WAƘA TA 85
Mu Riƙa Marabtar Juna
Hoto
	1. Muna marabtar dukanku a nan
Domin mun zo nazari tare.
Allah na so mu sami rai kyauta.
Mun zo nan domin mu nuna godiyarmu.
2. Mun gode Allah don dattawanmu
Da suke kula da mu da kyau.
Muna ƙaunar ’yan’uwan nan sosai,
Muna kuma marabtar kowa taron nan.
3. Allah Jehobah mai ƙauna sosai,
Kana son kowa ya bauta ma.
Mun kusace ka ta wurin Ɗanka.
Don haka mu riƙa marabtar junanmu.
(Ka kuma duba Yoh. 6:44; Filib. 2:29; R. Yoh. 22:17.)