Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp16 Na 6 pp. 4-7
  • Wahayi Game da Ruhohin da Ke Sama

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wahayi Game da Ruhohin da Ke Sama
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • JEHOBAH NE MAƊAUKAKI
  • YESU YANA HANNUN DAMA NA ALLAH
  • MALA’IKU SUNA WA ALLAH HIDIMA
  • SHAIƊAN YANA YAUDARAR MILIYOYIN MUTANE
  • MUTANEN DA AKA ZAƁO DAGA DUNIYA
  • ABIN DA MAZAUNAN SAMA ZA SU YI
  • Mala’iku ‘Ruhohi Ne Masu-hidima’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Tawaye a Cikin Lardi na Ruhu
    Ruhohin Matattu—Zasu Taimake Ka ne ko Kuwa Zasu Yi Maka Barna? Sun Wanzu Kuwa Da Gaske?
  • Su Waye Suke Zama a Duniya ta Ruhu?
    Hanyar Rai Madawwami​—Ka Same ta Kuwa?
  • Gaskiya Game da Mala’iku da Kuma Aljanu
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
wp16 Na 6 pp. 4-7
Yesu ya tsaya a gefen dama na kursiyin Jehobah, yana kewaye da mala’iku

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | MENE NE YAKE FARUWA A SAMA?

Wahayi Game Da Ruhohin Da ke Sama

Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da wahayi masu ƙayatarwa da suka bayyana wasu abubuwan da ke faruwa a sama. Ka yi la’akari da wahayin. Ko da yake ba dukan wahayin za ka ɗauka a zahiri ba, amma za su iya taimaka maka ka san ruhohin da ke sama da kuma yadda za su iya shafar rayuwarka.

JEHOBAH NE MAƊAUKAKI

“Ga kursiyi a kafe cikin sama, da wani kuma a zaune bisa kursiyin: wanda yake zaune kuma bisa yana kama da dutsen jasfer da sardius; bakan gizo kuma yana kewaye da kursiyin, ganinsa yana kama da emeral.”​—Ru’ya ta Yohanna 4:​2, 3.

“Kamar yadda ake ganin bakan gizo da ke cikin girgije ran da aka yi ruwa, hakanan aka ga sheƙin da ke kewaye. Wannan kamanin surar darajar Ubangiji ne.”​—Ezekiyel 1:​27, 28.

Waɗannan wahayin da aka saukar wa manzo Yohanna da kuma annabi Ezekiyel sun kwatanta ɗaukakar Jehobah Maɗaukakin Sarki da abubuwan da za mu iya fahimta, kamar su lu’u lu’ai da bakan gizo da kuma kursiyi. Sun nuna cewa wurin zaman Jehobah yana da ban razana da kuma kyan gaske.

Wannan kwatanci game da Allah ya jitu da furucin wani marubucin zabura da ya ce: “Ubangiji mai-girma ne, abin yabo ne ƙwarai: abin tsoro ne shi gāba da dukan alloli. Gama dukan alloli na dangogi gumaka ne; amma, Ubangiji ya yi sammai. Girma da ɗaukaka suna gabansa: ƙarfi da jamali suna cikin tsatsarkan wurinsa.”​—⁠Zabura 96:​4-6.

Ko da yake Jehobah ne Maɗaukaki, duk da haka, ya ce mu yi addu’a gare shi kuma ya tabbatar mana da cewa zai amsa mana. (Zabura 65:⁠2) Allah yana ƙaunarmu kuma yana kula da mu sosai, shi ya sa manzo Yohanna ya ce: “Allah ƙauna ne.”​—1 Yohanna 4:8.

YESU YANA HANNUN DAMA NA ALLAH

‘[Manzo Istifanus] cike da ruhu mai-tsarki, ya zuba ido zuwa sama, ya ga darajar Allah, da Yesu a tsaye ga hannun dama na Allah, ya ce, Ku duba, ina ganin sammai a buɗe, da Ɗan mutum a tsaye ga hannun dama na Allah.’​—⁠Ayyukan Manzanni 7:​55, 56.

Jim kaɗan kafin Istifanus ya ga wannan wahayin, limaman Yahudawa da yake wa magana sun yi kulle-kulle kuma sun kashe Yesu. Wannan wahayin ya tabbatar da cewa an ta da Yesu daga matattu zuwa sama kuma an ɗaukaka shi. Manzo Bulus ya ba da ƙarin haske a kan wannan batun. Ya ce: Jehobah “ya tashe [Yesu] daga cikin matattu, ya zamshe shi ga hannun damansa cikin sammai, gaba nesa da dukan sarauta, da hukunci, da iko, da mulki, da kowane suna wanda ake ambatonsa, ba cikin wannan zamani kaɗai ba, amma cikin zamani mai-zuwa kuma.”​—Afisawa 1:​20, 21.

Nassosi sun bayyana matsayin Yesu kuma sun nuna cewa yana kula da mutane sosai, kamar Ubansa Jehobah. Sa’ad da Yesu yake hidima a duniya, ya warkar da marasa lafiya kuma ya ta da matattu. Kuma ya nuna cewa yana ƙaunar mutane sosai sa’ad da ya mutu domin ya fanshe mu daga zunubi da mutuwa. (Afisawa 2:​4, 5) Da yake Yesu yana hannun dama na Allah, zai yi amfani da matsayinsa wajen yi wa mutane masu biyayya albarka, nan ba da daɗewa ba.

MALA’IKU SUNA WA ALLAH HIDIMA

Ni annabi Daniyel “ina dubawa sai na ga an ajiye gadajen sarauta, sai wani wanda yake Tun Fil Azal [Jehobah] ya zauna kursiyinsa. . . . Dubun dubbai suna ta yi masa hidima, dubu goma sau dubu goma suka tsaya a gabansa.”​—⁠Daniyel 7:​9, 10, Littafi Mai Tsarki.

A wannan wahayin, Daniyel ya ga mala’iku masu ɗimbin yawa. Babu shakka, wannan wahayi ne mai ban razana! Mala’iku halittu ne na ruhu masu iko da kuma basira. Matsayinsu ya haɗa da seraphim da kerub. Littafi Mai Tsarki ya ambata mala’iku fiye da sau 250.

Mala’iku ba mutane ba ne da suka taɓa rayuwa a duniya. Allah ya halicci mala’iku shekaru da yawa kafin ya halicci mutane. Mala’iku suna wanzuwa sa’ad da Allah ya halicci duniya kuma sun yabe shi don ayyukansa.​—⁠Ayuba 38:​4-7.

Hanya ɗaya da mala’iku suke wa Allah hidima ita ce ta wajen saka hannu a aiki mafi muhimmanci da ake yi a duniya, wato yaɗa bishara ta Mulkin Allah. (Matta 24:14) An bayyana aikin da suke yi a wani wahayin da aka saukar wa manzo Yohanna. Ya ce: “Na ga wani mala’ika kuma yana firiya a tsakiyar sararin sama, yana da bishara ta har abada wadda za ya yi shelarta ga mazaunan duniya, ga kowane iri da ƙabila da harshe da al’umma.” (Ru’ya ta Yohanna 14:⁠6) Ko da yake mala’iku ba sa magana da mutane a yau yadda suke yi a wasu lokuta a zamanin dā, amma suna wa mutanen da ke wa’azi ja-gora zuwa wurin masu son sanin gaskiya.

SHAIƊAN YANA YAUDARAR MILIYOYIN MUTANE

“Aka yi yaƙi cikin sama: Mika’ilu [Yesu Kristi] da nasa mala’iku sun fita su yi gāba da maciji; macijin kuma ya yi gāba tare da nasa mala’iku; ba su rinjaya ba, ba a kuwa ƙara tarar da matsayinsu cikin sama ba. Aka jefar da babban maciji, wato tsohon macijin nan, shi wanda ana ce da shi Iblis da Shaiɗan, mai-ruɗin dukan duniya; aka jefar da shi a duniya, aka jefar da mala’ikunsa kuma tare da shi.”​—Ru’ya ta Yohanna 12:​7-9.

Akwai lokacin da ake tashin hankali sosai a sama. Ba da daɗewa ba bayan Allah ya halicci mutum, wani mala’ika da ke so a riƙa bauta masa, ya yi tawaye da Jehobah kuma ya zama Shaiɗan. Wasu mala’iku ma suka goyi bayansa kuma suka zama aljanu. Waɗannan halittun mugaye ne sosai. Suna gaba da Jehobah kuma sun rinjayi yawancin mutane su yi tawaye da Jehobah.

Shaiɗan da aljanunsa mugaye ne kuma ba su da tausayi. Ba sa son mutane kuma suna jawo wahala sosai a duniya. Alal misali, Shaiɗan ya kashe dabbobin Ayuba mutum mai aminci da kuma bayinsa. Bayan haka, ya kashe duka ʼya’yansa goma ta wajen sa “guguwa” mai-ƙarfi ta rushe gidan da suke ciki. Sai kuma Shaiɗan ya harbi Ayuba da “gyambuna masu-ciwo, tun daga tāfin sawunsa har kan kansa.”​—⁠Ayuba 1:​7-19; 2:7.

Amma, nan ba da jimawa ba, za a halaka Shaiɗan. Tun da aka jefo shi duniya, ya san cewa “sauran zarafinsa kaɗan ya rage.” (Ru’ya ta Yohanna 12:12) Babu abin da zai iya hana a halaka Shaiɗan kuma wannan albishiri ne!

MUTANEN DA AKA ZAƁO DAGA DUNIYA

Yesu ya ‘saye wa Allah mutane daga cikin kowace kabila, da kowane harshe, da al’umma, iri-iri, ya maishe su su zama mulki da firistoci ga Allahnmu; suna kuwa mulki bisa duniya.’​—⁠Ru’ya ta Yohanna 5:​9, 10.

Wasu mutane za su tashi daga matattu zuwa sama kamar yadda Yesu ya yi. Yesu ya ce wa almajiransa masu aminci: Zan “tafi na shirya muku wuri kuma, sai in sake dawowa, in karɓe ku wurin kaina; domin wurin da ni ke, ku zauna kuma.”​—Yohanna 14:​2, 3.

Mene ne waɗannan mutanen za su je yi a sama? Za su yi mulki tare da Yesu bisa duniya kuma su sa kowa ya sami albarka. Wannan Mulkin ne Yesu ya ce almajiransa su yi addu’a a kai sa’ad da ya ce: “Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.”​—Matta 6:​9, 10.

Yesu tare da wasu da aka ta da su daga matattu zuwa sama

ABIN DA MAZAUNAN SAMA ZA SU YI

Ni manzo Yohanna “na ji babbar murya kuwa daga cikin kursiyin, ta ce, Duba, mazaunin Allah yana wurin mutane, . . . zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”​—⁠Ru’ya ta Yohanna 21:​3, 4.

Wannan wahayin ya annabta lokacin da Mulkin Allah, wanda Yesu da kuma wasu mutanen da aka ta da su daga duniya zuwa sama za su yi sarauta kuma su kawo ƙarshen sarautar Shaiɗan. Za su kuma mai da duniyar nan aljanna. Abubuwan da ke sa mutane baƙin ciki ba za su sake kasancewa ba. Har mutuwa ma za ta zama labari.

Me zai faru da biliyoyin mutanen da suka mutu kuma ba su da begen yin rayuwa a sama? Za a tayar da su daga matattu kuma za su yi rayuwa a Aljanna a duniyar nan har abada.​—Luka 23:43.

BA KA BUKATAR KA JI TSORON ALJANU

Miliyoyin mutane suna kamar mutanen da ke gidan yari don sun shaƙu da sihiri kuma suna tsoron miyagun ruhohi. Suna yin tsafi da camfi kuma suna riƙe layu don su kāre kansu. Yin hakan ɓata lokaci ne. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu cewa: “Idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.” (2 Labarbaru 16:⁠9) Jehobah, Allah na gaskiya wanda ya fi Shaiɗan ƙarfi zai kāre ka idan ka dogara gare Shi.

Idan kana so Jehobah ya kāre ka, kana bukatar sanin abubuwan da ke faranta masa rai kuma ka yi su. Alal misali, Kiristocin da ke birnin Afisa a ƙarni na farko sun tattara dukan littattafan sihirinsu kuma sun ƙone su. (Ayyukan Manzanni 19:​19, 20) Hakazalika, idan kana so Allah ya kāre ka, dole ne ka halaka kayan tsafi kamar su layu da gumaka da littattafan sihiri da dukan abubuwan da ke da alaƙa da aljanu.

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku zama fa masu-biyayya ga Allah, amma ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje muku.” (Yaƙub 4:⁠7) Idan ka yi biyayya ga Jehobah kuma kana bauta masa, za ka iya kasancewa da tabbaci cewa Shaiɗan da aljanunsa ba za su iya yin tasiri a kanka ba.

Waɗannan wahayin sun tabbatar mana da cewa Jehobah Allah da Ɗansa, Yesu Kristi, har da mala’iku masu aminci da kuma mutanen da za su yi rayuwa a sama suna ƙaunarmu sosai. Don samun ƙarin bayani a kan abubuwan da za su cim ma, ka tuntuɓi Shaidun Jehobah ko kuma ka shiga dandalin Yanar gizonmu na www.pr418.com/⁠ha kuma ka saukar da littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba