Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • fg darasi na 11 tambayoyi na 1-4
  • Ta Yaya Ne Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki Suke Amfanar Mu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Ne Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki Suke Amfanar Mu?
  • Albishiri Daga Allah!
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Ja-gorar Sawayenka Da Ƙa’idodin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ta Yaya Ne Dokokin Allah Suke Amfanar Mu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Bar Dokokin Allah da Kuma Ka’idodinsa Su Ja-gorance Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Ka Bi Umurnin Allah A Dukan Abu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Albishiri Daga Allah!
fg darasi na 11 tambayoyi na 1-4

DARASI NA 11

Ta Yaya Ne Dokokin Allah Suke Amfanar Mu?

1. Me ya sa muke bukatar ja-gora?

An bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki: Mahaifiya ta saka wa ’yarta igiyar tsaro da ke kujerar cikin mota; Mahaifi da yaronsa sun saka hular kwano; mata mai ciki, wani ma’aikaci yana a faɗake da hularsa

Ta yaya dokokin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu kāre ranmu da kuma na mutane?​—ZABURA 36:9.

Mahaliccinmu ya fi mu hikima. Yana ƙaunarmu kuma yana kula da mu. Kuma bai halicce mu don mu ja-goranci kanmu ba. (Irmiya 10:23) Kamar yadda ƙananan yara suke bukatar ja-gorar iyayensu, hakan ma muke bukatar ja-gorancin Allah. (Ishaya 48:17, 18) Ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki suna mana ja-gora kuma hakan baiwa ce daga Allah.​—Karanta 2 Timotawus 3:16.

Dukan dokokin Jehobah Allah suna da amfani a gare mu. Sun nuna mana hanyar yin rayuwa mafi kyau a yau da kuma yadda za mu iya more albarka na har abada a nan gaba.​—Karanta Zabura 19:7, 11; Ru’ya ta Yohanna 4:11.

2. Ta yaya Kalmar Allah take mana ja-gora?

Wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki sun nuna mana abin da Allah yake son mu yi. Wasu dokoki kuma sun shafi fannoni dabam-dabam na rayuwa. (Kubawar Shari’a 22:8) Wajibi ne mu yi amfani da sanin yakamata don mu san abin da Allah yake son mu yi. (Misalai 2:10-12) Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa rai baiwa ne daga Allah. Wannan dokar za ta iya mana ja-gora a wurin aiki da gida da kuma sa’ad da muke tafiya. Kuma idan mun tuna da hakan, ba za mu sa ranmu da na wasu cikin haɗari ba.​—Karanta Ayyukan Manzanni 17:28.

3. Waɗanne dokoki biyu ne suke da muhimmanci sosai?

Yesu ya yi magana game da dokoki biyu da suke da muhimmanci sosai. Na farko ya bayyana dalilin da ya sa ’yan Adam suke da rai, wato, don su san Allah, su ƙaunace shi kuma su bauta masa da aminci. Ya kamata mu yi la’akari da wannan dokar a duk shawarar da muke son mu yanke. (Misalai 3:6) Waɗanda suke yin biyayya ga wannan dokokin suna zama aminan Allah, suna yin farin ciki na gaske kuma za su samu rai na har abada.​—Karanta Matta 22:36-38.

Doka ta biyu za ta iya sa mu samu dangantaka mai kyau da mutane. (1 Korintiyawa 13:4-7) Bin wannan doka ta biyu tana nufin cewa za mu bi da mutane kamar yadda Allah yake bi da mu.​—Karanta Matta 7:12; 22:39, 40.

4. Ta yaya dokokin Littafi Mai Tsarki suke amfanar mu?

Iyali mai farin ciki

Dokokin Littafi Mai Tsarki suna koya wa iyalai yadda za su kasance da haɗin kai kuma su yi ƙaunar juna. (Kolosiyawa 3:12-14) Kalmar Allah tana kuma kāre iyalai ta wajen koya musu wata doka mai muhimmanci. Allah yana son aure ya dawwama.​—Karanta Farawa 2:24.

Idan mun bin koyarwar Littafi Mai Tsarki, za mu iya kāre dukiyarmu da motsin ranmu. Alal misali, shugabannin aiki sun fi son mutanen da suke bin dokokin Littafi Mai Tsarki na yin gaskiya da kuma aiki tuƙuru. (Misalai 10:4, 26; Ibraniyawa 13:18) Kalmar Allah ta kuma koya mana yadda za mu yi wadar zuci da abubuwan da suke da muhimmanci kuma mu daraja abotarmu da Allah fiye da dukiya.​—Karanta Matta 6:24, 25, 33; 1 Timotawus 6:8-10.

Yin biyayya ga dokokin Allah zai kyautata rayuwarmu. (Misalai 14:30; 22:24, 25) Alal misali, dokar Allah game da yin maye tana kāre mu daga muguwar cuta da kuma haɗarurruka. (Misalai 23:20) Jehobah yana son mu sha giya daidai wa daida. (Zabura 104:15; 1 Korintiyawa 6:10) Dokokin Allah suna amfanar mu ta wajen koya mana yadda za mu yi hankali da abubuwan da muke yi da kuma tunanin da muke yi. (Zabura 119:97-100) Amma, Kiristoci na gaskiya ba sa yin biyayya ga dokokin Allah don su amfane kansu kaɗai. Suna yin haka don su daraja Jehobah.​—Karanta Matta 5:14-16.

Don ƙarin bayani, ka duba babi na 12 da 13 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba