Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • kr babi na 9 pp. 87-97
  • Sakamakon Yin Wa’azi​—“Gonaki Sun Riga Sun Yi Fari Kuma Sun Isa Girbi”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sakamakon Yin Wa’azi​—“Gonaki Sun Riga Sun Yi Fari Kuma Sun Isa Girbi”
  • Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Gayyata don Aiki da Ke Sa Farin Ciki
  • Sarkinmu Yana Ja-gora a Aikin Girbi Mafi Muhimmanci a Tahiri
  • An Yi Amfani da Kwatanci Wajen Annabta Sakamakon Girbin
  • Dalilin da Ya Sa Dukan Bayin Jehobah Suke Farin Ciki
  • “Daga Fitowar Rana Har Faɗuwarta”
  • Ku Ci Gaba A Aikin Girbi!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Gonaki Sun Yi Fari Sun Isa Girbi
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Ku Zama Magirba Masu Farin Ciki!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ka Sa Hannu Sosai A Yin Babban Girbi Na Ruhaniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Mulkin Allah Yana Sarauta!
kr babi na 9 pp. 87-97

BABI NA 9

Sakamakon Yin Wa’azi​—“Gonaki Sun Riga Sun Yi Fari Kuma Sun Isa Girbi”

MANUFAR WANNAN BABIN

Jehobah ya sa iri na saƙon Mulkin ya bunƙasa

1, 2. (a) Me ya sa almajiran Yesu suka rikice? (b) Wane irin girbi ne Yesu ya yi maganarsa?

YESU ya gaya wa almajiransa cewa: “Ku tāda idanunku, ku duba gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi.” Kalaman nan sun ɗan rikitar da almajiransa. Sun kalli filin da Yesu ya nuna musu, amma ba su ga gonar da ta isa girbi ba domin ba a daɗe da shuka sha’ir ba. Mai yiwuwa sun yi mamaki, ‘Wane girbi ke nan, tun da yake za a yi watanni kafin a soma girbin sha’ir?’—Yoh. 4:35.

2 Amma ba girbi na zahiri ne Yesu yake magana a kai ba. Maimakon haka, yana amfani da wannan damar ce don ya koya wa almajiransa muhimman darussa biyu game da girbi na alama, wato tattara mutane zuwa cikin ikilisiyar Kirista. Waɗanne darussa ke nan? Domin mu sami amsar wannan tambayar, bari mu tattauna labarin dalla-dalla.

Gayyata don Aiki da Ke Sa Farin Ciki

3. (a) Mene ne wataƙila ya sa Yesu ya ce: “Gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi”? (Ka duba ƙarin bayani.) (b) Ta yaya Yesu ya bayyana kalmominsa?

3 Yesu ya tattauna da almajiransa a ƙarshen shekara ta 30 a zamaninmu, a kusa da garin Samariyawa da ake kira Sukar. Sa’ad da almajiransa suka shiga cikin gari, Yesu ya zauna a bakin wata rijiya kuma ya yi ma wata mata wa’azi. Matar ta fahimci koyarwarsa nan da nan. Sa’ad da almajiran Yesu suka dawo, sai matar ta gaggauta zuwa garin Sukar don ta gaya wa maƙwabtanta abin al’ajabi da ta koya. A sakamakon haka, maƙwabtanta da yawa sun yi jerin gwano zuwa wurin Yesu. Wataƙila a lokacin ne Yesu ya kalli filin kuma ya hangi Samariyawa masu ɗimbin yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce: “Ku tā da idanunku, ku duba gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi.”a Sai ya bayyana cewa ba girbi na zahiri yake magana a kai ba, amma na alama ne. Yesu ya ce: “Mai-girbi . . . yana kuwa tattara hatsi zuwa rai na har abada.”—Yoh. 4:5-30, 36.

4. (a) Waɗanne darussa biyu ne Yesu ya koyar game da girbin? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika amsoshinsu?

4 Waɗanne muhimman darussa biyu ne Yesu ya koyar game da girbin? Na farko, aikin na gaggawa ne. Sa’ad da Yesu ya ce ‘gonaki sun . . . yi fari, sun isa girbi,’ yana so almajiransa su ɗauki mataki. Domin Yesu ya nanata wa almajiransa gaggawar zancen, sai ya ce: “Mai girbi na samun lada.” Hakika, an riga an soma girbin kuma bai kamata a ɓata lokaci ba! Na biyu, masu girbin suna farin ciki. Yesu ya ce masu shuki da masu girbi za su “yi farin ciki tare.” (Yoh. 4:35b, 36, Littafi Mai Tsarki) Kamar yadda Yesu ya yi farin ciki sa’ad da ya lura cewa ‘Samariyawa da yawa sun ba da gaskiya gare shi,’ hakan ma almajiransa za su yi farin ciki yayin da suke yin girbi da zuciya ɗaya. (Yoh. 4:39-42) Wannan abin da ya faru a ƙarni na farko yana da muhimmanci sosai a yau. Me ya sa? Domin yana nuna abin da ke faruwa a yau, yayin da ake yin girbi mafi girma a tarihi. A yaushe ne aka soma wannan girbin? Su waye ne suke yin girbin? Kuma wane sakamako ake samu?

Sarkinmu Yana Ja-gora a Aikin Girbi Mafi Muhimmanci a Tahiri

5. Waye ne yake ja-gorantar aikin girbin da ake yi a faɗin duniya, kuma ta yaya wahayin da aka saukar wa Yohanna ya nuna cewa aikin na gaggawa ne?

5 A wahayin da Jehobah ya saukar wa manzo Yohanna, ya nuna cewa ya danƙa wa Yesu hakkin yin ja-gora a wannan aikin girbin. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 14:14-16.) A wannan wahayin, an nuna Yesu sanye da rawani kuma yana riƙe da lauje. Wannan “rawani na zinariya” da ke kan Yesu yana nuna cewa shi Sarki ne. “Lauje mai-ƙaifi” da ke hannunsa ya tabbatar da matsayinsa na Mai-girbi. Domin Jehobah ya yi amfani da mala’ika kuma ya ce “amfanin duniya ya” nuna sosai, Yana nanatawa ne cewa aikin na gaggawa ne. Hakika, ‘sa’ar girbi ta yi,’ kuma babu damar ɓata lokaci! Sa’ad da Allah ya gaya wa Yesu, “miƙa laujenka,” sai Yesu ya ja laujensa, kuma ya girbe duniya, wato, ya tattara mutane a duniya zuwa cikin ikilisiyar Kirista. Wannan wahayin ya tuna mana cewa ‘gonaki sun . . . yi fari, sun isa girbi.’ Shin wannan wahayin ya taimaka mana mu san lokacin da aka soma wannan girbin? Ƙwarai kuwa!

6. (a) A yaushe ne aka shiga “lokacin kaka”? (b) A yaushe ne aka soma girbe “amfanin duniya”? Ka bayyana.

6 Tun da wahayin da Yohanna ya gani da ke littafin Ru’ya ta Yohanna sura 14 ya nuna Yesu wanda shi ne Mai-girbin, sanye da rawani (aya ta 14), hakan ya nuna cewa ya riga ya soma Sarauta a shekara ta 1914. (Dan. 7:13, 14) Jim kaɗan bayan haka, an umurce Yesu ya soma girbi (aya ta 15). An kwatanta irin wannan aukuwar ma a kwatancin da Yesu ya ba da game da alkama. Ya ce: “Kaka kuma matuƙar zamani ce.” Saboda haka, lokacin kaka da kuma matuƙar zamani sun fara ne a lokaci guda, wato a shekara ta 1914. Daga baya ne aka fara ainihin girbin a “lokacin kaka.” (Mat. 13:30, 39) Idan muka lura sosai, za mu ga cewa an soma girbin ne ’yan shekaru bayan Yesu ya soma Sarauta. Da farko, daga shekara ta 1914 zuwa farkon 1919, Yesu ya tsarkake mabiyansa shafaffu. (Mal. 3:1-3; 1 Bit. 4:17) Bayan haka, sai aka soma girbe “amfanin duniya” a shekara ta 1919. Nan da nan, Yesu ya yi amfani da wannan sabon bawan da ba a daɗe da naɗawa ba wajen taimaka wa ’yan’uwanmu su fahimci cewa wa’azi aiki ne na gaggawa. Ka yi la’akari da abin da ya faru.

7. (a) Wane nazari ne ya taimaka wa ’yan’uwanmu su san cewa wa’azi aiki ne na gaggawa? (b) Mene ne aka ƙarfafa ’yan’uwanmu su yi?

7 Hasumiyar Tsaro ta Yuli, 1920, ta ce: “Babu shakka, nazarin Littafi Mai Tsarki da muka yi ya nuna cewa an danƙa wa Kiristoci babban gata na yaɗa saƙon mulkin.” Alal misali, annabcin Ishaya ya taimaka wa ’yan’uwan su ga cewa wajibi ne a yaɗa bisharar Mulkin a dukan duniya. (Isha. 49:6; 52:7; 61:1-3) Ba su san yadda za su yi wannan aikin ba, amma sun yi imani cewa Jehobah zai ba su damar yin hakan. (Karanta Ishaya 59:1.) Da yake ’yan’uwanmu sun ga cewa wa’azi aiki ne na gaggawa, hakan ya ƙarfafa su su yi wa’azi da ƙwazo. Wane mataki ne suka ɗauka?

8. Waɗanne abubuwa biyu game da wa’azi ne ’yan’uwa suka fahimta a shekara ta 1921?

8 Hasumiyar Tsaro ta Disamba, 1921, ta ce: “Babu shekarar da ta fi wannan kyau kuma mutane da yawa sun ji saƙon Mulkin a shekara ta 1921 fiye da shekarun da suka gabata.” Mujallar ta ci gaba da cewa: “Amma, tsugune ba ta ƙare ba tukun. . . . Bari mu yi hakan da farin ciki sosai.” Ka lura da yadda ’yan’uwa suka fahimci waɗannan abubuwa biyu masu muhimmanci da Yesu ya koya wa almajiransa game da wa’azi: Aikin na gaggawa ne kuma masu girbin suna farin ciki.

9. (a) Mene ne Hasumiyar Tsaro ta ce game da aikin girbi a shekara ta 1954, kuma me ya sa? (b) Wace ƙaruwa ce aka samu a adadin masu shela a cikin shekaru 50 da suka shige? (Ka duba jadawalin nan “Ƙaruwa a Faɗin Duniya.”)

9 A tsakanin shekara ta 1930 zuwa 1939, ’yan’uwa sun fahimci cewa waɗanda za su kasance cikin taro mai girma za su saurari saƙon Mulkin, kuma hakan ya sa sun yi wa’azi da ƙwazo sosai. (Isha. 55:5; Yoh. 10:16; R. Yoh. 7:9) Wane sakamako aka samu? An sami ƙaruwa a yawan masu wa’azin Mulki, daga 41,000 a shekara ta 1934 zuwa 500,000 a shekara ta 1953! Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1954, ta ce: “Ruhun Jehobah da kuma ikon Kalmarsa ne suka sa aka cim ma wannan gagarumin aikin girbin da ake yi a faɗin duniya.”b—Zak. 4:6.

ƘARUWA A FAƊIN DUNIYA

Kasa

1962

1987

2013

Ostareliya

15,927

46,170

66,023

Brazil

26,390

216,216

756,455

Faransa

18,452

96,954

124,029

Italiya

6,929

149,870

247,251

Japan

2,491

120,722

217,154

Meziko

27,054

222,168

772,628

Nijeriya

33,956

133,899

344,342

Filifin

36,829

101,735

181,236

Amirka

289,135

780,676

1,203,642

Zambiya

30,129

67,144

162,370

ƘARUWAR ADADIN NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI

1950

234,952

1960

646,108

1970

1,146,378

1980

1,371,584

1990

3,624,091

2000

4,766,631

2010

8,058,359

An Yi Amfani da Kwatanci Wajen Annabta Sakamakon Girbin

10, 11. Waɗanne fasalolin girma ne aka bayyana a kwatancin ƙwayar mustard?

10 A kwatancin da Yesu ya bayar game da Mulkin, ya annabta sakamakon aikin girbin. Bari mu tattauna kwatancin da Yesu ya yi game da ƙwayar mustard da kuma yis. Za mu mai da hankali ne musamman a kan yadda suka cika a kwanaki na ƙarshe.

11 Kwatancin ƙwayar mustard. Wani mutum ya shuka ƙwayar mustard. Sai ƙwayar ta tsira, ta yi girma kuma ta zama bishiya, inda tsuntsaye suke fakewa. (Karanta Matta 13:31, 32.) Waɗanne fasalolin girma ta ƙwayar ce Yesu ya nanata a wannan kwatancin? (1) Yadda ƙwayar ta yi girma yana da ban mamaki. Ƙwayar “da ta fi kowane irin da ke cikin ƙasa ƙanƙanta” ta zama bishiya mai “rassa masu-girma.” (Mar. 4:31, 32) (2) Tabbas, za ta yi girma. ‘Sa’an da aka shuka [irin] tana girma.’ Yesu bai ce, “Wataƙila za ta yi girma ba,” amma ya ce: Tana “girma.” Babu abin da ya isa ya hana ta girma. (3) Yayin da bishiyar take girma, tana jawo hankalin baƙi kuma suna samun mafaka a ƙarƙashinta. ‘Tsuntsayen sama suna sauka ƙarƙashin inuwarta.’ Ta yaya waɗannan fasaloli uku suka shafi aikin girbi da muke yi a yau?

12. Wace nasaba ce ke tsakanin kwatancin ƙwayar mustard da kuma aikin girbi a yau? (Ka kuma duba akwatin nan “Ƙaruwar Adadin Nazarin Littafi Mai Tsarki.”)

12 (1) Girma: Kwatancin ya nuna yadda saƙon Mulkin da kuma ikilisiyar Kirista suka yaɗu sosai. An soma tattara masu girbi da ke da ƙwazo sosai zuwa cikin ikilisiyar Kirista tun daga shekara ta 1919. A lokacin, masu girbin ba su da yawa, amma adadinsu ya ƙaru nan da nan. Hakika, ƙaruwar da aka samu daga farkon shekara ta 1900 zuwa yau ba kaɗan ba ne. (Isha. 60:22) (2) Tabbaci: Babu abin da ya hana ikilisiyar Kirista samun ƙaruwa. Duk da yawan matsin da ƙaramar ƙwayar nan ta fuskanta daga maƙiyan Allah, ta ci gaba da yin girma tana haɓaka. (Isha. 54:17) (3) Wurin Sauka: “Tsuntsayen sama” da suka sauka a itacen suna wakiltar miliyoyin mutane daga ƙasashe wajen 240 da suka saurari saƙon Mulkin kuma suka shiga ƙungiyar Jehobah. (Ezek. 17:23) A nan ne suke samun koyarwar Allah da shaƙatawa da kuma kāriya.—Isha. 32:1, 2; 54:13.

Tsuntsaye dabam-dabam sun fake a itacen mustard

Kwatancin ƙwayar mustard ya nuna cewa ’yan’uwan da ke cikin ƙungiyar Jehobah suna samun wurin fakewa da kuma kāriya (Ka duba sakin layi na 11, 12)

13. Waɗanne fasalolin girma ne aka bayyana a kwatancin yis?

13 Kwatancin Yis. Bayan wata mata ta zuba yis cikin garin fulawa, sai yis ɗin ya game garin. (Karanta Matta 13:33.) Waɗanne fasalolin girma ne aka bayyana a wannan kwatancin? Bari mu tattauna biyu cikinsu. (1) Girman ya kawo sauyi. Yis ɗin ya yaɗu har “ya game” dukan garin fulawar. (2) Girman ko kuma yaɗuwar ta game ko’ina. Yis ɗin ya game “mudu uku na gari.” Ta yaya waɗannan fasaloli biyu suka shafi aikin girbin da muke yi a yau?

14. Wace nasaba ce ke tsakanin kwatancin yis da kuma aikin girbin da muke yi a yau?

14 (1) Sauyi: Yis ɗin yana wakiltar saƙon Mulkin kuma garin fulawar yana wakiltar ’yan Adam. Kamar yadda yis yake canja garin fulawa sa’ad da aka kwaɓa su tare, haka saƙon Mulkin yake sauya ko kuma canja zukatan mutane bayan sun karɓi saƙon. (Rom. 12:2) (2) Zai game ko’ina: Yadda yis ɗin ya yaɗu har ya game dukan garin fulawar yana kwatanta yadda saƙon Mulkin yake yaɗuwa. Kamar yadda yis yake bin cikin fulawar da aka kwaɓa har ya game ta baki ɗaya, haka ma saƙon Mulkin ya yaɗu ‘har iyakan duniya.’ (A. M. 1:8) Wannan sashen kwatancin ya nuna cewa ko da yake mutane ba sa ganin mu muna wa’azi a ƙasashen da aka sa wa aikinmu takunkumi, duk da haka, saƙon Mulkin zai yaɗu.

15. Ta yaya kalmomin Ishaya 60:5, 22 suke cika? (Ka kuma duba akwatunan nan “Jehobah Ya Sa Ya Yiwu,” shafi na 93, da kuma “Yadda ‘Ƙanƙani’ Ya Zama “Al’umma” Mai Girma,” shafuffuka na 96-97.)

15 Shekaru 800 kafin Yesu ya yi waɗannan kwatancin, Jehobah ya yi annabci ta bakin Ishaya game da abubuwan da za a cim ma a aikin girbin nan da kuma farin cikin da hakan zai kawo.c Jehobah ya kwatanta yadda mutane “daga nesa” suke jerin gwano zuwa ƙungiyarsa. Sai ya mai da hankalinsa ga wata ‘mace,’ wadda take wakiltar shafaffun da suka rage a duniya, kuma ya ce: “Za ki gani ki sami haske, zuciyarki kuma ta motsu ta buɗe; domin albarkar teku za ta juya ta nufa wajenki, wadatar al’ummai kuma za ta zo gareki.” (Isha. 60:1, 4, 5, 9) Babu shakka, waɗannan kalmomin suna cika! Bayin Jehobah da suka daɗe suna bauta masa a yau, suna farin ciki domin suna ganin yadda masu shela suke ƙaruwa a ƙasashensu.

Dalilin da Ya Sa Dukan Bayin Jehobah Suke Farin Ciki

16, 17. Wane dalili ne ya sa ‘mai-shuka da mai-girbi suka yi farin ciki tare’? (Ka kuma duba akwatin nan “Yadda Warƙoƙi Biyu Suka Ratsa Zukatan Mutane Biyu a Yankin Amazon.”)

16 Za ka iya tuna cewa Yesu ya gaya wa manzanninsa: “Mai-girbi . . . yana kuwa tattara hatsi zuwa rai na har abada; domin mai-shuka da mai-girbi su yi farin ciki tare.” (Yoh. 4:36) Ta yaya muke ‘farin ciki tare’ a wannan aikin girbin da ake yi a dukan duniya? Muna yin haka a hanyoyi da yawa. Bari mu tattauna uku daga cikinsu.

17 Na farko, muna farin cikin ganin hannun Jehobah a wannan aikin. Muna shuka iri a duk sa’ad da muka yi wa’azin Mulkin. (Mat. 13:18, 19) Muna girbe amfani a duk lokacin da muka taimaka ma wani ya zama mabiyin Kristi. Kuma mu duka muna matuƙar farin ciki sa’ad da muka ga yadda Jehobah yake sa irin “ya tsira” kuma “ya yi girma.” (Mar. 4:27, 28) Wasu daga cikin irin da muka shuka suna yin tsiro daga baya, kuma wasu su girbe su. Wataƙila ka taɓa shaida irin abin da ya faru da wata ’yar’uwa a Biritaniya mai suna Joan wadda ta yi baftisma shekaru 60 da suka wuce. Ta ce: “Na haɗu da mutane da yawa da suka gaya mini cewa na shuka irin gaskiya a zuciyarsu sa’ad da na yi musu wa’azi shekarun baya. Daga baya ba da sanina ba, wasu Shaidun sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su kuma suka taimaka musu su zama bayin Jehobah. Ina farin ciki cewa irin da na shuka ya yi girma kuma an girbe shi.”—Karanta 1 Korintiyawa 3:6, 7.

JEHOBAH YA SA YA YIWU

YESU ya ce: “Abin da ba shi yiwuwa ga mutum ya yiwu ga Allah.” (Luk 18:27) Yawancinmu mun shaida cewa wannan furucin gaskiya ce. Duk da ƙoƙarin da mutane suke yi don su hana mu yin wa’azi, Jehobah ya taimaka mana mu ci gaba da yin hakan.

Zacharie

Zacharie Elegbe (ɗan shekara 66, ya yi baftisma a 1963), ya bayyana yadda takunkumin da aka sa wa aikin Shaidun Jehobah a Jamhuriyar Benin ya taimaka musu: “An sa wa aikinmu takunkumi a shekara ta 1976, sa’ad da muke da masu shela 2,300 a ƙasar kuma hukuma ta ce a sanar da hakan a dukan harsunan ƙasar. Wannan abu ne da bai taɓa faruwa ba. Ko da yake ana yin harsuna sama da 60 a ƙasar Benin, amma a harsuna biyar kawai ake watsa labarai a lokacin. Saboda haka, sa’ad da aka yi sanarwar a dukan harsunan, dubban mutane da ke zama a karkara sun ji game da mu a lokaci na farko. Sun yi mamaki, ‘Su waye ne Shaidun Jehobah kuma me ya sa aka hana aikinsu?’ Daga baya, sa’ad da muka isa waɗannan wuraren, mutane da yawa sun soma bauta wa Jehobah babu ɓata lokaci.” A yau, akwai Shaidu fiye da 11,500 a Jamhuriyar Benin.

Mariya

Mariya Zinich (’yar shekara 74, ta yi baftisma a 1957): “Sa’ad da nake ’yar shekara 12, an ƙaurar da dukan iyalinmu daga ƙasar Ukraine zuwa Siberia, a ƙasar Rasha. Duk da ƙoƙarin da gwamnati ta yi don ta sa mu daina wa’azi a ƙasar Rasha ta dā ba ta yi nasara ba, domin adadinmu ya ci gaba da ƙaruwa. Ganin yadda adadin mu ke ƙaruwa duk da hamayya da muke fuskanta ya sa na kasance da tabbaci cewa aikin da muke yi na Jehobah ne. Babu mutumin da ya isa ya hana mu yin aikin!” Wata ’yar’uwa kuma mai suna Mariya (’yar shekara 73, da ta yi baftisma a 1960) ta ce: “A sakamakon ƙaurar da aka yi wa ’yan’uwanmu zuwa Siberia, gwamnati ta sa mutane da yawa da ke wurare masu nisan gaske su ji saƙon gaskiya kuma su soma bauta wa Jehobah.”

Jesús

Jesús Martín (ɗan shekara 77, da ya yi baftisma a 1955) ya ce: “Sa’ad da na soma bauta wa Jehobah, akwai Shaidu guda 300 a ƙasar Sifen. Amma a shekara ta 1960, an tsananta mana sosai. Gwamnati ta ce ’yan sanda su kakkama dukan Shaidun Jehobah. A lokacin, babu mutumin da zai taɓa yarda cewa za mu yi wa’azin bishara a ƙasar baki ɗaya. Amma a yau, akwai Shaidu kusan 111,000 a ƙasar Sifen. Ganin yadda muka sami ƙaruwa duk da tsanantawar da aka yi mana ya sa na kasance da tabbaci cewa muddin Jehobah yana tare da mu, kome zai yiwu!”

18. Wane dalilin yin farin ciki ne aka ambata a 1 Korintiyawa 3:8?

18 Na biyu, muna farin ciki sa’ad da muka tuna da kalmomin manzo Bulus. Ya ce: ‘Kowane za ya sami nasa lada gwargwadon wahalarsa.’ (1 Kor. 3:8) Ana ba da lada ne dangane da aikin da mutum ya yi, ba dangane da yawan mutanen da muka koya wa gaskiya ba. Hakan abin ƙarfafa ne sosai ga ’yan’uwan da ke wa’azi a yankunan da mutane ƙalila ne kawai suke sauraron saƙon Mulkin. A wurin Allah, duk Mashaidin da ya yi wa’azi da zuciya ɗaya yana “bada ’ya’ya da yawa,” kuma ya kamata ya yi farin ciki.—Yoh. 15:8; Mat. 13:23.

19. (a) Ta yaya annabcin da ke littafin Matta 24:14 yake sa mu farin ciki? (b) Me ya kamata mu tuna ko da ba mu sami damar taimaka wa wani ya soma bauta wa Jehobah ba?

19 Na uku, muna farin ciki domin aikinmu yana cika annabci. Ka yi la’akari da amsar da Yesu ya ba almajiransa sa’ad da suka tambaye shi cewa: “Me ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” Yesu ya gaya musu cewa sashe ɗaya na wannan alamar shi ne wa’azin da za a yi a dukan duniya. Shin yana magana ne game da taimaka wa mutane su soma bauta wa Jehobah? A’a. Ya ce: ‘Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida.’ (Mat. 24:3, 14) Hakan ya nuna cewa wa’azin Mulki, wato shuka iri, sashen alamar ne. Saboda haka, yayin da muke wa’azin Mulkin, ya kamata mu sani cewa ko da ba mu yi nasara wajen taimaka wa wani ya soma bauta wa Jehobah ba, mun ba da “shaida.”d Hakika, ko da mutane sun saurare mu ko a’a, muna saka hannu wajen cika annabcin Yesu kuma muna da gatan zama “abokan aiki na Allah.” (1 Kor. 3:9) Tabbas, wannan dalili mai kyau ne na yin farin ciki!

“Daga Fitowar Rana Har Faɗuwarta”

20, 21. (a) Ta yaya Malakai 1:11 yake cika? (b) Mene ne ƙudurinka game da aikin girbi, kuma me ya sa?

20 A ƙarni na farko, Yesu ya taimaka wa almajiransa su fahimci cewa wa’azi aiki ne na gaggawa. Daga shekara ta 1919, Yesu ya taimaka wa mabiyansa su fahimci hakan. A sakamakon haka, bayin Allah sun sa ƙwazo sosai a wa’azin da suke yi. Hakika, babu abin da ya isa ya hana mu wannan aikin. Kamar yadda Malakai ya annabta, ana yin wannan wa’azin ne “daga fitowar rana har faɗuwarta.” (Mal. 1:11) Hakika, daga fitowar rana har faɗuwarta, wato daga gabas zuwa yamma, ko da a ina suke a duniya, masu shuki da kuma masu girbi suna farin ciki tare. Kuma daga fitowar rana har faɗuwarta, wato daga safiya zuwa yamma, muna yin wa’azi da gaggawa.

21 Idan muka duba muka ga yadda ƙaramin adadin bayin Allah ya yi girma ya zama “al’umma mai-ƙarfi” a cikin shekaru 100 da suka shige, zuciyar kowannenmu ta “motsu” kuma “ta buɗe” saboda farin ciki. (Isha. 60:5, 22) Bari wannan farin cikin da kuma ƙaunarmu ga Jehobah, wanda shi ne “Ubangijin girbi,” ya motsa kowannenmu ya ci gaba da yin iya ƙoƙarinsa wajen yin wannan aikin girbi mafi girma a tarihi!—Luk 10:2.

a Sa’ad da Yesu ya ce ‘gonaki sun rigaya sun yi fari,’ wataƙila yana magana ne game da fararen tufafin da Samariyawan da suke zuwa wurinsa suka saka.

b Domin ƙarin bayani game da wannan lokacin da kuma shekarun da suka biyo baya, muna ƙarfafa ka ka karanta littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, shafuffuka na 425-520, wanda ya bayyana abin da aka cim ma daga shekara ta 1919 zuwa 1992.

c Don ƙarin bayani game da wannan annabcin, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 2002, shafuffuka na 21-31.

d Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun riga sun fahimci wannan muhimmiyar gaskiya a lokacin. Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 1895, ta ce: “Amma idan har za a iya tattara ƙananan alkama, to, za a iya ba da shaida sosai game da gaskiya. . . . Kowa zai iya yin wa’azin bishara.”

Ka Gaskata da Mulkin Kuwa?

  • Mene ne Mulkin ya sa aka cim ma a aikin girbi?

  • Ta yaya kwatancin ƙwayar mustard da kuma yis suka ƙarfafa ka ka yi hidimarka sosai?

  • Mene ne ya kamata ya motsa ka ka yi farin ciki a hidimarka?

YADDA WARƘOƘI BIYU SUKA RATSA ZUKATAN MUTANE BIYU A YANKIN AMAZON

Antônio Simões

Antônio Simões

WANI dattijo mai aminci kuma ɗan shekara 91 mai suna Antônio Simões, ya tuna yadda wasu warƙoƙi biyu da Shaidun Jehobah suka wallafa suka sa mahaifinsa da kawunsa suka soma bauta wa Jehobah. Ya tambayi ma’auratan da suka zo wurinsa, “Kuna so ku ji wannan labarin?” Sai suka ce, “Ƙwarai kuwa!” Antônio ya zauna, ya yi murmushi kuma ya soma ba da labarin.

“Mahaifina mai suna Zeno, mai bishara ne a Cocin Baptist. A shekara ta 1931, ya yi tafiya zuwa wani gari mai nisa a yankin Amazon don ya ziyarci wata ’yar cocinsu. Da ya isa gidanta, sai ya ga wasu warƙoƙi guda biyu. Ta gaya masa cewa ta ga warƙoƙin ne a cocinsu, amma ba ta san mutanen da suka ajiye su a wurin ba. Ɗaya daga cikin warƙoƙin ta yi magana ne game da jahannama, ɗayan kuma game da tashin matattu. Abin da mahaifina ya karanta ya ratsa zuciyarsa sosai. Nan da nan, ya tuna da surukinsa mai suna Guilherme, wanda ya daɗe yana gaya masa: ‘Ban yi imani da jahannama ba. Allah mai ƙauna ba zai halicci irin wannan wurin ba.’ Domin yana ɗokin nuna wa surukinsa waɗannan warƙoƙin, sai mahaifina ya shiga kwalekwalensa kuma ya yi tafiyar awa takwas zuwa Manaquiri, wani ƙauye da ke kusa da birnin Manaus, inda Guilherme yake da zama.

Antônio Simões yana rike da hotuna biyu na ikilisiyoyi biyu na farko a Manaquiri, Jihar Amazonas, a kasar Brazil

Ikilisiya ta farko a Jihar Amazonas a ƙasar Brazil

“Bayan Mahaifina da kuma Kawuna Guilherme sun karanta warƙoƙin, sai suka ce, ‘Wannan ita ce gaskiya!’ Nan da nan, sai suka rubuta wasiƙa zuwa ofishin reshen da ke Brazil cewa suna so a turo musu littattafai. Mahaifina ya daina aikin fasto, kuma shi da kawuna suka soma yin wa’azi a wannan yankin. Mutane sun saurare su sosai kuma a sakamakon haka, an kafa ikilisiya ta farko a Manaquiri cikin shekara guda. Ba da daɗewa ba, mutane 70 daga ƙauyen suka soma halartan taro, kuma hakan ya sa ikilisiyar ta zama mafi girma a ƙasar Brazil a lokacin.” Antônio ya dakata, sai ya ce, “Yadda saƙon Mulkin Allah ya shigo yankin Amazon abin mamaki ne, ko ba haka ba?” Haka ne. Ƙananan iri guda biyu, wato ƙananan warƙoƙi biyu sun yi ’ya’ya a cikin ƙungurmin dajin Amazon, kuma hakan ya kai ga kafa ikilisiya. Kuma a yau, wannan ikilisiyar Manaquiri wadda aka kafa shekaru 83 da suka shige tana ɗaya daga cikin ikilisiyoyi guda 143 a Jihar Amazonas a ƙasar Brazil!

YADDA ‘ƘANƘANI’ YA ZAMA “AL’UMMA” MAI GIRMA

“ƘARAMIN za ya zama dubu, ƙanƙanin kuma za ya zama al’umma mai-ƙarfi [mai girma, NW]: ni, Ubangiji, zan hanzarta wannan a lotonsa.” (Isha. 60:22) Ta yaya wannan annabcin ya cika? Ta yaya cikar annabcin ya shafi Shaidun da suka daɗe suna bauta wa Jehobah?

Börje Nilsson

Börje Nilsson (ɗan shekara 84, ya yi baftisma a 1943): “Na tuna da wani ɗan’uwa shafaffe da ke hidimar majagaba a tsakanin shekara ta 1920 zuwa 1929. Sa’ad da aka ce masa ya yi wa’azi a kusan rabin ƙasar Sweden, bai yi gunaguni ba. Babu shakka, aikin da wannan ɗan’uwan da kuma wasu amintattu a ƙasar suka yi ya kawo sakamako mai kyau! A yau, akwai masu shela sama da 22,000 a ƙasar. Ko da yake na tsufa yanzu, ina so in ci gaba da bauta wa Jehobah. Babu wanda ya san abubuwan da Jehobah yake shirin yi mana a nan gaba.”

Etienne Esterhuyse

Etienne Esterhuyse (ɗan shekara 83, ya yi baftisma a 1942): “Yadda adadin Shaidun Jehobah a Afirka ta Kudu ya ƙaru daga mutane wajen 1,500 a shekara ta 1942 zuwa sama da 94,000 a yau yana ba ni mamaki sosai. Kasancewa cikin wannan ƙungiyar yana ƙarfafa bangaskiyarmu sosai!”

Keith Gaydon

Keith Gaydon (ɗan shekara 82, ya yi baftisma a 1948): “Ganin yadda adadin masu shela a Biritaniya ya ƙaru daga mutane wajen 13,700 a shekara ta 1948 zuwa mutane kusan 137,000 a yau ya tabbatar mini cewa lallai wannan aikin Jehobah ne. Da a ce da ikon ɗan Adam ne, da ba a yi nasara ba. Amma Jehobah ne yake wannan ‘aikin al’ajibi.’”—Fit. 15:11.

Ulrike Krolop

Ulrike Krolop (’yar shekara 77, ta yi baftisma a 1952): “Bayan Yaƙin Duniya na Biyu, imanin ’yan’uwan da suka jimre a lokacin da sojojin Nazi sake tsananta musu, ya ƙarfafa ikilisiyoyi a ƙasar Jamus. Mun yi wa mutane ta’aziya kuma zuciyarmu ba ta dame mu ba sa’ad da muke hakan domin ba mu saka hannu a yaƙin ba. A cikin shekaru 60 da suka gabata, na lura da yadda Allah ya yi wa bayinsa ja-gora da ruhu mai tsarki. A yau, akwai Shaidu sama da 164,000. Babu shakka, hakan sakamako ne mai kyau!”

Mariya Brinetskaya

Mariya Brinetskaya (’yar shekara 77, ta yi baftisma a 1955): “An yi mini baftisma daddare domin kada a kama ni. Daga baya, aka kai mijina wani sansani mai nisa sosai domin shi Mashaidi ne. Amma na ci gaba da yin wa’azi a ƙauyenmu a nan ƙasar Rasha a ɓoye, kuma maƙwabtanmu da yawa sun soma bauta wa Jehobah. A lokacin, babu ’yan’uwa da yawa a ƙasar. Amma a yau, ina farin ciki cewa akwai Shaidu sama da 168,000 a ƙasar Rasha!”

Kimiko Yamano

Kimiko Yamano (’yar shekara 79, ta yi baftisma a 1954): “A shekara ta 1970, sa’ad da na ji cewa muna da masu shela 10,000 a ƙasar Japan, na zub da hawaye saboda farin ciki kuma hakan ya sa na yi wa Jehobah alkawari cewa, ‘Zan kasance da aminci muddin raina.’ Ina matuƙar farin ciki a yau domin muna da masu shela sama da 216,000 a ƙasar!”

Daniel Odogun

Daniel Odogun (ɗan shekara 83): “Akwai masu shela 8,000 a Nijeriya sa’ad da na yi baftisma a shekara ta 1950. Amma a yau, akwai masu shela wajen 351,000 a ƙasar baki ɗaya! A duk lokacin da na halarci babban taro, Adadin mahalartan yana motsa ni sosai kuma yana sa in tuna da littafin Haggai 2:7. Babu shakka, Jehobah yana girgiza al’ummai kuma dukiyoyi suna fitowa. Har ila, ina iya ƙoƙarina a wa’azi domin hanya ce na gaya wa Jehobah cewa, ‘Na gode!’”

Carlos Silva

Carlos Silva (ɗan shekara 79): “Sa’ad da na yi baftisma a shekara ta 1952, akwai Shaidu 5,000 a ƙasar Brazil. A shekarar, mun yi babban taro a wani daƙin motsa jiki a birnin São Paulo. Mutane biyu ne kawai suka kawo motoci wurin. Sai wani ɗan’uwa ya nuna mini wani baban filin wasa da ke kusa kuma ya ce, ‘Kana ganin za mu iya cika wannan wurin kuwa?’ Mun ji kamar hakan ba zai iya yiwu ba, amma a shekara ta 1973, mutane 94,586 ne suka halarci taro a wannan filin wasan! A yau, akwai ’yan’uwa maza da mata sama da 767,000 a ƙasar Brazil. Hakika wannan ƙaruwar abin ban al’ajabi ne!”

Carlos Cázares

Carlos Cázares (ɗan shekara 73): “Sa’ad da na yi baftisma a shekara ta 1954, masu shela guda 10,500 ne a ƙasar Meziko. A lokacin, ana bukatar ƙarin masu wa’azi sosai har aka naɗa ni mai kula da da’ira ina ɗan shekara 21. Ganin yadda Ishaya 60:22 take cika babban gata ne a gare ni. A yanzu haka, akwai masu shela sama da 806,000 a ƙasar, kuma suna gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane sama da miliyan ɗaya! Wannan abin ban al’ajabi ne!”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba