari Kuma Sun Isa Girbi”
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Ka Sa Hannu Sosai A Yin Babban Girbi Na Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 8/1 pp. 8-13

Ku Zama Magirba Masu Farin Ciki!

“Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aike ma’aikata cikin girbinsa.”—MATTA 9:37, 38.

1. Me yake taimakonmu mu ci gaba wajen yin nufin Allah?

IDAN muka tuna da ranar baftismarmu don mu zama bayin Jehovah, ko ta auku shekaru kaɗan ne da suka shige ko da yawa, sai ya zama kamar jiya jiya ne ya faru. Yabon Jehovah ya zama muhimmin abu a cikin keɓaɓɓiyar rayuwarmu. Yayin da muka ba da lokaci domin mu taimake wasu su ji kuma wataƙila su karɓi saƙon Mulki, hidima da farin ciki ga Jehovah ita ce babbar aba da ta dame mu. (Afisawa 5:15, 16) Har zuwa yau, muna ganin lokaci yana shigewa da wuri ainun yayin da muka shagala “cikin aikin Ubangiji.” (Korinthiyawa 15:58) Ko da yake, muna samun wasu matsaloli, farin cikinmu wajen yin nufin Jehovah yana motsa mu mu ci gaba.—Nehemiah 8:10.

2. Menene suke sa mu sami farin cikinmu da muke da shi a aikin girbi na alama?

2 Mu Kiristoci, mun shagala cikin aikin girbi na alama. Yesu Kristi ya kwatanta tara mutane domin rai madawwami da girbi. (Yohanna 4:35-38) Tun da muna saka hannu cikin wannan aiki na girbi, yana da kyau mu binciki farin cikin Kiristoci na farko waɗanda magirba ne. Za mu bincika abubuwa uku da suke sa mu sami farin ciki da muke da shi a aikin girbi na yau. Waɗannan sune (1) saƙonmu na bege, (2) nasarar nema da muke yi, da kuma (3) halinmu na salama na magirba.

An Aike Su Su Zama Magirba

3. A wace hanya ce mabiyan Yesu na farko suka sami farin ciki?

3 Rayuwar magirba na farko—musamman ma manzannin Yesu masu aminci 11—ya canja a shekara ta 33 A.Z., a ranar da suka je dutsen Galili su sadu da Kristi da ya tashi daga matattu! (Matta 28:16) “ ’Yan’uwa, sun yi hamsaminya” da suke wajen a wannan lokacin. (1 Korinthiyawa 15:6) Aiki da Yesu ya ba su suna tunawa da shi. Ya gaya musu: “Ku tafi . . . ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:19, 20) Duk da tsanantawa mai tsanani, suna samun farin ciki sosai wajen aikin girbi yayin da suke ganin ana kafa ikilisiyoyin mabiyan Kristi a wurare da yawa. Da shigewar lokaci, an yi “bishara . . . , wadda aka yi wa’azinta cikin dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.”—Kolossiyawa 1:23; Ayukan Manzanni 1:8; 16:5.

4. A wane irin yanayi ne aka aike almajiran Kristi?

4 Da farko cikin hidimarsa a Galili, ya tare manzanninsa 12 ya aike su musamman su sanar: “Mulkin sama ya kusa.” (Matta 10:1-7) Shi da kansa “ya yi yawo cikin dukan birane [na Galili] da ƙauyuka, yana koyarwa cikin majami’unsu, yana wa’azin bishara ta mulkin, yana warkadda kowace irin cuta da kowane irin rashin lafiya.” Yesu ya ji tausayin taron domin “suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Matta 9:35, 36) Abin ya motsa shi ƙwarai, sai ya gaya wa almajiransa: “Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi [Jehovah Allah], shi aike ma’aikata cikin girbinsa.” (Matta 9:37, 38) Bukatar magirba da Yesu ya kimanta lokacin, wata shida kawai ne ya rage a hidimarsa ta duniya daidai yake da na Yahudiya. (Luka 10:2) A duk lokacin, ya aike mabiyansa su yi aikin girbi.—Matta 10:5; Luka 10:3.

Saƙonmu na Bege

5. Wane irin saƙo muke sanarwa?

5 Mu bayin Jehovah na zamani, muna amsa kira na bukatar magirba da farin ciki. Abu ɗaya da yake ƙara mana farin ciki shi ne muna idar da saƙonmu na bege ga waɗanda suka razana da kuma waɗanda suka raunana a zuci. Kamar almajiran Yesu na ƙarni na farko, gata ce ƙwarai mu sanar da bisharar—saƙon bege na gaske—ga waɗanda “suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi”!

6. Wane aiki ne manzanni suka yi a ƙarni na farko?

6 A tsakiyar ƙarni na farko, manzo Bulus ya shagala yana wa’azin bishara. Kuma babu shakka, aikinsa na girbi ya yi kyau, domin da yake rubuta wa Kiristoci a Koranti a kusan shekara ta 55 K.Z., ya ce: “ ’Yan’uwa, ina sanarda ku bishara wadda na yi muku wa’azinta, wadda kuka karɓa, inda ku ke tsayawa.” (1 Korinthiyawa 15:1) Manzannin da kuma wasu Kiristoci na farko magirba ne masu ƙwazo. Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai gaya mana ko manzanni nawa ne suka tsira daga aukuwa da ba za a manta da ita ba da ta ƙare a halakar Urushalima a shekara ta 70 A.Z., mun san cewa manzo Yohanna ya yi wa’azi shekaru na 25 daga baya.—Ru’ya ta Yohanna 1:9.

7, 8. Wane saƙon bege ne bayin Jehovah suke sanarwa da gaggawa fiye da dā?

7 Sai kuma ƙarnukan mallaka ta limaman Kiristendam, ɗan ridda, “mutumin zunubi.” (2 Tassalunikawa 2:3) Amma dai, kusan ƙarshen ƙarni na 19, waɗanda suke so su yi rayuwa daidai da Kiristanci na dā suka ɗauki saƙon bege, suna shelar Mulki. Hakika, tun daga fitar farko a (Yuli 1879) jigon wannan jaridar yana ɗauke da waɗannan kalmomi “Shelar bayyanar Kristi,” “Shelar Mulkin Kristi,” ko kuma “Shelar Mulkin Jehovah.”

8 An kafa Mulkin Jehovah na samaniya ta hannun Yesu Kristi a shekara ta 1914, kuma yanzu muna shelar saƙon bege da gaggawa fiye da dā. Me ya sa? Domin albarka ɗaya na Mulkin shi ne ƙarshen wannan mugun tsarin abubuwa da ya kusa. (Daniel 2:44) Wane saƙo ne zai fice wannan? Kuma wane farin ciki za mu samu fiye da sanar da Mulkin kafin “ƙunci mai-girma” ya fara?—Matta 24:21; Markus 13:10

Nema Mai Nasara

9. Wane umurni Yesu ya bai wa almajiransa, kuma yaya mutane suka ɗauki saƙon?

9 Wani abin da yake ƙara mana farin ciki mu magirba shi ne nasararmu wajen neman waɗanda suke zama almajirai suke haɗuwa da mu wajen aikin girbi. A shekara ta 31-32 A.Z., Yesu ya umurci almajiransa: “Kowane birni ko ƙauye inda kuka shiga, a cikinsa ku nemi wanda ya cancanta.” (Matta 10:11) Ba dukan mutane ba ne suka cancanta, kamar yadda amsarsu ga saƙon Mulkin ya nuna. Duk da haka, almajiran Yesu suka yi wa’azin bishara da ƙwazo a dukan inda mutane suke.

10. Ta yaya Bulus ya yi nasa neman waɗanda suka cancanta?

10 Bayan mutuwar Yesu da kuma tashinsa daga matattu, neman waɗanda suka cancanta ya ci gaba da kuzari. Bulus ya yi muhawwara da Yahudawa a cikin majami’arsu da kuma mutane da ya gamu da su a kasuwa a Atina. Lokacin da ya yi wa’azi a Ariyabagi a cikin birnin Helas, “waɗansu mutane suka manne masa, suka bada gaskiya: ga kuwa Diyonisiyus Ba-ariyabagi a cikinsu, da wata mace, sunanta Damaris, da waɗansu kuma tare da su.” Ko’ina Bulus ya je, abin koyi ne wajen wa’azi “gida gida . . . [kuma a] sarari.”—Ayukan Manzanni 17:17, 34; 20:20.

11. Waɗanne hanyoyi na yin hidima aka yi amfani da su shekaru da yawa da suka shige?

11 A shekarun ƙarshe na ƙarni na 19, Kiristoci shafaffu suka shiga neman waɗanda sun cancanta da gaba gaɗi. A wani talifi mai jigo “An Shafa Su Su Yi Wa’azi,” Zion’s Watch Tower na Yuli/Agusta shekara ta 1881 ya ce: “Wa’azin bishara . . . yana ci gaba wajen ‘masu tawali’u—waɗanda suke so su ji kuma sukan ji, saboda ya gina a tsakaninsu jikin Kristi, waɗanda za su yi sarauta da shi.” Magirba na Allah sau da yawa suna samun mutane ne lokacin da waɗannan suke fitowa daga coci suna ba su warƙa da suke ɗauke da saƙonnin Nassosi da aka shirya domin waɗanda suka cancanta su yi na’am da shi. Bayan an bincika muhimmancin wannan hanyar wa’azi, Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu, 1903, (Turanci) ta aririci magirba su rarraba warƙar “gida gida, ranar Lahadi da rana.”

12. Ta yaya muka kyautata aikin wa’azinmu? Ka ba da misali.

12 A shekarun baya bayan nan, mun faɗaɗa hidimarmu ta wajen gamuwa da mutane a wasu wurare ba a gidajensu ba kawai. Wannan ya kasance da amfani ƙwarai a ƙasashe da tattalin arziki da kuma shaƙatawa suke fid da mutane a gidajensu a lokatai da mukan zo. Da wata Mashaidiya da abokiyarta suka lura cewa baƙi suna tashi a kai a kai cikin safā bayan sun shaƙata a bakin teku, suka yi gaba gaɗi suka shiga safā safā suna ba da Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! ga fasinjojin. A cikin wata guda, suka rarraba jaridu wajen 229. Suka ce: “Ba ma tsoron wa’azi a bakin teku, a kasuwa, ko kuma wani abin da za mu fuskanta domin mun sani cewa Jehovah yana tare da mu ko da yaushe.” Suka kafa inda suke ba da jaridu, suka fara nazarin Littafi Mai Tsarki na gida, kuma dukansu sun yi hidima ta majagaba ta ɗan lokaci.

13. Wane gyara ake bukata a hidimarmu yanzu a wasu wurare?

13 Yayin da neman waɗanda suka cancanta ya ci gaba, sake bincika hidimarmu zai zama dole a wasu wurare. Ko da yawancin Shaidun suna yin wa’azi ta hanyar nan na gida gida ranaikun Lahadi da safe, a wasu wurare sun ga cewa ziyara da safe ba ta samun nasara sosai domin wataƙila mutanen suna barci. Ta wajen gyara tsarin aikinsu, yawancin Shaidun yanzu suna fita fage da rana, wataƙila bayan taron Kirista. Kuma wannan neman ya kasance da albarka. Bara adadin masu shelar Mulki ya ƙaru da fiye da kashi biyu bisa ɗari. Wannan ya daraja Ubangijin girbin kuma ya faranta mana rai.

Ka Riƙe Salama a Aikin Girbi

14. Da wane hali muke gabatar da saƙonmu, kuma me ya sa?

14 Wani dalilin farin cikinmu yana da alaƙa ne da halin salama da muke nunawa a aikin girbin. Yesu ya ce: “Da shigarku cikin gida kuma, ku gaishe shi. Idan gidan ya cancanta, salamarku ta sauka bisansa.” (Matta 10:12, 13) Gaisuwa ta Ibraniyanci da kuma ta Helenanci a cikin Littafi Mai Tsarki suna nufin ‘Ka kasance lafiya.’ Wannan halin yake ja-gorar yadda muke tunƙarar mutane lokacin da muke wa’azin bishara. Begenmu shi ne za su yi na’am da saƙon Mulkin. Ga waɗanda suka yi haka, suna da damar sulhuntawa da Allah yayin da suka tuba daga zunubansu, suka juyo, suka yi nufinsa. Haka kuma, salama da Allah tana kai ga rai madawwami.—Yohanna 17:3; Ayukan Manzanni 3:19; 13:38, 48; 2 Korinthiyawa 5:18-20.

15. Ta yaya za mu riƙe halin salama yayin da muke fuskantar hali da babu kyau a aikinmu na wa’azi?

15 Ta yaya za mu riƙe salamarmu idan ba a yi na’am ba da saƙonmu? Yesu ya ba da umurni: “Idan [gidan] ba ya cancanta, salamarku ta komo gareku.” (Matta 10:13) Labarin Luka game da aika almajirai 70 ya haɗa da kalamin Yesu: “Idan ɗan salama yana nan, salamarku za ta zama a kansa: in ba shi, sai ta komo muku kuma.” (Luka 10:6) Lokacin da muka tunƙari mutane da bishara, muna yin haka daidai cikin hali mai kyau kuma cikin salama. Mai gida da ya nuna ba ya so, yana ƙara, ko kuma yin baƙar magana, yana sa saƙonmu na salama ya ‘komo mana ne.’ Amma babu ɗaya cikin wannan da ke hana mu farin ciki, ’yar ruhu mai tsarki na Jehovah.—Galatiyawa 5:22, 23.

Buri Mai Kyau ga Magirba

16, 17. (a) Menene burinmu yayin da muka koma ziyara? (b) Ta yaya za mu taimake waɗanda suke da tambayoyi daga Littafi Mai Tsarki?

16 Mu magirba muna farin cikin saka hannu cikin tara mutane domin rai madawwami. Kuma muna farin ciki yayin da mutum wanda muka yi wa wa’azi ya yi na’am, ya so ya koya, kuma ya kasance “ɗan salama”! Wataƙila yana da tambayoyi daga Littafi Mai Tsarki kuma ba zai yiwu ba mu amsa duka tambayoyin a lokacin ziyararmu na ɗaya kawai. Tun da yake daɗewa ainu a ziyara na farko ba zai dace ba, menene za mu yi? Za mu iya tsai da buri kamar wanda aka shawarta shekara 60 da ta shige.

17 “Dukan Shaidun Jehovah ya kamata su shirya su yi nazarin gurbi da wasu cikin Littafi Mai Tsarki.” Wannan maganar ta bayyana a na uku a jerin Model Study littafin umurni da aka buga daga shekara ta 1937 zuwa ta 1941. Ya ci gaba da cewa: “Dukan masu shelar [Mulki] ya kamata su kasance da ƙwazo wajen taimakon mutane masu zuciyar kirki da suka nuna suna son saƙon Mulki a kowacce hanya. Komowa [koma ziyara] ya kamata a yi shi ga waɗannan mutane, a amsa tambayoyinsu iri-iri . . . sai kuma a fara gurbin yin nazari . . . nan da nan yadda za ka iya.” Hakika, burinmu a koma ziyara domin mu fara nazarin Littafi Mai Tsarki ne kuma mu gudanar da shi a kai a kai.a Kasancewa da abokantaka da kuma damuwa ta ƙauna ga mutane da suke nuna suna so zai sa mu shirya sosai kuma mu gudanar da nazarin da kyau.

18. Ta yaya za mu taimake sababbi su zama almajiran Yesu Kristi?

18 Tare da taimakon littafi nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada da kuma mujallar nan Minene Allah ke Bukata Daga Garemu?, za mu iya gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida da kyau kuma mu saka hannu wajen taimakon mutane da suke son yin nazari su zama almajirai. Yayin da muke ƙoƙari mu zama kamar Babban Malami, Yesu Kristi, wataƙila waɗannan ɗaliban Littafi Mai Tsarki za su koya daga halinmu na salama, farin ciki, na yin gaskiya, da kuma daraja da muke ba wa mizanan Jehovah da kuma ja-gorarsa. Lokacin da muka taimake sababbin mutane muka amsa tambayoyinsu, bari mu yi abin da za mu iya mu ma mu koya musu yadda za su amsa tambayoyin da wasu suka tambaye su. (2 Timothawus 2:1, 2; 1 Bitrus 2:21) Yadda muke magirba na alama, babu shakka za mu yi farin ciki cewa matsakaicin nazarin Littafi Mai Tsarki na gida 4,766,631 ne muka gudanar a dukan duniya a wannan shekarar hidima da ta shige. Musamman ma mun fi farin ciki idan muna tsakanin magirba waɗanda suka saka hannu cikin ayyukan nazarin Littafi Mai Tsarki na gida.

Ci Gaba da Farin Ciki a Girbin

19. Me ya sa da kyakkyawan dalilai na farin ciki a girbi a lokacin hidimar Yesu da kuma jim kaɗan bayan haka?

19 Lokacin hidimar Yesu da akwai kyakkyawan dalilan farin ciki a girbi da kuma jim kaɗan bayan haka. Da yawa sun yi na’am da bisharar. Farin ciki musamman ya yi yawa a Fentikos na shekara ta 33 A.Z., domin wasu 3,000 a lokacin sun karɓi ja-gorar Bitrus, sun sami ruhu mai tsarki na Jehovah, kuma sun zama sashen al’ummar Allah ta Isra’ila na ruhaniya. Babu shakka, adadinsu ya ci gaba da ƙaruwa kuma farin ciki ya ƙaru yayin da “Ubangiji kuma yana tattarawa yau da gobe waɗanda a ke cetonsu.”—Ayukan Manzanni 2:37-41, 46, 47; Galatiyawa 6:16; 1 Bitrus 2:9.

20. Me yake kawo mana farin ciki sosai a aikinmu na girbi?

20 A wannan lokacin, annabcin Ishaya ya kasance gaskiya: “Ka [Jehovah] yawaita al’ummar, ka ƙara musu farinciki: suna murna a gabanka irin murnata kaka, kamar yadda mutane su ke murna sa’anda su ke rarraba ganima.” (Ishaya 9:3) Ko da yake yanzu mun ga wannan ‘yawaitacciyar al’ummar’ na shafaffu ya kusa ya cika, farin cikinmu yana yawa yayin da muka lura da adadin wasu magirba yana ƙaruwa shekara shekara.—Zabura 4:7; Zechariah 8:23; Yohanna 10:16.

21. Menene za mu tattauna a talifi na gaba?

21 Babu shakka muna da kyawawan dalilai mu ci gaba da farin ciki a aikin girbi. Saƙonmu na bege, neman da muke yi na waɗanda suka cancanta, da kuma halinmu na salama—dukan waɗannan abubuwa suna kawo mana mu magirba farin ciki. Duk da haka, suna kawo rashin na’am daga mutane da yawa. Manzo Yohanna ya shaida hakan. An ɗaure shi a tsibirin Batmusa “sabili da maganar Allah da shaidar Yesu.” (Ru’ya ta Yohanna 1:9) To, ta yaya za mu riƙe farin cikinmu lokacin da muka fuskanci tsanantawa ko kuma hamayya? Menene zai taimake mu jimre wa taurin hali na mutane da yawa da muke yi wa wa’azi a yau? Talifinmu na gaba ya ba da taimako na Nassi wajen amsa waɗannan tambayoyin.

[Hasiya]

a Da farko an shirya nazari a wurare inda rukunin mutanen da suke nuna suna so za su taru. Ba da daɗewa ba, aka fara nazari da mutane ɗaɗɗaya da kuma iyalai.—Dubi Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, shafi na 574, Shaidun Jehovah ne suka buga.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene aikin girbi na alama?

• Wane irin saƙo ne muke sanarwa?

• Me ya sa neman almajirai da muke yi yake nasara?

• Ta yaya za mu riƙe salama a aikin girbi?

• Me ya sa muke ci gaba da farin ciki a girbi?

[Hotuna a shafuffuka na 10, 11]

Wa’azi a ƙarni na ɗaya da kuma na 20

[Hotuna a shafi na 11]

Kamar Bulus, magirba na zamani suna ƙoƙarin su isa mutane a ko’ina

[Hoto a shafi na 11]

Ka yi shelar bishara da farin ciki

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba