DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | NEHEMIYA 9-11
Amintattun Bayin Jehobah Suna Tallafa wa Tsarin Allah
Bayin Allah suna goyon bayan bauta ta gaskiya a hanyoyi da dama
10:28-30, 32-39; 11:1, 2
Al’ummar Isra’ila ta yi shiri sosai don ta kiyaye Idin Bukkoki a hanyar da ta dace
A kowace rana, mutanen suna taruwa don su saurari karatun Dokar Allah da ke sa su farin ciki sosai
Mutanen sun faɗi zunubansu, sun yi addu’a, sun kuma roƙi Allah ya albarkace su
Mutanen sun yarda su ci gaba da tallafa wa tsarin Allah
Tallafa wa tsarin Allah ya ƙunshi:
Auren mutanen da suke bauta wa Jehobah kaɗai
Ba da gudummawar kuɗi
Kiyaye ranar Asabar
Tanadar da itace don bagadi
Ba da nunan fari da kuma ɗan fari na dabba ga Jehobah