DARASI NA 23
Za Ka Amfana Sosai Idan Ka Yi Baftisma!
Yesu ya ce wajibi ne Kiristoci su yi baftisma. (Karanta Matiyu 28:19, 20.) Amma yaya ake yin baftisma? Kuma mene ne mutum zai yi don ya cancanci yin baftisma?
1. Mene ne yin baftisma?
An samo kalmar nan “baftisma” daga wata kalmar Hellenanci da take nufin “a tsoma” abu a cikin ruwa. A lokacin da aka yi wa Yesu baftisma, an nitsar da shi a cikin Kogin Urdun, sa’an nan ya “fito daga ruwan.” (Matiyu 3:13, 16) Hakazalika, Kiristoci na gaske sukan tsoma ko nitsar da mutum a cikin ruwa sa’ad da ake yi masa baftisma.
2. Idan mutum ya yi baftisma, me hakan ya nuna?
Idan mutum ya yi baftisma, hakan ya nuna cewa ya yi alkawarin bauta wa Jehobah. Ta yaya mutum zai yi wannan alkawarin? Kafin ya yi baftisma, mutumin zai yi addu’a ga Jehobah cewa zai bauta masa har abada. A cikin addu’ar, zai yi alkawarin bauta wa Jehobah shi kaɗai, kuma ya gaya masa cewa yin nufinsa ne zai zama abu mafi muhimmanci a rayuwarsa. Sa’an nan ya zaɓi “ya ƙi kansa, . . . ya bi” misalin Yesu da koyarwarsa babu fashi. (Matiyu 16:24) Yin baftisma zai sa ya kasance da dangantaka ta kud da kud da Jehobah da kuma ’yan’uwa masu bi.
3. Mene ne mutum zai yi don ya yi baftisma?
Kafin ka yi baftisma, wajibi ne ka koyi abubuwa game da Jehobah kuma ka kasance da bangaskiya. (Karanta Ibraniyawa 11:6.) Idan ka ci gaba da koya game da Jehobah kuma ka daɗa kasancewa da bangaskiya, hakan zai sa ka ƙaunaci Jehobah sosai. Ban da haka, za ka so ka gaya wa mutane game da shi, kuma ka yi rayuwar da ta jitu da nufinsa. (2 Timoti 4:2; 1 Yohanna 5:3) Idan mutum yana rayuwar da ta “cancanta da masu bin Ubangiji,” hakan zai iya sa ya yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ya yi baftisma.—Kolosiyawa 1:9, 10.a
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu koyi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da yadda aka yi wa Yesu baftisma da kuma yadda mutum zai yi shirin ɗaukan matakin nan mai muhimmanci.
4. Me za mu koya daga baftismar Yesu?
Ku karanta Matiyu 3:13-17 don ku koyi ƙarin abubuwa game da yadda aka yi wa Yesu baftisma. Sai ku tattauna tambayoyin nan:
Yesu jariri ne sa’ad da ya yi baftisma?
Yaya aka yi masa baftisma? Yayyafa masa ruwa kawai aka yi?
Bayan da Yesu ya yi baftisma ne ya soma aiki na musamman da Allah ya ba shi. Ku karanta Luka 3:21-23 da Yohanna 6:38, sai ku tattauna tambayar nan:
Bayan Yesu ya yi baftisma, wane aiki ne ya sa a gaba a rayuwarsa?
5. Yin baftisma maƙasudi ne da za ka iya cim ma
Yin alkawarin bauta wa Jehobah da yin baftisma zai iya yi maka wuya da farko. Amma za ka iya ci gaba da koya game da Jehobah kuma ka ƙara kusantar sa, hakan zai taimaka maka ka yanke wannan shawarar mai muhimmanci. Don ku ga wasu da suka yi hakan, ku kalli BIDIYON nan.
Ku karanta Yohanna 17:3 da Yakub 1:5, sai ku tattauna tambayar nan:
Me zai taimaka wa mutum ya yi shirin yin baftisma?
Muna yin alkawarin bauta wa Jehobah ta wurin gaya masa cikin addu’a cewa za mu bauta masa har abada
Sa’ad da muka yi baftisma, hakan ya nuna cewa mun yi alkawarin bauta wa Allah
6. Idan mun yi baftisma, mun zama ɗaya cikin masu bauta wa Jehobah
Idan mun yi baftisma, mun zama ɗaya cikin masu bauta wa Jehobah da haɗin kai a faɗin duniya. Ko da daga wace ƙasa ce Shaidun Jehobah suka fito, imaninsu da kuma ƙa’idodin da suke bi ɗaya ne. Ku karanta Zabura 25:14 da 1 Bitrus 2:17, sai ku tattauna tambayar nan:
Ta yaya yin baftisma yake shafan dangantakarmu da Jehobah da kuma ’yan’uwa masu bi?
WASU SUN CE: “Ban shirya yin baftisma ba.”
Idan haka ne kake ji, kana ganin baftisma maƙasudi ne da za ka iya cim ma?
TAƘAITAWA
Yesu ya ce wajibi ne Kiristoci su yi baftisma. Kafin mutum ya yi baftisma, yana bukatar ya ba da gaskiya ga Jehobah, ya bi ƙa’idodinsa, kuma ya yi alkawarin bauta masa.
Bita
Mene ne yin baftisma, kuma me ya sa yake da muhimmanci?
Wace alaƙa ce ke tsakanin baftisma da kuma alkawarin bauta wa Jehobah?
Waɗanne matakai ne mutum zai ɗauka kafin ya yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ya yi baftisma?
KA BINCIKA
Ku karanta talifin nan don ku ga abin da yin baftisma yake nufi da abin da ba ya nufi.
Ku karanta talifin nan don ku ga abubuwa da mutum zai yi don ya cancanci yin baftisma.
“Ƙauna ga Jehobah Za Ta Sa Mu Yi Baftisma” (Hasumiyar Tsaro, Maris 2020)
Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya sa wani mutum ya yi baftisma.
“Suna So In Gano wa Kaina Gaskiyar Littafi Mai Tsarki” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Maris, 2013)
Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya sa yake da muhimmanci mutum ya yi baftisma da kuma yadda zai yi shirin yin hakan.
a Idan mutum ya yi baftisma a wani addini a dā, yana bukatar ya sake yin baftisma. Me ya sa? Domin ba a koyar da gaskiyar da ke Kalmar Allah a waccan addinin.—Ka duba Ayyukan Manzanni 19:1-5 da Darasi na 13.