Sabon Talifi don Soma Nazarorin Littafi Mai Tsarki
1. Wane sabon talifi ne zai fito a Hasumiyar Tsaro ta wa’azi, kuma yaya aka shirya shi?
1 Sabon talifi zai bayyana a fitowar Hasumiyar Tsaro ta wa’azi da za ta taimaka mana mu soma nazarorin Littafi Mai Tsarki. Wannan zai soma da fitowa ta Afrilu-Yuni. Jigonsa shi ne “Ka Koya Daga Kalmar Allah.” Ko da yake wasu a yankin za su ji daɗin karanta kowane talifi, an shirya talifofin don a yi amfani da su wajen tattaunawa da mai gida.
2. Waɗanne abubuwa ne suke cikin waɗannan talifofin?
2 Abin da ke Ciki: An rubuta jigon da kawunan maganan a matsayin tambayoyin da za a yi wa maigidan a lokacin tattaunawar. An nuna nassosi masu muhimmanci, ba a yi ƙaulinsu ba, domin maigidan ya ji daɗin koyo kai tsaye daga cikin Kalmar Allah. Sakin layin ba su da yawa domin a iya tattauna su kai tsaye a bakin kofa. Kowane talifi ya yi nuni ga littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? don ya taimaka maka ka soma nazarin wannan littafin da maigidan sa’ad da ya dace.
3. Sa’ad da ake wa’azi gida gida, yaya za mu iya yin amfani da waɗannan talifofin don soma nazarin Littafi Mai Tsarki a bakin ƙofa?
3 Yadda Za a Yi Amfani da Talifofin: Sa’ad da kake ba da mujallu kana iya yin tambaya a kan batun da ke cikin talifin da maigidan zai so. Alal misali, fitowa ta Afrilu-Yuni ta tattauna muhimmancin Littafi Mai Tsarki. Kana iya tambaya: “Kana ɗaukan Littafi Mai Tsarki a matsayin Kalmar Allah ko kuwa littafi mai kyau ne kawai? [Ka bari ya ba da amsa.] Ina da wani abu a kan wannan batun da za ka so.” Ka nuna tambaya na farko, sai ka karanta sakin layi na farko, kuma ka karanta nassin da aka nuna a ciki. Ka sake karanta tambayar, kuma ka bari maigidan ya ba da amsa. Ka yi tattaunawar yawan yadda ya dace, ka yi amfani da tambayoyi da aka saka wa lamba a matsayin batun tattaunawa. Kafin ka tafi, ka jawo hankalin maigidan ga tambaya na gaba kuma ka yi shirin komawa don tattauna shi. Ka koma don ka ƙara tattauna talifin kowane mako da mai gidan har sai ka kawo masa fitowa na gaba. Wata hanya kuma ita ce ka yi amfani da yin magana kai tsaye da maigidan kuma ka ce za ka so ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Sai ka yi amfani da talifin mujallar don gwada nazarin.
4. Ta yaya za mu iya yin amfani da waɗannan talifofin sa’ad da muka koma ziyara?
4 Za ka kuma iya yin amfani da wannan sabon talifin da kyau ga wanda kake kai masa mujallu a kai a kai da kuma sa’ad da ka koma ziyara. Kana iya cewa: “Da akwai sabon talifi a cikin Hasumiyar Tsaro. Bari in nuna maka yadda ake amfani da shi.” Muna addu’a cewa wannan sabon talifin zai taimaki mutane da yawa su “kawo ga sanin gaskiya.”—1 Tim. 2:4.