Alhamis, 16 ga Oktoba
Ku shirya wa Yahweh hanya a daji, ku gyara hanya a hamada domin Allahnmu!—Isha. 40:3.
Wannan tafiyar za ta iya ɗauki Israꞌilawan watanni huɗu. Amma Jehobah ya yi alkawari cewa zai kawar da duk wani abin da zai iya hana su komawa. A ganin Yahudawa masu aminci, komawa ƙasar Israꞌila zai kawo musu albarka sosai fiye da sadaukarwa da za su yi. Albarka mafi muhimmanci da za su samu ita ce bautar da za su yi wa Jehobah. A Babila, babu haikali inda Yahudawan za su riƙa miƙa hadayu ga Jehobah kamar yadda Dokar Musa ta ce, kuma babu firistoci. Ƙari ga haka, mutanen da suke bauta ma allolin ƙarya sun fi waɗanda suke bauta wa Jehobah yawa sosai. Don haka, dubban Yahudawa da suke ƙaunar Jehobah suna marmarin lokacin da za su koma ƙasarsu domin su maido da bauta ta gaskiya. w23.05 14-15 sakin layi na 3-4
Jumma’a, 17 ga Oktoba
Ku yi zaman mutanen haske.—Afis. 5:8.
Ruhu mai tsarki ne zai taimaka mana mu ci-gaba da ‘zama mutanen haske.’ Me ya sa? Domin yin rayuwa mai tsarki a wannan duniyar da ke cike da halin lalata, bai da sauƙi ko kaɗan. (1 Tas. 4:3-5, 7, 8) Ruhu mai tsarki zai iya taimaka mana mu kauce ma irin tunanin mutanen da ke duniyar nan, waɗanda raꞌayinsu dabam yake da na Allah. Ruhu mai tsarki zai kuma taimaka mana mu dinga yin “ayyuka masu kyau, da zaman adalci.” (Afis. 5:9) Wani abin da za mu iya yi don mu sami ruhu mai tsarki shi ne, mu roƙi Allah cewa ya ba mu ruhunsa. Yesu ya ce Jehobah ‘zai ba da ruhu mai tsarki ga masu roƙonsa.’ (Luk. 11:13) Ƙari ga haka, idan muna yabon Jehobah tare da ꞌyanꞌuwanmu a taro, Jehobah zai ba mu ruhunsa. (Afis. 5:19, 20) Idan muna da ruhu mai tsarki, zai taimaka mana mu riƙa yin abin da Allah yake so. w24.03 23-24 sakin layi na 13-15
Asabar, 18 ga Oktoba
Ku yi ta roƙo za a ba ku. Ku yi ta nema za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a buɗe muku.—Luk. 11:9.
Kana bukatar ka ƙara zama mai haƙuri? Idan haka ne ka roƙi allah ya ba ka wannan halin. Haƙuri yana ɗaya daga cikin halayen da ruhu mai tsarki yake ba mu. (Gal. 5:22, 23) Don haka, za mu iya roƙan Allah ya ba mu ruhu mai tsarki, kuma ya sa mu kasance da halayen da ruhun yake haifarwa. Idan mun shiga yanayi da ke bukatar mu yi haƙuri, mu “yi ta roƙo” Allah ya ba mu ruhu mai tsarki don mu iya yin haƙuri. (Luk. 11:13) Za mu kuma iya roƙan Jehobah ya taimaka mana mu kasance da irin raꞌayinsa game da abubuwa. Bayan mun yi adduꞌa, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ci-gaba da yin haƙuri a kullum. Idan mun ci-gaba da roƙan Jehobah ya sa mu ƙara zama masu haƙuri, kuma muka ci-gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu nuna haƙuri, Jehobah zai taimaka mana mu kasance da halin nan ko da ba mu da shi a dā. Zai kuma taimaka mana mu yi tunani mai zurfi a kan labarai da ke Littafi Mai Tsarki. A Littafi Mai Tsarki, akwai labaran mutane da yawa da suka nuna haƙuri. Yin tunani a kan labaransu zai taimaka mana mu zama masu haƙuri. w23.08 22 sakin layi na 10-11