Maganar Jehovah Rayayyiya Ce
Taƙaici Daga Littafin Ƙidaya
BAYAN da suka fita daga Masar an shirya Isra’ila ta zama al’umma. Bayan haka, ba da daɗewa ba da sun shiga Ƙasar Alkawari amma hakan bai yiwu ba. Maimako, sun yi ta gantali na kusan shekaru arba’in cikin “babban jejin nan mai bantsoro.” (Maimaitawar Shari’a 8:15) Me ya sa? Labarin tarihin da ke cikin Littafin Ƙidaya na Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da ya faru. Ya kamata mu fahimci cewa muna bukatar mu yi wa Jehovah Allah biyayya kuma mu daraja wakilansa.
Musa ne ya rubuta littafin a Filayen Mowab, Littafin Ƙidaya ya ɗauki shekaru 38 da watanni 9—wato, daga 1512 K.Z. zuwa 1473 K.Z. (Littafin Ƙidaya 1:1; Maimaitawar Shari’a 1:3) An samo sunansa daga ƙirge biyu da aka yi wa Isra’ilawa ne na shekaru 38. (Surori 1-4, 26) An rarraba labaran kashi uku. Kashi na ɗaya ya yi zancen abubuwan da suka faru a Jejin Sinai. Na biyu kuma ya yi zancen abubuwan da suka faru a lokacin gantali na Isra’ilawa a jeji. Kashi na ƙarshe kuma game da abubuwan da suka faru a Filayen Mowab ne. Yana da kyau ka tambayi kanka sa’ad da kake karanta wannan labarin: ‘Menene waɗannan abubuwan suke koya mini? Akwai ƙa’idodin da suke cikin wannan littafin ne da zan yi amfani da su a yau?’
A JEJIN SINAI
(Littafin Ƙidaya 1:1–10:10)
An yi ƙirge na farko sa’ad da Isra’ilawa suke ƙasan Jejin Sinai. Maza da suke shekaru 20 zuwa gaba ban da Lawiyawa sun kai 603,550. An yi wannan ƙirgen saboda a sami sojoji ne. Dukan mutanen, mata, yara, da kuma Lawiyawa ƙila sun fi miliyan uku.
An ba wa Isra’ilawa umurni game da yadda za su yi tafiya bayan ƙirgen, an ba da cikakken bayani game da aikin Lawiyawa da kuma hidima na mazauni, umurni game da wariya domin cuta, dokoki game da kishi, da ɗaura alkawari da Keɓaɓɓu suka yi. Sura 7 tana ɗauke da umurni game da hadayu da ya kamata shugabannin ƙabilai su yi a bikin buɗe bagadi, sura 9 kuma ta yi zance game da kiyaye Faska. An kuma ba wa al’ummar umurni game da yadda za su kafa kuma su warware zango.
An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:
2:1, 2—Mecece “tutar” da ƙabilai za su bi su kafa zango a jeji? Littafi Mai Tsarki bai kwatanta mana yadda wannan tutar take ba. Amma, ba abin da ake ɗauka da tsarki ko kuma wata alama ta addini ba ne. Ana amfani da tutar domin wani abu ne—domin mutum ya san masaukinsa cikin zangon.
5:27—Menene ake nufi da cewa matar da ta yi zina “cinyarta ta shanye”? An yi amfani da kalmar nan ‘cinya’ a nan a matsayin iya haihuwa. (Farawa 46:26) Cewa ‘cinyar za ta shanye’ yana nufin ba za ta iya haihuwa kuma ba.
Darussa da Za Mu Koya:
6:1-7. Bai kamata Keɓaɓɓu su sha ruwan inabi ba da kuma abubuwan da za su iya bugar da su domin keɓe kansu da suka yi. An bukace su su ƙyale gashin kansu ya yi dogo—alamar biyayyarsu ce ga Jehovah yadda mata da suke biyayya ga mazansu ko kuma ubanninsu suke yi. An bukaci Keɓaɓɓu su kasance da tsarki ta wurin guje wa taɓa gawa, har ma idan na dangi ne. Waɗanda suke hidima ta cikakken lokaci a yau suna nuna ba da kansu sa’ad da ya shafi yin biyayya ga Jehovah da kuma tsarinsa. Wasu hakki suna bukatar a yi tafiya zuwa ƙasa mai nisa, wannan ba zai zama da sauƙi ko ya yiwu mutum ya dawo gida ma don jana’izar wani cikin iyalinsa.
8:25, 26. Ana kula da tsofaffi domin su cika hidimar Lawiyawa yadda ya dace, ana gaya wa tsofaffi maza su yi murabus daga aikin soja. Amma za su iya ba da kansu su taimaka wa Lawiyawan. Ko da yake babu yin murabus a batun shelar Mulki a yau, ƙa’idar da ke cikin dokar nan tana koya mana wani muhimmin abu. Idan saboda tsufa Kirista bai iya cika wasu hakki ba, zai iya yin hidimar da take gwargwadon iyawarsa.
TAFIYE-TAFIYE A JEJI
(Littafin Ƙidaya 10:11–21:35)
Sa’ad da girgije da ke kan mazauni ya tashi, sai Isra’ilawa suka soma tafiya da ta kawo su filayen Mowab bayan shekaru 38 da wata guda ko biyu. Zai yi maka sauƙi ka bi tafiyarsu a taswira a shafi 9 na mujallar nan “See the Good Land,” da Shaidun Jehovah suka buga (Turanci).
Sa’ad da suke kan hanyar zuwa Kadesh, a Jejin Faran, sun yi gunaguni sau uku. Jehovah ya daina na farko ta wurin aika da wuta ta halaka mutanen. Sai kuma Isra’ilawa suka yi kukan nama Jehovah kuma ya ba su makware. Gunagunin Maryamu da Haruna game da Musa ya sa Maryamu ta kuturta na ɗan lokaci.
Sa’ad da suke zango a Kadesh, sai Musa ya aiki ’yan leƙen asirin ƙasa guda 12 su je su leƙo Ƙasar Alkawari. Bayan kwanaki 40 suka dawo. Mutanen suka nemi su jajjefi Musa, Haruna, da kuma amintattu ’yan leƙen asirin ƙasa Joshuwa da Kalibu, domin sun yarda da mugun labari daga ’yan leƙe goman. Sai Jehovah ya ƙudura zai buga mutanen da cuta, amma Musa ya yi musu sulhu, sai Allah ya ce za su zama masu gantali cikin jeji na shekara 40—har sai dukan waɗanda aka ƙidaya sun mutu.
Jehovah ya daɗa ba su umurnai. Kora da wasu suka yi tawaye wa Musa da Haruna, amma an halaka ’yan tawayen da wuta ko kuma ƙasa ta buɗe baki ta haɗiye su. Washegari taron suka yi wa Musa da Haruna gunaguni. Saboda haka mutane 14,700 suka mutu a hannun Jehovah. Don ya nuna cewa shi ya zaɓi babban firist, Allah ya sa sandar Haruna ya yi toho. Sai kuma Jehovah ya ƙara ba da dokoki game da hakkin Lawiyawa da kuma tsarkakawar mutanen. Ana amfani da tokar jar saniya a hoton tsarkakewa da hadayar Yesu za ta yi.—Ibraniyawa 9:13, 14.
Isra’ilawa suka dawo Kadesh inda Maryamu ta mutu. Taron suka yi gunaguni game da Musa da Haruna. Menene dalilinsu? Rashin ruwa ne. Musa da Haruna ba su tsarkake sunan Jehovah ba sa’ad da suke tanadin ruwa ta mu’ujiza, saboda haka aka hana su shigar Ƙasar Alkawari. Isra’ilawa suka kaura daga Kadesh kuma Haruna ya mutu a Dutsen Hor. Da Isra’ilawa suka gaji da tafiya sa’ad da suke gewaye Edom sai suka yi gunaguni game da Allah da Musa. Sai Jehovah ya sa macizai masu dafi su yi musu horo. Har ila kuma Musa ya yi musu sulhu, sai Allah ya ce masa ya yi maciji na ƙarfe ya kafa shi a kan ice saboda dukan waɗanda maciji ya sara su kalli na ƙarfen kuma su warke. Macijin yana hoton Yesu Kristi ne da za a kafa shi don madawwamin amfaninmu. (Yahaya 3:14, 15) Isra’ilawa suka ci Sarakunan Sihon da Og suka kuma mallaki ƙasashensu.
An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:
12:1—Me ya sa Maryamu da Haruna suka zargi Musa? Ainihin dalilin zarginsu domin Maryamu tana son girma ne ainu. Lokacin da Ziffora, matar Musa ta zo wurinsa a jeji, ƙila Maryamu tana jin cewa ba za ta ci gaba da samun gatar zama shugaban mata kuma ba a zangon.—Fitowa 18:1-5.
12:9-11—Me ya sa Maryamu kaɗai ce ta kuturce? Mai yiwuwa ne cewa ita ta fara gunagunin kuma ta zuga Haruna ya sa baƙi. Haruna ya nuna halin tuba ta wurin yin ikirarin laifinsa.
21:14, 15—Wane littafi ne aka ambata a nan? Nassosi sun yi nuni ga littattafai da yawa da marubutan Littafi Mai Tsarki suka yi amfani da su a rubutunsu. (Joshuwa 10:12, 13; 1 Sarakuna 11:41; 14:19, 29) “Littafin Yaƙe-yaƙe na Ubangiji” ne waɗannan littattafai. Yana ɗauke da labarin tarihin yaƙe-yaƙe na mutanen Jehovah.
Darussa da Za Mu Koya:
11:27-29. Musa ya bar misali mai kyau game da yadda ya kamata mu yi sa’ad da wasu suka sami gata a hidimar Jehovah. Maimakon jin kishi domin ɗaukaka kansa, Musa ya yi farin ciki sa’ad da Eldad da Medad suka fara annabci.
12:2, 9, 10; 16:1-3, 12-14, 31-35, 41, 46-50. Jehovah yana bukatar masu bauta masa su yi biyayya da ikon da ya bayar.
14:24. Abin da zai taimaka a tsayayya wa matsi na yin laifi shi ne kasance da wani ‘ruhu dabam’ ko wani hali. Dole ya zama wanda ba kamar na duniya ba.
15:37-41. Tuntayen riguna na Isra’ilawa domin ya tunasar da su ne cewa an keɓe su domin bauta wa Allah kuma domin su yi biyayya da dokokinsa. Bai kamata ba ne mu kasance da mizanan Allah kuma mu bambanta da duniya?
A FILAYEN MOWAB
(Littafin Ƙidaya 22:1–36:13)
Lokacin da Isra’ilawa suka yi zango a filayen Mowab, tsoronsu ya kama ’yan Mowab. Saboda haka, Sarki Balak na Mowab ya kira Bal’amu ya la’anci Isra’ilawa. Amma Jehovah ya tilasta wa Bal’amu ya albarkace su. Sai aka yi amfani da matan Mowab da na Midiya su jarabci mazan Isra’ilawa da lalata da kuma bautar gumaka. Domin haka, Jehovah ya halaka masu laifi 24,000. Bala’in ya daina sa’ad da Finehas ya nuna ya ƙi reni da ake wa Jehovah.
Ƙidaya na biyu da aka yi ya nuna cewa Joshuwa da Kalibu ne kaɗai suke da rai a duk maza da aka ƙirga a farko. An umurci Joshuwa ya zama magajin Musa. An ba Isra’ilawa umurni da koyarwa game da hadayu dabam dabam game da yin wa’adi. Mutanen Isra’ila kuma suka yi ramako a kan Madayanawa. Ƙabilar Ra’ubainu, Gad, da kuma rabin ƙabilar Manassa sun zauna a gabashin Kogin Urdun. Aka ba wa Isra’ilawa umurnan yadda za su ƙetare Urdun su mallaki ƙasar. An kwatanta daki-dakin iyakar ƙasashen. Ana ba da gadōn ta wurin kuri’a. Aka ba wa Lawiyawa birane 48, an mai da 6 cikinsu su zama biranen mafaka.
An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi:
22:20-22—Me ya sa Jehovah ya yi fushi da Bal’amu? Jehovah ya gaya wa annabi Bal’amu cewa kada ya la’anci Isra’ilawa. (Littafin Ƙidaya 22:12) Duk da haka, annabin ya je wajen mutanen Balak da niyyar ya la’anci Isra’ila. Bal’amu yana son ya faranta wa sarkin Mowab ne kuma ya sami lada daga wurinsa. (2 Bitrus 2:15, 16; Yahuza 11) Lokacin da aka tilasta wa Bal’amu ya albarkaci Isra’ila maimakon ya la’anta su, ya biɗi samun tagomashin sarkin ta wurin ba shi shawarar cewa mata masu bauta wa Ba’al su je su jarabi mazan Isra’ilawa. (Littafin Ƙidaya 31:15, 16) Dalilin fushin Allah a kan Bal’amu domin muguwar haɗama ta annabin ne.
30:6-8—Kirista zai iya kawar da wa’adin matarsa? A zancen wa’adi, Jehovah yana bi da masu bauta masa ɗai ɗai ne. Alal misali, keɓe kai ga Jehovah, wa’adi ne na mutumin. (Galatiyawa 6:5) Miji ba shi da izinin ya kawar da wa’adin. Amma kuma, kada mata ta yi wa’adi da ya saɓa da Kalmar Allah ko kuma wajibinta wajen mijinta.
Darussa da Za Mu Koya:
25:11. Misali mai kyau ne ƙwarai Finehas ya bar mana na himma a bauta wa Jehovah! Bai kamata sha’awarmu cewa ikilisiya ta zama da tsabta ta motsa mu mu yi ƙarar kowane mugun lalata da muka sani ga dattawa Kirista ba?
35:9-29. Cewa mai kisankai zai bar gidansa ya gudu zuwa birnin mafaka na wani lokaci ya koya mana cewa rai yana da tsarki kuma dole mu daraja shi.
35:33. Jinin marasa laifi da ke ƙazantar da ƙasa, jinin waɗanda suka zubar da shi ne za su yi kafararsa. Lalle ya dace da Jehovah zai halaka miyagu kafin a sabonta duniya zuwa aljana!—Karin Magana 2:21, 22; Daniyel 2:44.
Kalmar Allah Tana da Ƙarfin Aiki
Dole ne mu daraja Jehovah da kuma waɗanda suke da hakki a tsakanin mutanensa. Littafin Ƙidaya ya bayyana wannan gaskiya sarai. Lalle muhimmin darasi ne don mu kasance da salama da haɗin kai cikin ikilisiya a yau!
Aukuwa da aka ba da labarinta cikin Littafin Ƙidaya sun nuna yadda waɗanda suka ƙyale ruhaniyarsu suke fāɗi cikin laifi, kamar gunaguni, lalata, da kuma bautar gumaka. Wasu misalai da darussa daga wannan littafi na Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka mana mu lura da bukatun yankinmu a Taron Hidima ta ikilisiyar Shaidun Jehovah. Hakika, “maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki” a rayuwarmu.—Ibraniyawa 4:12.