Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • cl babi na 13 pp. 128-137
  • Dokar ‘Jehobah Cikakkiya Ce’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dokar ‘Jehobah Cikakkiya Ce’
  • Ka Kusaci Jehobah
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mai Ba da Doka Mafi Girma
  • Dokar Musa—Taƙaitacciya
  • Doka da ta Nanata Jinƙai da Nuna Rashin Son Zuciya Wajen Hukunci
  • Dokar ta Ɗaukaka Ƙauna
  • Dokokin Allah Don Amfaninmu Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Dokoki Game da Nuna Kauna da Adalci a Isra’ila ta Dā
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Dokar Ƙauna A Zukata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Ka Kusaci Jehobah
cl babi na 13 pp. 128-137
Musa rike da allon dutse guda biyu da ke dauke da Dokoki Goma

BABI NA 13

Dokar ‘Jehobah Cikakkiya Ce’

1, 2. Me ya sa mutane ba su ɗauki doka kome ba, duk da haka yaya za mu ji game da dokar Allah?

“DOKA rami ce marar iyaka, tana . . . haɗiye ko mene ne.” Wannan furucin ya bayyana a wani littafi da aka wallafa a shekara ta 1712. Mawallafinsa ya nuna rashin yardarsa ne game da tsarin doka wanda ƙara a kotu wani lokaci za ta riƙa ja har na wasu shekaru, ta talautar da waɗanda suke nema a yi musu adalci. A ƙasashe da yawa, tsarin kafa doka da yin hukunci sun kasance da wuya, kuma sun cika da rashin adalci, son zuciya, da kuma rashin jituwa, saboda haka ƙyamar dokar ta yi yawa.

2 Akasarin haka ka yi la’akari da kalmomin da aka rubuta shekaru 2,700 da suka shige: “Ina misalin ƙaunata ga Koyarwarka!” (Zabura 119:97) Me ya sa mai Zabura yake da irin wannan ƙaunar sosai? Domin doka da ya yaba wa ba ta kasance daga wata gwamnati ba, amma daga Jehobah Allah ne. Yayin da ka yi nazarin dokar Jehobah, za ka ji kamar yadda mai Zabura ya ji. Irin wannan nazarin zai ba ka fahimi cikin tunani mafi muhimmanci na hanyar hukunci a dukan sararin samaniya.

Mai Ba da Doka Mafi Girma

3, 4. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya kasance Mai Ba da Doka?

3 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa: “Allah ne kaɗai mai ba da Koyarwa, shi ne kuma mai yin shari’a.” (Yakub 4:12) Hakika, Jehobah ne kaɗai Mai Ba da Doka ta gaske. Har tafiyar ababan sammai ma “dokokin sammai” suke musu ja-gora. (Ayuba 38:33, The New Jerusalem Bible) Tsarkakkan mala’ikun Jehobah masu yawa ma dokar Allah ce take yi musu ja-gora, domin an tsara su matsayi matsayi kuma suna bauta ne masu hidima bisa umurnan Jehobah.—Zabura 104:4; Ibraniyawa 1:7, 14.

4 Jehobah ya ba da dokoki ga ’yan Adam ma. Kowanne cikinmu yana da lamiri, nuni ne na shari’ar Jehobah. Doka ce ta ciki, lamirin zai iya taimakonmu bambance tsakanin abin da ke nagari da kuma mugu. (Romawa 2:14) Iyayenmu na farko an albarkace su da kamiltaccen lamiri, saboda haka ba sa bukatar dokoki da yawa. (Farawa 2:15-17) Amma, mutum ajizi yana bukatar dokoki su yi masa ja-gora wajen yin nufin Allah. Iyaye kamar su Nuhu, Ibrahim, da kuma Yakubu sun karɓi dokoki daga Jehobah Allah kuma sun koyar ga iyalansu. (Farawa 6:22; 9:3-6; 18:19; 26:4, 5) Jehobah ya zama Mai Ba da Doka a hanyar da ba ta biyunta lokacin da ya ba wa al’ummar Isra’ila Doka ta hannun Musa. Wannan tsarin doka ya ba mu fahimi ƙwarai bisa shari’ar Jehobah.

Dokar Musa—Taƙaitacciya

5. Shin tsarin dokoki na Dokar Musa tsari ne kawai na dokoki masu yawa kuma masu wuya, me ya sa ka faɗi haka?

5 Mutane da yawa suna tsammanin cewa Dokar Musa tsarin dokoki ne masu yawa, masu wuya. Irin wannan ra’ayin ya yi nesa da gaskiya. Tsarin dokokin ya ƙunshi fiye da dokoki 600. Kamar dai suna da yawa, amma ka yi tunani: A ƙarshen ƙarni na 20, dokokin ƙasa na Amirka sun cika shafuffuka 150,000 na littattafan dokoki. Bayan kowacce shekara biyu ana daɗa dokoki 600! Idan muka yi maganar yawa kawai, yawan dokokin mutane ya wadantar da Dokar Musa. Duk da haka, Dokar Allah ta yi wa Isra’ilawa ja-gora a ɓangarorin rayuwa da dokokin zamani ba su ma fara taɓawa ba tukuna. Ga shi a taƙaice.

6, 7. (a) Mene ne ya bambanta Dokar Musa daga kowane irin tsarin doka, kuma wacce ce babba cikin Dokar? (b) Ta yaya Isra’ilawan za su nuna yardarsu ga ikon mallaka na Jehobah?

6 Dokar ta ɗaukaka ikon mallaka na Jehobah. Saboda haka, Dokar Musa ta fi gaban a gwada ta da kowane tsarin dokoki. Babba cikin dokokin ita ce wannan: “Ku ji, ya jama’ar Isar’ila, Yahweh Allahnmu Yahweh ɗaya ne. Za ku ƙaunaci Yahweh Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da dukan ƙarfinku.” Yaya mutanen Allah za su nuna ƙauna gare shi? Za su bauta masa, su kuma miƙa kai ga ikonsa na mallaka.—Maimaitawar Shari’a 6:4, 5; 11:13.

7 Kowanne Ba’isra’ile zai nuna yardarsa ga ikon mallaka na Jehobah ta wajen saɗaukar da kai ga waɗanda ya ba su iko bisa kansa. Iyaye, hakimai, alƙalai, firistoci, da kuma a ƙarshe sarki dukan waɗannan suna wakiltan ikon Allah ne. Jehobah yana ɗaukar kowane tawaye ga waɗannan tawaye ne gare shi. A wani ɓangare kuma, waɗanda aka ba su iko za su fuskanci fushin Jehobah idan suka bi da mutanensa cikin rashin adalci da kuma mugunta. (Fitowa 20:12; 22:28; Maimaitawar Shari’a 1:16, 17; 17:8-20; 19:16, 17) Saboda haka, da masu iko da waɗanda ake mallaka suna da hakkin ɗaukaka ikon mallaka na Allah.

8. Ta yaya Dokar ta ɗaukaka mizanin Jehobah na tsarki?

8 Dokar ta ɗaukaka mizanin Jehobah na tsarki. Kalmar nan “tsarki” da kuma “tsarkaka” sun bayyana fiye da sau 280 a cikin Dokar Musa. Dokar ta taimaki mutanen Allah su bambance tsakanin abin da yake da tsarki da abin da ba shi da tsarki, ya faɗi abubuwa dabam dabam kusan 70 da za su iya sa Ba’isra’ile ya zama marar tsarki a jiki. Waɗannan dokokin sun yi maganar tsabta ta jiki, abinci, har da kawar da najasa. Irin waɗannan dokokin sun kawo amfani na ban mamaki ga lafiyar jiki.a Amma suna da ma’ana mai zurfi—domin mutanen su ci gaba da kasancewa da tagomashin Jehobah, a ware daga ayyukan zunubi na mugayen al’ummai da suka kewaye da su. Ga misali.

9, 10. Dokar alkawari ta haɗa da waɗanne dokoki ne game da jima’i da kuma haihuwa, kuma waɗanne amfani waɗannan dokoki suka bayar?

9 Tsarin Dokar alkawari ya ce jima’i—har a tsakanin ma’aurata da kuma haihuwa—suna kawo rashin tsarkaka na ɗan lokaci. (Littafin Firistoci 12:2-4; 15:16-18) Irin waɗannan dokoki ba su kushe wa wannan kyautar ba mai tsabta daga Allah. (Farawa 1:28; 2:18-25) Maimakon haka, waɗannan dokokin suna ɗaukaka tsarkakar Jehobah, suna kāre bayinsa daga gurɓacewa. Abin lura ne cewa al’ummai da suka kewaye Isra’ila suna haɗa bauta da jima’i, bukukuwan ni’ima. Addinin Kan’aniyawa ya haɗa da karuwai maza da mata. Aka samo ayyukan rashin kunya mafi muni kuma suka yaɗu. Akasin haka, Dokar ta ware bautar Jehobah gabaki ɗaya daga ayyukan jima’i.b Da wasu amfani har ila.

10 Waɗannan dokokin suna koyar da gaskiya mai muhimmanci.c Kuma ta yaya ake gādar zunubin Adamu daga tsara zuwa tsara? Ba ta wajen jima’i ne da kuma haihuwa ba? (Romawa 5:12) Hakika, Dokar Allah tana tunasar da mutanensa kasancewa ta kullum na zunubi. Dukanmu babu shakka, an haife mu cikin zunubi. (Zabura 51:5) Muna bukatar gafara da kuma ceto domin mu matso kusa da Allahnmu mai tsarki.

11, 12. (a) Dokar ta ɗaukaka wane mizani ne mai muhimmanci na shari’a? (b) Wace kāriya ce game da rashin adalci take ƙunshe cikin Dokar?

11 Dokar ta ɗaukaka kamiltacciyar shari’a ta Jehobah. Dokar ta ɗaukaka mizanin daidaitawa, a batun shari’a. Saboda haka, Dokar ta ce: “Zai zama rai maimakon rai, ido maimakon ido, haƙori maimakon haƙori, hannu maimakon hannu, ƙafa maimakon ƙafa.” (Maimaitawar Shari’a 19:21) A batun laifi, horon zai yi daidai da laifin da aka yi. Wannan ɓangare na shari’ar Allah ya rinjayi Dokar kuma har zuwa yau tana da muhimmanci wajen fahimtar hadayar fansa na Yesu Kristi, kamar yadda Babi na 14 zai nuna.—1 Timoti 2:5, 6.

12 Dokar kuma ta haɗa da kāriya game da yin rashin adalci. Alal misali, ana bukatar aƙalla shaidu biyu domin a tabbatar da gaskiyar tuhuma. Sakamakon shaidan zur yana da tsanani. (Maimaitawar Shari’a 19:15, 18, 19) An haramta cin hanci da rashawa. (Fitowa 23:8; Maimaitawar Shari’a 27:25) Har a hulɗarsu ta kasuwanci, mutanen Allah dole su ɗaukaka mizanai masu girma na shari’a ta Jehobah. (Littafin Firistoci 19:35, 36; Maimaitawar Shari’a 23:19, 20) Wancan tsarin dokoki mai kyau kuma marar son zuciya babbar albarka ce ga Isra’ila!

Doka da ta Nanata Jinƙai da Nuna Rashin Son Zuciya Wajen Hukunci

13, 14. Ta yaya Dokar ta ɗaukaka hukuncin adalci ga ɓarawo da kuma wanda aka yi wa sata?

13 Shin Dokar Musa tarin dokoki ne kawai, ƙagagge, marar jinƙai? A’a! An hure Sarki Dauda ya rubuta: “Koyarwar Yahweh cikakkiya ce.” (Zabura 19:7) Kamar yadda ya sani ƙwarai, Dokar ta ɗaukaka jinƙai da kuma rashin son zuciya. Ta yaya ta yi haka?

14 A wasu ƙasashe a yau, dokar ƙasar kamar dai tana nuna laushin hali da kuma tagomashi ga mai laifi fiye da yadda take yi ga waɗanda aka cuta. Alal misali, ɓarayi za a kai su kurkuku. Har ila, waɗanda aka yi musu sata ba su samu kayansu ba kuma dole su biya haraji kuma a yi amfani da shi wajen ciyar da ɓarayin kuma a ba su wajen kwana. A Isra’ila ta dā, babu kurkuku kamar waɗanda muka san su a yau. Da akwai iyaka game da tsananin horo. (Maimaitawar Shari’a 25:1-3) Ɓarawo dole ya biya wanda ya yi wa sata abin da ya sace. Ƙari ga haka, ɓarawon dole ya biya diyya. Nawa? Ya bambanta. Hakika, an bai wa alƙalai damar su dubi wasu ƙa’idodi, kamar su tuba ta mai zunubin. Wannan zai bayyana dalilin da ya sa diyya da ake bukata daga ɓarawon in ji Littafin Firistoci 6:1-7 bai kai ko kusan abin da aka ƙa’ide ba a Fitowa 22:7.

15. Ta yaya Dokar ta tabbatar da jinƙai da kuma shari’a a batun wanda ya kashe mutum cikin tsausayi?

15 Dokar ta yi la’akari da cewa ba dukan laifi ba ake yi da gangan. Alal misali, idan mutum ya kashe wani cikin tsausayi, ba dole ba ne ya bayar da rai ga rai idan ya yi abin da ke daidai ta wajen gudu zuwa biranen mafaka da aka baza a cikin dukan Isra’ila. Bayan ƙwararrun alƙalai sun bincika batunsa, dole ne ya zauna a birnin mafaka, har sai mutuwar babban firist. Sannan zai sami ’yancin zama a dukan inda ya zaɓa. Ta haka ya amfana daga jinƙai na Allah. A haka, wannan dokar ta nanata muhimmancin ran mutum.—Littafin Ƙidaya 15:30, 31; 35:12-25.

16. Ta yaya Dokar ta kāre wasu hakkoki na mutum?

16 Dokar ta kāre hakkin mutum. Ka yi la’akari da hanyoyin da ta kāre waɗanda ake bi bashi. Dokar ta hana shiga cikin gidan wanda ya ci bashi a kwace kayansa a maimakon bashin. Maimakon haka, wanda aka ci bashinsa zai tsaya a waje wanda ya ci bashin ya fito masa da kayan jingina. Saboda haka, gidan mutumin ba wurin shiga a yi kwace ba ne. Idan mai ba da bashi ya karɓi rigar wanda ya ci bashi jingina, dole ya mayar masa da maraice, domin wanda ya ci bashin wataƙila zai bukaci mayafinsa cikin dare.—Maimaitawar Shari’a 24:10-14.

17, 18. A al’amura na yaƙi, ta yaya Isra’ilawa suka bambanta da wasu al’ummai, kuma me ya sa?

17 Har yaƙi ma yana da ƙa’idodi a cikin Dokar. Mutanen Allah za su yi yaƙi ba domin su cika burin samun iko ko kuma su ci ƙasashe ba ne, amma su kasance wakilan Allah a “yaƙe-yaƙen Yahweh.” (Littafin Ƙidaya 21:14) A yanayi da yawa, Isra’ilawan suna ba da gari da farko. Idan birnin ya ƙi, sai Isra’ilawan su kai masa hari—amma bisa umurnan Allah. Ba kamar sojoji ba a cikin dukan tarihi, sojojin Isra’ila ba a yarda musu su yi wa mata fyaɗe ba ko kuma su yi kisa ba ji ba gani. An dokace su ma su daraja mahallin, kada su tuge itatuwan abokan gāba.d Wasu sojoji ba su da irin wannan hanin.—Maimaitawar Shari’a 20:10-15, 19, 20; 21:10-13.

18 Kana baƙin ciki idan ka ji cewa a wasu ƙasashe ana horar yara su zama sojoji? A Isra’ila ta dā, babu mutumin da ya gaza shekara 20 da zai shiga soja. (Littafin Ƙidaya 1:2, 3) Har wanda ya kai namiji ana ƙyale shi idan matsoraci ne. Ana ƙyale ango na shekara guda domin wataƙila a haifa masa magajinsa kafin ya je irin wannan hidima mai haɗari. A wannan hanyar, Dokar ta yi bayani, wanda ya yi sabon aure “zauna a gida” don “faranta wa amaryarsa rai.”—Maimaitawar Shari’a 20:5, 6, 8; 24:5.

19. Wane tanadi ne Dokar ta ƙunsa domin kāre mata, yara, iyalai, gwauraye, da kuma marayu?

19 Dokar kuma ta kāre mata, yara, da kuma iyalai, ta wajen yi musu tanadi. Ta umurci iyaye su mai da hankali ga yaransu kuma su koyar da su a abubuwa na ruhaniya. (Maimaitawar Shari’a 6:6, 7) Ta haramta dukan ire-iren jima’i tsakanin dangi da dangi, kuma sakamakon haka mutuwa ne. (Littafin Firistoci, sura 18) Hakanan kuma ta haramta zina, da sau da yawa take raba iyalai kuma take halaka kwanciyar ransu da kuma darajarsu. Dokar ta yi tanadi wa gwauraye da kuma marayu, kuma cikin ƙaƙƙarfan harshe ta haramta wulakanta su.—Fitowa 20:14; 22:22-24.

20, 21. (a) Me ya sa Dokar Musa ta ƙyale aurar mata fiye da ɗaya tsakanin Isra’ilawa? (b) Game da batun kashe aure, me ya sa Dokar ta bambanta daga ƙa’idar da Yesu daga baya ya maido?

20 Amma a nan, wasu za su yi mamaki, ‘Me ya sa Dokar ta ƙyale auren mata fiye da ɗaya?’ (Maimaitawar Shari’a 21:15-17) Muna bukatar yin la’akari da dokokin daidai da zamansu lokacin. Waɗanda suka kwatanta Dokar Musa bisa lokatai na zamani da kuma al’adu babu shakka ba za su fahimce ta ba. (Karin Magana 18:13) Ƙa’idar Jehobah, da ya kafa a Adnin, ta sa aure ya kasance gami ne na dindindin tsakanin namiji da tamace. (Farawa 2:18, 20-24) A lokacin da Jehobah ya bai wa Isra’ila Dokar, ayyuka kamar su aurar mata fiye da ɗaya ya riga ya kahu da daɗewa. Jehobah ya san cewa ‘mutanensa masu taurin kai’ za su ƙi biyayya da har umurnai da suka kasance dole ma, kamar waɗanda ke haramta bauta wa gunki. (Fitowa 32:9) Cikin hikima, bai zaɓi wannan zamanin domin ya sake dukan sha’anonin aurensu ba. Ka tuna cewa, Jehobah bai kafa auren fiye da mace guda ba. Amma, ya yi amfani da Dokar Musa ya kafa ƙa’ida game da aurar mata fiye da ɗaya tsakanin mutanensa kuma don ya hana su ɓata ƙa’idar.

21 Hakazalika, Dokar Musa ta ƙyale mutum ya saki matarsa domin abubuwa da yawa masu tsanani. (Maimaitawar Shari’a 24:1-4) Yesu ya kira ta dama da Allah ya bai wa Yahudawa, domin ‘taurin zuciyarsu.’ Amma dai, irin wannan damar ba ta dindindin ba ce. Ga mabiyansa, Yesu ya maido da ƙa’idar aure ta asali.—Matiyu 19:8.

Dokar ta Ɗaukaka Ƙauna

22. A waɗanne hanyoyi ne Dokar Musa ta ƙarfafa ƙauna, kuma ga wane ne?

22 Za ka iya tunanin tsarin dokoki na zamani da ya ƙarfafa cewa a yi ƙauna? Dokar Musa ta ɗaukaka ƙauna fiye da kome. Hakika, a cikin littafin Maimaitawar Shari’a kawai, kalmar nan “ƙauna” ta bayyana a yanayi dabam-dabam fiye da sau 20. “Za ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” ita ce doka mafi girma ta biyu a Dokar. (Littafin Firistoci 19:18; Matiyu 22:37-40) Mutanen Allah za su yi ƙaunar ba junansu kawai ba amma har da baƙi da suke da zama a tsakaninsu, suna tuna cewa su ma sun taɓa zaman baƙunci. Za su yi ƙaunar gajiyayyu da wahalallu, za su taimake su da abin da suke da shi kuma za su guji ci wa waɗanda suka galabaita zarafi. An umurce su su bi da jaki da kirki da kuma sanin ya-kamata.—Fitowa 23:6; Littafin Firistoci 19:14, 33, 34; Maimaitawar Shari’a 22:4, 10; 24:17, 18.

23. Mene ne marubucin Zabura ta 119 ya motsa ya yi, kuma mene ne za mu ɗaura aniyyar yi?

23 Wace al’umma ce ban da wannan da aka yi wa albarka take da irin wannan tsarin doka? Ba mamaki da mai Zabura ya rubuta: “Ina misalin ƙaunata ga Koyarwarka!” Babu shakka, ƙaunarsa ba motsin zuciya ba ne kawai. Ta motsa shi ga yin aiki, domin ya yi ƙoƙari ya yi biyayya ga dokar kuma ya rayu bisanta. Ya ci gaba da cewa: “Dukan yini ita ce tunanina.” (Zabura 119:11, 97) Hakika, yana ba da lokaci ya yi nazarin dokokin Jehobah a kai a kai. Babu shakka cewa da ya yi haka, ƙaunarsa ga dokokin ta ƙaru. Hakanan, ƙaunarsa ga Mai Ba da Dokar, Jehobah Allah ma ta ƙaru. Yayin da ka ci gaba da nazarin dokar Allah, bari kai ma ka matso kusa da Jehobah, Mai Ba da Doka Mai Girma kuma Allah na shari’a.

a Alal misali, da daɗewa kafin wasu su kai ga fahimin, doka ta bukaci a rufe kashin mutum, a ware majiyyaci, kuma dukan wanda ya taɓa gawa ya wanke jikinsa.—Littafin Firistoci 13:4-8; Littafin Ƙidaya 19:11-13, 17-19; Maimaitawar Shari’a 23:13, 14.

b Kuma haikalin Kan’aniyawa suna da ɗakuna da aka keɓe domin ayyukan jima’i, Dokar Musa ta ce waɗanda ba su da tsarki ba za su shiga cikin haikali ba ma. Saboda haka, tun da jima’i yana kawo rashin tsabta, babu wanda zai yi jima’i cewa daidai ne domin bauta a gidan Jehobah.

c Koyarwa ita ce ainihin dalilin Dokar. Hakika, Encyclopædia Judaica ya lura cewa kalmar Ibrananci na “doka,” toh·rahʹ, tana nufin “koyarwa.”

d Dokar ta ce: “Ba za ku halaka itatuwan garin ta wurin sassare su ba, gama itatuwan daji ba mutum ba ne da za ku kai musu yaƙi.” (Maimaitawar Shari’a 20:19) Philo, manazarci na ƙarni na farko Bayahude, ya yi ƙaulin wannan dokar, ya yi bayani cewa Allah ya ga “rashin adalci ne fushin da ake yi da mutane a kai shi bisa abubuwa da ba su da laifin kome.”

Tambayoyi don Bimbini

  • Littafin Firistoci 19:9, 10; Maimaitawar Shari’a 24:19 Yaya kake ji game da Allah wanda ya kafa waɗannan dokoki?

  • Zabura 19:7-14 Yaya Dauda ya ji game da ‘dokar Jehobah,’ kuma yaya ya kamata dokokin Allah su kasance a gare mu?

  • Mika 6:6-8 Ta yaya wannan wurin ya taimake mu mu ga cewa dokokin Jehobah ba za a iya ɗaukansu cewa da ban ciwo ba?

  • Matiyu 23:23-39 Ta yaya Farisawa suka nuna cewa ba su fahimci dalilin Dokar ba, kuma ta yaya wannan ya kasance misali ne na gargaɗi a gare mu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba