Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • Tsarin Ayyuka na Makon 23 ga Mayu
    Hidimarmu Ta Mulki—2011 | Mayu
    • Tsarin Ayyuka na Makon 23 ga Mayu

      MAKON 23 GA MAYU

      Waƙa ta 39 da Addu’a

      □ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:

      bh babi na 19 sakin layi na 10-19 (minti 25)

      □ Makarantar Hidima ta Allah:

      Karatun Littafi Mai Tsarki: Zabura 19-25 (minti 10)

      Na 1: Zabura 23:1–24:10 (minti 4 ko ƙasa da hakan)

      Na 2: Littafi Mai Tsarki—Littafi Don Dukan Mutane—td 30C (minti 5)

      Na 3: Ta Yaya da Kuma Yaushe Ne Romawa 8:21 Za ta Cika? (minti 5)

      □ Taron Hidima:

      Waƙa ta 78

      Minti 10: Sanarwa. “Yadda Za a Yi Amfani da Fom Ɗin Please Follow Up (S-43).” Tattaunawa.

      Minti 10: Hanyoyi Uku na Yin Gabatarwa Mai Kyau. Jawabin da aka ɗauko daga ƙasidar nan Yadda Za a Soma Kuma Cigaba da Mahawwarai na Littafi Mai-Tsarki, shafi na 2, sakin layi na 1. Bayan ka kammala sakin layin, ka sa a yi gwaji biyu da ya nuna gabatarwa da za a iya yin amfani da ita don ba da mujallu na watan Yuni.

      Minti 15: Ka Taɓa Gwadawa Kuwa? Tattaunawa. Ta hanyar jawabi, ka ɗan ba da gajeriyar bita daga talifofi na kwanan nan da ke cikin Hidimarmu Ta Mulki: “Sabon Talifi don Soma Nazarorin Littafi Mai Tsarki” (km 12/10) da “Taimako ga Iyalai” (km 1/11). Ka gayyaci masu sauraro su ba da kalami a kan yadda suka yi amfani da shawarwarin da suke cikin talifofin nan da kuma yadda suka amfana.

      Waƙa ta 56 da Addu’a

  • Tsarin Ayyuka na Makon 30 ga Mayu
    Hidimarmu Ta Mulki—2011 | Mayu
    • Tsarin Ayyuka na Makon 30 ga Mayu

      MAKON 30 GA MAYU

      Waƙa ta 33 da Addu’a

      □ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:

      bh babi na 19 sakin layi na 20-23 da akwati (minti 25)

      □ Makarantar Hidima ta Allah:

      Karatun Littafi Mai Tsarki: Zabura 26-33 (minti 10)

      Na 1: Zabura 31:9-24 (minti 4 ko ƙasa da hakan)

      Na 2: Misalan da ke Cikin Littafi Mai Tsarki Na Tawali’u Na Gaske (minti 5)

      Na 3: Ƙarin Jini Yana Ɓata Tsarkin Jini—td 24A (minti 5)

      □ Taron Hidima:

      Waƙa ta 38

      Minti 10: Sanarwa. Ka yi amfani da shawarar da ke shafi na 4 don gwada yadda za a iya soma nazari a Asabar ta farko a watan Yuni. Ka ƙarfafa kowa ya saka hannu.

      Minti 15: Yadda Za a Yi Bincike. Tattaunawa da aka ɗauko daga littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafuffuka na 33-38. Ka haɗa da yi wa kai magana da mai shela zai yi yana nuna yadda yake amfani da littattafan bincike don neman amsa ga tambaya da wani ya yi a hidima.

      Minti 10: Ku Yi Shirin Ba da Mujallu a Watan Yuni. Tattaunawa. Ka yi amfani da minti ɗaya ko biyu don yin bitar abin da ke cikin mujallun. Sai ka zaɓi talifofi biyu ko uku, kuma ka gayyaci masu sauraro su faɗi tambayoyi da nassosi da za su yi amfani da su don gabatar da mujallun. Ka sa a gwada yadda za a gabatar da kowacce mujalla.

      Waƙa ta 113 da Addu’a

  • Yadda Za a Yi Amfani da Fom Ɗin Please Follow Up (S-43)
    Hidimarmu Ta Mulki—2011 | Mayu
    • Yadda Za a Yi Amfani da Fom Ɗin Please Follow Up (S-43)

      Ku cika wannan fam ɗin sa’ad da kuka tarar da wani da ke son saƙonmu wanda ba shi da zama a yankinku ko kuma yana wani harshe. Ko da yake a dā muna yin amfani da shi sa’ad da muka haɗu da waɗanda suke wani harshen ko suna son saƙonmu ko a’a, amma yanzu za mu riƙa yin amfani da shi kawai sa’ad da wani yake son saƙonmu. Sai dai idan mutumin kurma ne. Idan mun haɗu da kurma, ko yana son saƙonmu ko a’a, a cika fom ɗin S-43.

      Mene ne za mu yi da fom ɗin bayan an cika shi? Mu ba wa sakataren ikilisiyar. Idan ya san ikilisiyar da ya kamata ya aika wa fom ɗin, kamar ikilisiyar da ke kusa inda ake yaren, zai iya aika wa dattawan ikilisiyar don su shirya wani ya ziyarci wanda ke son saƙonmu. Idan bai san ikilisiyar ba, ya aika fom ɗin zuwa ofishin reshe.

      Idan mutumin da ke son saƙonmu yana wani harshe kuma yana zama a yankinku, za ku iya ci gaba da koma ziyara wurinsa har sai an aiko da wani mai shela daga ikilisiyar inda ake harshen. A wasu lokatai, zai iya kasance cewa babu ikilisiya da ke yaren da ke kusa da wurin. Idan hakan ne, ka ci gaba da ziyarar mutumin don ka ƙarfafa shi, ka ba shi kowanne littafi da ake da shi a yarensa, kuma ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi idan zai yiwu.—Ka duba Hidimarmu Ta Mulki ta Nuwamba 2009, shafi na 4.

Littattafan Hausa (1987-2026)
Fita
Shiga Ciki
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba