DARASI NA 05
Littafi Mai Tsarki Saƙo Ne Daga Allah
Jehobah ya ba mu Littafi Mai Tsarki. Wannan kyauta ce mai kyau sosai da ke ɗauke da littattafai 66. Amma kana iya cewa: ‘Ta yaya muka samu Littafi Mai Tsarki? Wane ne mawallafinsa?’ Don mu amsa waɗannan tambayoyin, bari mu tattauna yadda aka samo Littafi Mai Tsarki.
1. Da yake ’yan Adam ne suka rubuta Littafi Mai Tsarki, me ya sa muka ce Allah ne mawallafinsa?
Mutane wajen 40 ne suka rubuta Littafi Mai Tsarki. An rubuta littafi na farko wajen shekaru 3,500 da suka shige, littafi na ƙarshe kuma wajen shekaru 1,900 da suka shige. Marubutan ba su rayu a lokaci ɗaya ba. Wasu cikinsu makiyaya ne da masu kamun kifi da kuma sarakuna. Duk da haka, abin da suka rubuta a Littafi Mai Tsarki sun jitu da juna. Ta yaya hakan ya yiwu? Domin Allah ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki. (Karanta 1 Tasalonikawa 2:13.) Marubutan ba su rubuta ra’ayinsu ba. Amma ‘ruhun Allaha ne ya shiga zukatansu’ kuma suka faɗi “abin da suka karɓa daga wurin Allah.” (2 Bitrus 1:21) Allah ya yi amfani da ruhunsa don ya sa su rubuta kalmarsa.—2 Timoti 3:16.
2. Wane ne zai iya amfana daga Littafi Mai Tsarki?
Allah ya ce “kowace al’umma, da zuriya, da yare, da kabila” za su iya amfana daga saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:6.) A yau, an wallafa Littafi Mai Tsarki a harsuna da yawa fiye da kowane littafi. Kusan kowa yana iya karanta Littafi Mai Tsarki, ko a wace ƙasa yake da zama da kuma yaren da yake yi.
3. Ta yaya Jehobah ya kāre Littafi Mai Tsarki?
An rubuta Littafi Mai Tsarki a kan abubuwan da ba sa daɗewa kamar su fata da takardar ganye. Mutanen da ke son Kalmar Allah sun mai da hankali sosai yayin da suke kofar ta da hannu. Duk da cewa mutane masu iko sun yi iya ƙoƙarinsu don su hallaka Littafi Mai Tsarki, wasu sun sadaukar da ransu don su kāre shi. Jehobah bai bar mutane ko wani abu ya hana mu samun Littafi Mai Tsarki ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Maganar Allahnmu tana nan har abada!”—Ishaya 40:8.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu ƙara koyan yadda Allah ya sa mutane suka rubuta Kalmarsa, yadda ya kāre ta, kuma ya sa kowa ya sami zarafin karanta ta.
4. Littafi Mai Tsarki ya bayyana Mawallafinsa
Ku kalli BIDIYON nan. Sai ku karanta 2 Timoti 3:16, kuma ku tattauna tambayoyin da ke gaba.
Tun da ’yan Adam ne suka rubuta Littafi Mai Tsarki, me ya sa ake kiransa Kalmar Allah?
Kana ganin ya dace mu gaskata cewa Allah ne ya sa mutane su rubuta Kalmarsa?
Idan sakatare ya rubuta wasiƙa, saƙon da ke wasiƙar ba nasa ba ne, amma na wanda ya gaya masa abin da zai rubuta ne. Hakazalika, ’yan Adam ne suka rubuta Littafi Mai Tsarki, amma saƙon da ke cikinsa na Allah ne
5. Mutane sun kasa hallaka Littafi Mai Tsarki
Allah ya kāre Littafi Mai Tsarki domin Kalmarsa ne. Mutane masu iko sun yi shekaru da yawa suna ƙoƙarin su hallaka Littafi Mai Tsarki. Malaman addinai ma sun yi ƙoƙari su hana mutane karanta shi. Duk da cewa an yi barazanar kashe su, mutane da yawa sun sadaukar da ransu don su kāre Littafi Mai Tsarki. Idan kana so ka san ɗaya cikin mutanen nan, ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.
Za ka so ka karanta Littafi Mai Tsarki yanzu da ka san famar da mutane suka yi don su kāre shi? Me ya sa ka ce haka?
Ku karanta Zabura 119:97, sai ku tattauna tambayar nan:
Mene ne ya sa mutane da yawa suka yi kasada don su fassara da kuma rarraba Littafi Mai Tsarki?
6. Littafi don dukan mutane
Littafi Mai Tsarki ne littafin da aka fi fassarawa da kuma rarrabawa a duniya. Ku karanta Ayyukan Manzanni 10:34, 35, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Me ya sa Allah ya sa aka fassara Kalmarsa kuma aka rarraba ta a faɗin duniya?
Mene ne ka fi so game da Littafi Mai Tsarki?
Kusan
kowa
a duniya
zai iya karanta Littafi Mai Tsarki a yaren da yake ji
Akwai a harsuna fiye da
3,000
rabi ko gabaki ɗayansa
An wallafa kofofi wajen
5,000,000,000
kuma babu littafin da yawansa ya kai hakan
WASU SUN CE: “Littafi Mai Tsarki tsohon littafi ne da ’yan Adam suka rubuta.”
Mene ne ra’ayinka?
Me ya nuna cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ne?
TAƘAITAWA
Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ne, kuma Allah ya tabbata cewa kowa zai iya samun sa kuma ya karanta.
Bita
Mene ne muke nufi sa’ad da muka ce Allah ne ya hure mutane su rubuta Littafi Mai Tsarki?
Ta yaya yadda ake fassara da rarraba Littafi Mai Tsarki da kuma yadda ya tsira ya burge ka?
Yaya kake ji yanzu da ka san matakan da Allah ya ɗauka don ka san Kalmarsa?
KA BINCIKA
Ku karanta talifin nan don ku koyi game da tarihin Littafi Mai Tsarki, da kuma yadda aka fassara shi daga rubuce-rubuce na dā zuwa na zamani.
Ku karanta talifin nan don ku koyi yadda aka so a hallaka Littafi Mai Tsarki sau uku, amma ba a yi nasara ba.
“Yadda Aka Kāre Littafi Mai Tsarki” (Hasumiyar Tsaro Na 4 2016)
Ku kalli bidiyon nan ku ga yadda wasu suka yi kasada da ransu don su fassara Littafi Mai Tsarki.
An kofa da kuma fassara Littafi Mai Tsarki sau da yawa. Ku karanta talifin nan don ku san abin da ya tabbatar mana cewa ba a canja saƙon da ke cikinsa ba.
“An Canja Ko Kuma Sake Saƙon Littafi Mai Tsarki Ne?” (Talifin jw.org)
a A darasi na 7, za mu tattauna cewa ruhu mai tsarki iko ne da Allah yake amfani da shi don ya cim ma nufinsa.