Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 1/1 p. 28
  • “Ya Samu Gareka”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ya Samu Gareka”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Daraja Yesu, Wanda Ya Fi Dauda Da Sulemanu Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Sulemanu Sarki Ne Mai Hikima
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Shi Misali Mai Kyau Ne A Gare Ka Ko Kuma Kashedi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • ‘Ka Koya Mini Na Aikata Nufinka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 1/1 p. 28

Ka Kusaci Allah

“Ya Samu Gareka”

1 LABARBARU 28:9

KA SAN Allah? Amsa wannan tambayar ba ta da sauƙi kamar yadda muke zato. Sanin Allah da gaske ya ƙunshi fahimtar nufinsa da hanyoyinsa sosai. Hakan zai sa mu ƙulla dangantaka da shi wadda za ta shafi rayuwarmu gabaki ɗaya. Irin wannan dangantakar za ta yiwu kuwa? Idan za ta yiwu, ta yaya za mu iya ƙulla ta? Za a iya samun amsar a cikin shawarar da Sarki Dauda ya ba ɗansa Sulemanu, wadda take Labarbaru 28:9.

Ka yi tunanin yanayin. Dauda ya yi wajen shekara 40 yana sarauta bisa Isra’ila, kuma al’ummar ta samu arziki a ƙarƙashin sarautarsa. Ba da daɗewa ba Sulemanu zai gaje shi, kuma shi matashi ne sosai. (1 Labarbaru 29:1) Wace shawara ta ƙarshe ce Dauda ya ba ɗansa?

Sa’ad da yake magana bisa ga abubuwan da ya shaida daga bauta wa Allah da yake yi, Dauda ya soma: “Solomon ɗana, ka san Allah na ubanka.” Abin da Dauda ke nufi ya wuce kasancewa da sani na kai kawai. Sulemanu yana bauta wa Allahn Dauda, Jehobah. A wannan lokacin, an riga an kammala wajen kashi uku na Nassosin Helenanci, kuma babu shakka Sulemanu ya san abubuwan da waɗannan rubutu masu tsarki suka ce game da Allah. Wani masani ya ce kalmar Helenanci da aka fassara ‘sani’ yana nufin “ainihin sani na kud da kud.” Hakika, Dauda yana son ɗansa ya samu abin da Dauda da kansa yake ɗauka tamani—dangantaka na kud da kud da Allah.

Ya kamata irin wannan dangantakar ta shafi ra’ayin Sulemanu sosai da kuma hanyar rayuwarsa. Dauda ya ƙarfafa ɗansa: “Ka bauta masa da sahihiyar zuciya da yardan rai kuma.” Idan ka lura za ka ga cewa umurnin nan na bauta wa Allah ya zo bayan ƙarfafawa ta saninsa. Babu shakka, sanin Allah yana kai ga bauta masa. Amma bai kamata a bauta masa da rabin zuciya ko munafunci ba. (Zabura 12:2; 119:113) Dauda ya roƙi ɗansa ya bauta wa Allah da cikakkiyar zuciya da kuma son rai.

Me ya sa Dauda ya aririci ɗansa ya bauta wa Allah da manufa da kuma tunani mai kyau? Dauda ya bayyana: “Gama Ubangiji yana binciken dukan zukata, ya kuma gāne dukan sifofin tunani.” Bai kamata Sulemanu ya bauta wa Allah don kawai yana son ya faranta ran mahaifinsa, Dauda ba. Allah yana neman waɗanda suke son su bauta masa da sahihiyar zuciya.

Sulemanu zai bi misalin mahaifinsa kuwa kuma ya kusaci Allah? Hakan yana hannun Sulemanu. Dauda ya gaya wa ɗansa: “Idan ka biɗe shi, ya samu gareka; idan ka yashe shi, shi kuma za ya yashe ka har abada.” Don ya zama mai bauta da ya kusaci Allah, Sulemanu yana bukatar ya ƙoƙarta sosai don ya san Jehobah.a

Shawara irin ta uba da Dauda ya ba da ta tabbatar da mu cewa Jehobah yana son mu kusace shi. Amma don mu kusace shi, muna bukatar mu “biɗe shi,” mu kutsa cikin Nassosi don mu ƙara saninsa sosai. Ya kamata saninsa ya motsa mu mu bauta masa da dukan zuciyarmu kuma da son rai. Jehobah yana so, kuma ya cancanci hakan daga masu bauta masa.—Matta 22:37.

[Hasiya]

a Abin baƙin ciki, ko da yake Sulemanu ya soma bauta wa Allah da cikakkiyar zuciya, bai ci gaba da kasancewa da aminci ba.—1 Sarakuna 11:4.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba