DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | NEHEMIYA 12-13
Darussan da Za Mu Koya Daga Littafin Nehemiya
Nehemiya ya kāre bauta ta gaskiya da ƙwazo
13:4-9, 15-21, 23-27
Babban Firist Eliashib ya ƙyale Tobiya wanda ba ya bauta wa Allah ya rinjaye shi
Eliashib ya ba Tobiya wuri a ɗakin cin abinci da ke haikalin
Nehemiya ya zubar da kayayyakin Tobiya, ya tsabtace ɗakin kuma aka soma amfani da shi yadda ya kamata
Nehemiya ya ci gaba da kawar da abubuwa masu ƙazamta daga Urushalima