KA KUSACI ALLAH
“Mai-Sākawa Ne ga Dukan Waɗanda Ke Biɗarsa”
Jehobah yana ɗaukan ƙoƙarin da bayinsa suke yi don su faranta masa rai da muhimmanci kuwa? Wasu mutane suna iya cewa a’a, domin suna ganin Allah bai damu da abin da muke yi ba. Amma, wannan ra’ayin bai dace da Allah ba. Kalmarsa Littafi Mai Tsarki ya bayyana gaskiyar lamarin kuma ya tabbatar mana cewa Jehobah yana ɗaukan ƙoƙarin da bayinsa masu bangaskiya suke yi da tamani. Ka yi la’akari da kalamin manzo Bulus a littafin Ibraniyawa 11:6.
Mene ne muke bukatar yi don mu faranta wa Jehobah rai? Bulus ya ce: “Ba ya kuwa yiwuwa a gamshe shi ba sai tare da bangaskiya.” Ka lura cewa Bulus bai ce da kyar mutum ya faranta wa Allah rai idan ba shi da bangaskiya ba, amma ya ce ba ya yiwuwa a yi hakan ban da bangaskiya. Hakan yana nufin cewa wajibi ne mu kasance da bangaskiya idan muna so mu faranta wa Allah rai.
Mene ne ya kamata mu yi don mu kasance da bangaskiyar da za ta faranta wa Jehobah rai? Akwai abubuwa biyu da ya kamata mu yi. Na ɗaya, wajibi ne mu “ba da gaskiya cewa yana da rai.” Shin zai yiwu mu faranta wa Allah rai idan ba mu amince cewa ya wanzu ba? Amma kasancewa da bangaskiya ta ƙwarai ta fi amincewa kawai cewa Allah ya wanzu, domin ko aljanu ma sun gaskata cewa Jehobah ya wanzu. (Yaƙub 2:19) Idan muna da bangaskiya cewa Allah ya wanzu, hakan zai sa mu yi rayuwa a hanyar da za ta faranta masa rai.—Yaƙub 2:20, 26.
Na biyu, wajibi ne mu “ba da gaskiya” cewa Allah ne “mai-sākawa.” Mutumin da yake da bangaskiya sosai yana da tabbaci cewa duk ƙoƙarin da yake yi don ya yi rayuwa a hanyar da za ta faranta wa Allah rai ba zai taɓa zama aikin banza ba. (1 Korintiyawa 15:58) Zai yiwu mu faranta wa Jehobah rai idan muna shakka ko zai sāka mana? (Yaƙub 1:17; 1 Bitrus 5:7) Mutumin da bai gaskata ba cewa Allah karimi ne wanda ke kula da mu kuma yana ɗaukan ƙoƙarinmu da muhimmanci, bai san Allah na gaskiya ba.
Waɗanne irin mutane ne Jehobah yake sāka musu? Bulus ya ce “waɗanda ke biɗarsa” da himma. Wani littafin bincike da mafassaran Littafi Mai Tsarki suke amfani da shi ya ce asalin kalmar nan a Helenanci ba ta nufin “neman” Allah kawai ba, amma tana nufin yin ƙoƙari wajen bauta masa. Wani littafi dabam ya bayyana cewa yadda ake yin amfani da wannan kalmar a Helenanci tana kwatanta yin abu da aniya da kuma ƙoƙari sosai. Hakika, Jehobah yana sāka ma waɗanda suke bauta masa da ƙwazo da kuma dukan zuciyarsu domin suna da bangaskiya kuma suna ƙaunarsa.—Matta 22:37.
Zai yiwu mu faranta wa Jehobah rai idan muna shakka ko zai sāka mana?
A wace hanya ce Jehobah yake sāka wa bayinsa masu bangaskiya? Ya yi alkawari cewa a nan gaba, za su rayu har abada a cikin Aljanna a duniya. Wannan alkawarin ya bayyana yawan ƙauna da kuma karimcinsa. (Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Ko a yanzu ma, waɗanda suke biɗar Jehobah da himma suna samun albarkarsa sosai. Suna more rayuwa mai ma’ana domin suna bin koyarwar da ke cikin Kalmar Allah da kuma ja-gorar ruhunsa mai tsarki.—Zabura 144:15; Matta 5:3.
Tabbas, Jehobah Allah ne da ke ɗaukan hidimar da bayinsa masu aminci suke yi masa da muhimmanci sosai. Kana marmarin kusantar Allah kuwa yanzu da ka koyi waɗannan abubuwa game da shi? Idan haka ne, don Allah ka ƙara koyan abin da zai taimaka maka ka kasance da bangaskiya don Jehobah ya sāka maka.