Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 8/1 p. 27-p. 31 par. 3
  • Darussa Daga Littafin Sarakuna na Biyu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Sarakuna na Biyu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ELISHA YA GĀJI ILIYA
  • (2 Sarakuna 1:1–8:29)
  • AN KWASHI ISRA’ILA DA YAHUZA BAUTA
  • (2 Sarakuna 9:1–25:30)
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Elisha Ya Ga Karusai na Wuta​—⁠Kai Kuma Fa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ta So Ta Yi Taimako
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ya Jimre Har Zuwa Karshe
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 8/1 p. 27-p. 31 par. 3

Maganar Jehobah Rayayyiya Ce

Darussa Daga Littafin Sarakuna na Biyu

LITTAFIN Sarakuna na Biyu na Littafi Mai Tsarki ya fara daga inda littafin Sarakuna na Ɗaya ya ƙare. Labari ne na sarakuna 29, 12 daga masarautar Isra’ila ta arewa da kuma 17 daga masarautar Yahuza ta kudu. Littafin Sarakuna na Biyu kuma ya ba da labarin ayyukan annabi Iliya, Elisha, da kuma Ishaya. Ko da yake ba a shirya su kamar yadda suka faru ba, tarihin ya kai har lokacin halakar Samariya da Urushalima. Gaba ɗaya, littafin Sarakuna na Biyu ya ba da labarin abin da ya faru cikin shekaru 340, daga shekara ta 920 K.Z. zuwa shekara ta 580 K.Z. sa’ad da annabi Irmiya ya kammala rubuta wannan littafin.

Menene muhimmancin littafin Sarakuna na Biyu a gare mu? Menene ya koya mana game da Jehobah da kuma ayyukansa? Waɗanne darussa za mu koya daga ayyukan sarakuna, annabawa, da kuma wasu da aka ambata a cikin wannan littafin? Bari mu ga abin da za mu koya daga wannan littafin na Sarakuna na Biyu.

ELISHA YA GĀJI ILIYA

(2 Sarakuna 1:1–8:29)

Sarki Ahaziya na Isra’ila ya faɗi a gidansa ya ji ciwo. Ya yi tambaya ta annabi Iliya kuma ya sami labarin cewa zai mutu. Ahaziya ya mutu, sai ɗan’uwansa Yehoram ya hau gadon sarauta. Sa’an nan, Yehoshafat ne sarkin Yahuza. Aka ɗauki Iliya ta guguwa, sai kuma mataimakinsa Elisha ya gaje shi wajen annabci. Cikin shekaru 60 na hidimarsa da ya biyo baya, Elisha ya yi mu’ujizai masu yawa.—Dubi akwati “Mu’ujizan Elisha.”

Sa’ad da sarkin Mowabawa ya yi wa Isra’ila tawaye, Yehoram, Yehoshafat, da kuma sarkin Edom suka tare da shi da yaƙi. Aka ba su nasara domin amincin Yehoshafat. Daga baya, sarkin Suriya ya yi shirin kai wa Isra’ila hari ba zato. Amma, Elisha ya ɓata masa sha’ani. Sarkin Suriya ya fusata ya aika da “dawakai, da karusai, da sojoji da yawa” su kama Elisha. (2 Sarakuna 6:14) Elisha ya yi mu’ujizai biyu da suka sa Suriyawan suka koma cikin kwanciyar hankali. Da shigewar lokaci, Sarkin Suriya Ben-hadad ya yi wa Samariya kwanton ɓauna. Hakan ya jawo muguwar yunwa, amma Elisha ya annabta cewa yunwar za ta ƙare.

Bayan wani lokaci, Elisha ya tafi Dimashƙa. Sarki Ben-hadad, sa’an nan yana ciwo, sai ya aiki Hazayel ya yi tambaya ko zai tashi daga ciwonsa. Elisha ya annabta cewa sarkin zai mutu kuma Hazayel zai ɗare gadon sarauta. Washegari, sai Hazayel ya “ɗauki bargo, ya tsoma a ruwa,” ya shaƙe sarkin da shi ya kashe shi ya karɓi sarauta. (2 Sarakuna 8:15) A Yahuza kuma ɗan sarki Yehoshafat, Yehoram ya zama sarki, shi ma ɗansa Ahaziya ya gaje shi.—Dubi akwatin nan “Sarakunan Yahuza da Isra’ila.”

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

2:9—Me ya sa Elisha ya roƙi ‘rabon ɗan fari na ruhun Iliya’? Domin ya cika hakkinsa na annabci ga Isra’ila, Elisha zai bukaci irin ruhu da Iliya ya nuna, na gaba gaɗi da rashin tsoro. Fahimtar haka, Elisha ya roƙi kashi biyu na ruhun Iliya. Iliya ya naɗa Elisha ya zama magajinsa kuma Elisha ya yi masa hidima na shekara shida, saboda haka Elisha ya ɗauki Iliya ubansa ne na ruhaniya; Elisha kamar ɗan fari yake na ruhaniya ga Iliya. (1 Sarakuna 19:19-21; 2 Sarakuna 2:12) Saboda haka, kamar yadda ɗan fari na zahiri yake samun kashi biyu na gadon ubansa, Elisha ya roƙi kashi biyu na gado ta ruhaniya daga Iliya.

2:11—Ina ne “sama” da Iliya ya je “cikin guguwa”? Wannan ba wani wuri ba ne mai nisa na sararin samaniya na zahiri ko kuma wurin da Allah da mala’ikunsa suke zaune. (Maimaitawar Shari’a 4:19; Zabura 11:4; Matiyu 6:9; 18:10) “Sama” inda Iliya ya je sama ce inda tsuntsaye suke firiya. (Zabura 78:26; Matiyu 6:26) A bayane yake cewa karusar wuta ta kai Iliya zuwa wani ɓangaren duniya, inda ya ci gaba da rayuwa na wani lokaci. Hakika, bayan wasu shekaru, Iliya ya rubuta wa Yehoram sarkin Yahuza wasiƙa.—2 Tarihi 21:1, 12-15.

5:15, 16—Me ya sa Elisha bai karɓi kyautar Na’aman ba? Elisha ya ƙi ya karɓa ne domin ya fahimci cewa mu’ujizar warkar da Na’aman ya faru ne da ikon Jehobah ba na shi ba. Bai yi tunani ma na yadda zai amfani kansa da aiki da Allah ya ba shi ba. Masu bauta ta gaskiya a yau ba sa biɗan su amfani kansu da hidimar Jehobah. Suna biyayya da umurnin Yesu: “Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta.”—Matiyu 10:8.

5:18, 19—Na’aman ya nemi gafara ne domin ya saka hannu a bauta? Wataƙila sarkin Suriya tsoho ne kuma ya raunana yana bukatar tokara da Na’aman. Sa’ad da sarkin ya rusuna yana bauta ga Rimmon, Na’aman ma ya rusuna. Amma Na’aman ya rusuna ne kawai domin ya tokara wa sarkin amma ba domin bauta ba. Na’aman yana roƙon Jehobah ne ya gafarta masa domin ya aikata wannan aiki. Da yake ya gaskata abin da Na’aman ya ce, Elisha ya ce masa: “Ka sauka lafiya.”

Darussa Domin Mu:

1:13, 14. Koyo daga lura da kuma yin abubuwa cikin tawali’u zai ceci rayuka.

2:2, 4, 6. Ko da yake Elisha ya kasance mai yi wa Iliya hidima wataƙila na shekara shida, ya nace ba zai bar shi ba. Wannan misali ne mai kyau na aminci da abokantaka!—Karin Magana 18:24.

2:23, 24. Ainihin dalilin yi wa Elisha ba’a shi ne wai mutum mai sanƙo yana sanye da tufafin Iliya. Yaran sun fahimci cewa Elisha wakilin Jehobah ne amma ba sa son sa a yankin ne kawai. Sun ce masa “ka bar wurin nan,” wato, ka ci gaba da tafiya zuwa Betel ko kuma a ɗauke ka kamar yadda aka ɗauki Iliya. Wataƙila yaran sun nuna irin ƙiyayya ne na iyayensu. Yana da muhimmanci iyaye su koya wa yaransu su daraja wakilan Allah!

3:14, 18, 24. Kalmar Jehobah a ko yaushe tana kasancewa gaskiya.

3:22. Hasken rana da safiya ya sa ruwa ta bayyana kamar jini, wataƙila kuma domin sababbin kunyoyi da aka yi sun haɗa da jan taɓo. Jehobah yana iya yin amfani da yanayi ya cim ma nufinsa.

4:8-11. Fahimtar cewa Elisha “adali ne, mutumin Allah,” wata mata a Shunem ta yi masa kirki. Bai kamata mu ma mu yi haka ba ga masu bauta wa Jehobah da aminci?

5:3. ’Yar yarinya Ba’isra’iliya ta tabbata cewa Allah zai iya yin mu’ujiza. Kuma ta kasance da gaba gaɗi ta yi magana game da bangaskiyarta. Ku matasa kuna ƙoƙari ku ƙarfafa bangaskiyarku a alkawuran Allah kuma ku yi gaba gaɗi wajen gaya wa malamanku da ’yan’uwanku ɗalibai gaskiya?

5:9-19. Misalin Na’aman bai nuna ba ne cewa mutum mai fahariya zai iya koyon tawali’u?—1 Bitrus 5:5.

5:20-27. Sakamakon ƙarya ba shi da daɗi! Tunanin irin baƙin ciki da kuma masifa da yin rayuwa iri biyu zai jawo zai iya taimaka mana mu guji wannan tafarkin.

AN KWASHI ISRA’ILA DA YAHUZA BAUTA

(2 Sarakuna 9:1–25:30)

An naɗa Yehu ya zama sarkin Isra’ila. Bai ɓata lokaci ba wajen halaka gidan Ahab. Yehu cikin basira ya ‘kawar da masu bauta wa Ba’al daga Isra’ila.’ (2 Sarakuna 10:28) Da ta sami labarin cewa Yehu ya kashe ɗanta, uwar Ahaziya, Ataliya, sai ta ‘halaka dukan ’ya’yan sarauta na masarautar Yahuza’ ta kwace gadon sarauta. (2 Sarakuna 11:1) Jaririn Ahaziya, Yowash ne kawai aka ceta, bayan shekara shida na ɓoye-ɓoye aka naɗa shi sarkin Yahuza. Firist Yehoyada ya umurce shi, Yowash ya ci gaba da yin abin da ke mai kyau a gaban Jehobah.

Bayan Yehu, dukan sarakuna da suka yi sarauta a Isra’ila sun yi abin da ke mugu a gaban Jehobah. Elisha ya rasu a lokacin sarautar jikan Yehu. Sarkin Yahuza na huɗu bayan Yowash shi ne Ahaz, kuma ‘bai yi abin da ke mai kyau a gaban Jehobah ba.’ (2 Sarakuna 16:1, 2) Amma ɗansa Hezekiya ya tabbatar da kansa sarki wanda ya ‘manne wa Jehobah.’ (2 Sarakuna 17:20; 18:6) A shekara ta 740 K.Z., sa’ad da Hezekiya yake sarauta a Yahuza kuma Hosheya yake sarauta bisa Isra’ila, Sarki Shalmanesa na Assuriya ‘ya kama Samariya kuma ya kwashi Isra’ilawa zuwa bauta a Assuriya.’ (2 Sarakuna 17:6) Daga baya, aka kawo bare cikin yankin Isra’ila, haka addinin Samariya ya sami kahuwa.

A tsakanin sarakuna bakwai da suka bi bayan Hezekiya a Yahuza, Yosiya ne kawai ya yi ƙoƙari ya kawar da bauta ta ƙarya a ƙasar. A ƙarshe, a shekara ta 607 K.Z., Babiloniyawa suka kama Urushalima “haka aka kai mutanen Yahuza zuwa zaman talala.”—2 Sarakuna 25:21.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

13:20, 21—Wannan mu’ujizar ta goyi bayan bautar waɗanda addinai suka ɗaukaka? A’a, ko kaɗan. Littafi Mai Tsarki bai nuna ba cewa an taɓa bauta wa ƙasusuwan Elisha. Ikon Allah ne ya sa wannan mu’ujiza ta faru, kamar dukan sauran mu’ujizai da Elisha ya yi sa’ad da yake raye.

15:1-6—Me ya sa Jehobah ya harbi Azariya (wato Uzziya,) da kuturta? “Amma sa’ad da [Uzziya] ya yi ƙarfi, sai ya shiga girmankai, . . . Sai ya yi izgili a gaban Ubangiji Allahnsa, ya shiga Haikalin Ubangiji don ya ƙona turare a bisa bagaden ƙona turare.” Sa’ad da firistoci ‘suka tasam ma Uzziya’ suka ce masa ya “fita daga wurin nan mai tsarki,” sai ya yi fushi da firistocin sai kuturta ta faso a goshinsa.—2 Tarihi 26:16-20.

18:19-21, 25—Hezekiya ya yi kawance ne da ƙasar Masar? A’a. Tuhumar Rabshake ƙarya ce, kamar yadda ya yi da’awar cewa ya zo ne da ‘yardar Jehobah.’ Sarki Hezekiya ya dogara ne ƙwarai ga Jehobah.

Darussa Domin Mu:

9:7, 26. Hukunci mai tsanani ga gidan Ahab ya nuna cewa Jehobah yana ƙin bauta ta ƙarya da kuma kashe mutane marasa laifi.

9:20. Suna da Yehu ya yi wajen sukuwa ya ba da tabbacin himmarsa wajen cika aikin da aka ba shi. An san ka da himma wajen shelar Mulki?—2 Timoti 4:2.

9:36, 37; 10:17; 13:18, 19, 25; 14:25; 19:20, 32-36; 20:16, 17; 24:13. Za mu iya tabbata cewa ‘magana da ta fita daga bakin Jehobah hakika za ta yi nasara.’—Ishaya 55:10, 11.

10:15. Kamar yadda Yehonadab ya karɓi gayyatar Yehu da zuciya ɗaya ya hau karusarsa, “ƙasaitaccen taro” da son rai suke taimakon Yesu Kristi, Yehu na zamani, da kuma mabiyansa shafaffu.—Wahayin Yahaya 7:9.

10:30, 31. Ko da yake tarihin Yehu ba wanda babu aibi ba ne, Jehobah ya nuna godiya ga dukan abin da ya yi. Hakika, ‘Allah ba marar adalci ba ne, har da zai manta da aikinmu.’—Ibraniyawa 6:10.

13:14-19. Tun da jikan Yehu Yehowash bai nuna ƙwazo ba ya harba kibiya sau uku kawai, bai sami cikakkiyar nasara ba a kan Suriyawa. Jehobah yana so mu yi wannan aikin da aka ba mu da zuciya ɗaya da himma.

20:2-6. Jehobah yana “amsa addu’o’i.”—Zabura 65:2.

24:3, 4. Domin alhakin jini na Manassa, Jehobah bai ‘gafarta’ wa Yahuza ba. Allah yana daraja jinin marasa laifi. Mu tabbata cewa Jehobah zai ɗauki fansa domin jinin marasa laifi ta wajen halaka waɗanda suke da hakkin zubar da su.—Zabura 37:9-11; 145:20.

Da Muhimmanci a Garemu

Littafin Sarakuna na Biyu ya nuna cewa Jehobah mai cika alkawuransa ne. Kwasan mazauna masarautan biyu zuwa bauta, da farko, Isra’ila sai kuma Yahuza, ya nanata mana ƙwarai yadda annabce-annabce da aka rubuta a Maimaitawar Shari’a 28:15–29:28 suka cika. Sarakuna na Biyu ya kwatanta Elisha cewa annabi ne mai himma ga sunan Jehobah da kuma bauta ta gaskiya. Hezekiya da Yosiya an nuna cewa sarakuna ne masu tawali’u waɗanda suka daraja Dokar Allah.

Sa’ad da muka yi bimbini a kan halaye da kuma ayyukan sarakunan, annabawan, da kuma wasu da aka ambata a Sarakuna na Biyu, ba mu koyi darussa game da abin da za mu yi fama a kai ba da kuma abubuwa da za mu guje wa? (Romawa 15:4; 1 Korantiyawa 10:11) Hakika, “maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki.”—Ibraniyawa 4:12.

[Box/Hoto a shafi na 29]

MU’UJIZAR ELISHA

1. An raba ruwan kogin Urdun.—2 Sarakuna 2:14

2. An tsabtace mummunan ruwa daga Yariko ya zama mai kyau.—2 Sarakuna 2:19-22

3. Namomin daji suka tasam wa yara masu laifi.—2 Sarakuna 2:23, 24

4. An bai wa sojoji ruwa.—2 Sarakuna 3:16-26

5. Gwauruwa ta sami mai.—2 Sarakuna 4:1-7

6. Bashunemiya marar haihuwa ta sami ciki.—2 Sarakuna 4:8-17

7. An tashi yaro daga matattu.—2 Sarakuna 4:18-37

8. Jar miya mai guba ta zama tana ciwuwa.—2 Sarakuna 4:38-41

9. An ciyar da mutane ɗari da burodi 20.—2 Sarakuna 4:42-44

10. An warkar da kuturtar Na’aman.— 2 Sarakuna 5:1-14

11. Kuturtar Na’aman ta koma kan Gehazi.—2 Sarakuna 5:24-27

12. Kan gatari ya yi bambaro a kan ruwa.—2 Sarakuna 6:5-7

13. Bara ya ga karusan mala’iku.—2 Sarakuna 6:15-17

14. Sojojin Suriya sun makance.—2 Sarakuna 6:18

15. An buɗe idon sojojin Suriya.—2 Sarakuna 6:19-23

16. Matacce ya tashi.—2 Sarakuna 13:20, 21

[Box/Hotuna a shafi na 31]

SARAKUNAN YAHUZA DA ISRA’ILA

Saul/Dauda/Sulemanu: 1117/1077/1037 K.Z.*

MASARAUTAR YAHUZA KWANAN WATA (K.Z.) MASARAUTAR ISRA’ILA

Rehobowam ․․ 997 ․․ Yerobowam

Abaija/Asa ․․ 980/978 ․․

․․ 976/975/952 ․․ Nadab/Ba’asha/Elah

․․ 951/951/951 ․․ Zimri/Omri/Tibni

․․ 940 ․․ Ahab

Yehoshafat ․․ 937 ․․

․․ 920/917 ․․ Ahaziya/Yehoram

Yehoram ․․ 913 ․․

Ahaziya ․․ 906 ․․

(Ataliya) ․․ 905 ․․ Yehu

Yehowash ․․ 898 ․․

․․ 876/859 ․․ Yehoahaz/Yehowash

Amaziya ․․ 858 ․․

․․ 844 ․․ Yerobowam II

Azariya (Uzziya) ․․ 829 ․․

․․ 803/791/791 ․․ Zekariya/Shallum/Menahem

․․ 780/778 ․․ Fekahiya/Feka

Jotam/Ahaz ․․ 777/762 ․․

․․ 758 ․․ Yusha’u

Hezekiya ․․ 746 ․․

․․ 740 ․․ Kama Samariya

Manassa/Amon/Yosiya ․․ 717/661/659 ․․

Yehowahaz/Yehoiakim ․․ 628/628 ․․

Yehoiakin/Zedekiya ․․ 618/617 ․․

Halakar Urushalima ․․ 607 ․․

[Hasiya]

Kwanakin wata na shekarar fara sarauta ne.

[Hoto a shafi na 27]

Na’aman ya ƙasƙantar da kansa kuma an warkar da shi da ikon Jehobah

[Hoto a shafi na 28]

Menene ya sami Iliya sa’ad da ya ta shi “sama cikin guguwa”?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba