Yadda Za a Yi Amfani da Fom Ɗin Please Follow Up (S-43)
Ku cika wannan fam ɗin sa’ad da kuka tarar da wani da ke son saƙonmu wanda ba shi da zama a yankinku ko kuma yana wani harshe. Ko da yake a dā muna yin amfani da shi sa’ad da muka haɗu da waɗanda suke wani harshen ko suna son saƙonmu ko a’a, amma yanzu za mu riƙa yin amfani da shi kawai sa’ad da wani yake son saƙonmu. Sai dai idan mutumin kurma ne. Idan mun haɗu da kurma, ko yana son saƙonmu ko a’a, a cika fom ɗin S-43.
Mene ne za mu yi da fom ɗin bayan an cika shi? Mu ba wa sakataren ikilisiyar. Idan ya san ikilisiyar da ya kamata ya aika wa fom ɗin, kamar ikilisiyar da ke kusa inda ake yaren, zai iya aika wa dattawan ikilisiyar don su shirya wani ya ziyarci wanda ke son saƙonmu. Idan bai san ikilisiyar ba, ya aika fom ɗin zuwa ofishin reshe.
Idan mutumin da ke son saƙonmu yana wani harshe kuma yana zama a yankinku, za ku iya ci gaba da koma ziyara wurinsa har sai an aiko da wani mai shela daga ikilisiyar inda ake harshen. A wasu lokatai, zai iya kasance cewa babu ikilisiya da ke yaren da ke kusa da wurin. Idan hakan ne, ka ci gaba da ziyarar mutumin don ka ƙarfafa shi, ka ba shi kowanne littafi da ake da shi a yarensa, kuma ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi idan zai yiwu.—Ka duba Hidimarmu Ta Mulki ta Nuwamba 2009, shafi na 4.