Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/1 pp. 10-12
  • Kashe Kuɗi Yadda Ya Kamata

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kashe Kuɗi Yadda Ya Kamata
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Ƙalubalen?
  • Abubuwa Huɗu da Za Su Sa Ku Yi Nasara
  • Abin da Tattaunawarku Game da Kuɗi Ya Kamata Ya Bayyana
  • Ku Kashe Kuɗi a Hanyar da Ta Dace
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Kudi Shi Ne Tushen Dukan Mugunta Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Me Zai Taimaka Maka Ka Rage Kashe Kudi?
    Tambayoyin Matasa
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/1 pp. 10-12

Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali

Kashe Kuɗi Yadda Ya Kamata

Ya ce: “A gani na, matata Laura,a tana kashe kuɗi a kan abubuwa marar amfani, aƙalla a kan abubuwan da nake ganin ba ma bukata. Kuma kamar ba ta iya ajiye kuɗi! Hakan yakan zama matsala sosai sa’ad da muka sayi abubuwa da ba ma bukata. Ina yawan faɗin cewa idan matata tana riƙe da kuɗi, za ta kashe duka.”

Ta ce: “Wataƙila ba na ajiye isassun kuɗi, amma maigidana bai san ko nawa ake sayar da abubuwa a kasuwa ba, kamar su, abinci, kayan gyara daƙi, da sauran abubuwan da ake bukata a gida, kuma ni ce nake yawan zama a gida. Na san abubuwan da muke bukata, kuma nakan saye su ko da hakan zai jawo gardama game da kuɗi.”

ZANCEN kuɗi yakan zama abu mafi wuya da ma’aurata za su tattauna cikin natsuwa. Babu shakka, shi ya sa ya zama ainihin abin da ke jawo gardama tsakanin ma’aurata.

Ma’auratan da ba su da ra’ayin da ya dace game da kuɗi a yawancin lokaci suna samun alhini, rigima, matsalar motsin rai su kuma ɓata dangantakarsu da Jehobah. (1 Timotawus 6:9, 10) Idan iyaye suka kasa magance matsalar kashe kuɗi hakan zai iya tilasta su su yi aiki na dogon lokaci, kuma su ƙi kula da bukatun kansu da na yaransu su kuma kasa ƙarfafa ruhaniyarsu da ta yaransu. Kuma suna koya wa yaransu su kasance da ra’ayin da bai dace ba game da kuɗi.

“Dukiya, kāriya ce” in ji Littafi Mai Tsarki. (Mai-Wa’azi 7:12) Amma kuɗi zai kāre aurenku da iyalinku ne kawai idan kuka koyi yadda ake tattauna batun kuɗi da juna ba kashe shi ba kawai.b Hakika, maimakon kasancewa masu gardama, tattauna batutuwan kuɗi zai iya ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin ma’aurata.

Amma menene ya sa kuɗi yake jawo matsaloli da yawa a cikin iyali? Kuma waɗanne matakai masu amfani ne za ku iya ɗauka domin tattaunawarku game da kuɗi ya magance matsalar maimakon ya jawo gardama?

Menene Ƙalubalen?

Sau dayawa, saɓani da ake samu game da kuɗi ba saboda kuɗin ba ne amma saboda aminci ne ko tsoro. Alal misali, maigidan da ya ce matarsa ta gaya masa yadda ta kashe kuɗin da ya ba ta yana gaya mata ne cewa ba za ta iya yin amfani da kuɗin iyalin yadda ya dace ba. Kuma matar da take yin gunagunin cewa mijinta ba ya tara isassun kuɗi, wataƙila tana jin tsoro ne cewa wasu abubuwa za su iya faruwa a gaba da za su jawo wa iyalinsu matsalar kuɗi.

Wani ƙalubalen da suke fuskanta shi ne, yadda aka raine su. “Matata ta girma ne a iyalin da ake yin amfani da kuɗi sosai,” in ji Matthew, wanda ya yi aure shekaru takwas da suka wuce. “Ba ta da irin tsoron da nike da shi. Baba na mugun mashayin giya ne da taba sigari, kuma ya daɗe ba ya aiki. A yawancin lokaci muna rayuwa ne ba tare da samun abubuwan da muke bukata, hakan kuma ya sa na soma jin tsoron cin bashi. A wasu lokatai, wannan tsoron yana hana ni nuna sanin ya kamata ga matata idan ya zo ga batutuwan kuɗi.” Ko da menene yake jawo hargitsin, menene za ku iya yi don kuɗi ya taimake ku a aurenku ba ya jawo hargitsi ba?

Abubuwa Huɗu da Za Su Sa Ku Yi Nasara

Littafi Mai Tsarki ba littafin da ke ba da shawara game yadda za a kashe kuɗi ba ne. Amma yana ɗauke da shawarwari masu amfani da za su iya taimaka wa ma’aurata su guji matsalolin kuɗi. Zai dace idan ka duba shawarar da ya ba da kuma ka gwada shawarwarin da ke gaba.

1. Ku koyi yin magana game da kuɗi cikin natsuwa. “Hikima ce a nemi shawara.” (Karin Magana 13:10, Littafi Mai Tsarki) Ya dangana a kan yadda aka raine ka, neman shawara daga wasu yana iya zama abu mai wuya, musamman da aboki ko abokiyar aure game da batun kuɗi. Duk da haka, tafarki ne na hikima idan kuka tattauna wannan batu mai muhimmanci da juna. Alal misali, me ya sa ba za ku bayyana wa aboki ko abokiyar aurenku ba yadda wataƙila renon da iyayenku suka yi muku ya shafi halin da kuke nuna wa game da kuɗi? Kuma ku fahimci yadda irin rainon da aka yi wa aboki ko abokiyar aurenku ya shafi halin shi ko ita.

Kada ku bari sai matsala ta taso kafin ku tattauna game da kuɗi. Wani marubucin Littafi Mai Tsarki ya tambayi: “Mutum biyu za su iya yin tafiya tare, in ba su rigaya sun yi alkawari ba?” (Amos 3:3) Yaya za mu yi amfani da wannan mizanin? Idan kuka keɓe lokaci don tattaunawa batutuwan kuɗi tare, za ku rage matsalolin da za su iya tasowa domin rashin fahimta.

GWADA WANNAN: Ku keɓe lokacin da za ku riƙa tattaunawa game da kuɗin da iyalin take kashewa. Kuna iya riƙa tattauna batun a ranar farko na kowane wata ko kuwa a ranar da kuka zaɓa a kowane mako. Tattaunawar ta kasance taƙaitacciya, wataƙila minti sha biyar ko ƙasa da hakan. Ku zaɓi lokacin da ku biyu kuke cikin natsuwa. Kuma ku tsai da shawara cewa ba za ku tattauna game da kuɗi ba a wasu lokatai, kamar sa’ad da kuke cin abinci tare ko kuma lokacin da kuke shakatawa tare da yaranku.

2. Ku tsai da shawara game da yadda za ku ɗauki kuɗin da kuke samu. “Wajen ba da girma, kowa ya riga ba ɗan’uwansa.” (Romawa 12:10, LMT) Idan kai kaɗai ne kake karɓan albashi, za ka iya daraja abokiyar aurenka idan ka ɗauki kuɗin da kake samu a matsayin kuɗin iyalin, ba na ka ba.—1 Timotawus 5:8.

Idan kai da abokiyar aurenka kuna karɓan albashi, za ku iya daraja juna ta wajen gaya wa juna ko nawa ne kuke samu da kuma kuɗaɗen da kuka kashe. Idan kuka ɓoye wa juna waɗannan abubuwan, za ku yi wa amincewar da kuka yi wa juna zagon ƙasa kuma za ku ɓata dangantakarku. Ba lallai sai kun tambayi juna ba kafin ku kashe kuɗi ɗan kaɗan. Amma idan kuka tattauna da juna game da sayayya mai yawa, za ku nuna cewa kuna daraja juna.

GWADA WANNAN: Ku tsai da shawara game da kuɗin da ku biyun za ku iya kashewa ba tare da kun tambayi juna ba, kamar naira dubu ɗaya zuwa biyar, ko fiye da hakan. Ka tuntuɓi matarka ko mijinki kafin ku kashe kuɗin da ya fi hakan.

3. Ku rubuta abubuwan da kuke son ku saya. “Yin shiri a tsanaki zai kai ka ga biyan bukatarka.” (Karin Magana 21:5, LMT) Hanya ɗaya na yin shiri don gaba da kuma guje wa kashe kuɗinka a banza shi ne kimanta kuɗin da iyalin za su kashe. Nina, wacce ta yi aure shekaru biyar da suka wuce, ta ce: “Ganin kuɗin da kake samu da wanda ka kashe a rubuce zai iya buɗe ido sosai. Hakan yakan hana musu.”

Bai kamata tsarin kuɗin da kuke son ku kashe ya kasance mai wuyar fahimta ba. Darren, wanda ya yi aure shekaru 26 da suka wuce kuma mai yara maza biyu, ya ce: “Da farko, mukan saka kuɗin da za mu kashe ne a cikin ambulan. Muna saka kuɗin da za mu kashe a makon a cikin ambulan dabam-dabam. Alal misali, muna da ambulan na abinci, nishaɗi, da kuma aski. Idan kuɗin da ke cikin ambulan guda ya ƙare, sai mu ranto daga wani amma mukan tabbata cewa mun sake miyar da kuɗin cikin ambulan ɗin da zarar mun samu kuɗin.” Idan ba ka yawan biyan abubuwan da ka saya da kuɗi, amma kana biya ne da katin banki ko kuma katin bashi, yana da kyau ka rubuta abubuwan da za ka saya kuma ka riƙa bincika kuɗaɗen da ka kashe.

GWADA WANNAN: Ku rubuta kasafin kuɗin da kuke kashewa. Ku tattauna game da nawa za ku riƙa tarawa a cikin kuɗin da kuke samu. Sai ku lissafa kuɗin da za ku riƙa kashewa waɗanda za su iya canjawa, kamar na abinci, lantarki, kuɗin tarho. Sai ku riƙa rubuta ainihin yawan kuɗin da kuke kashewa na watanni da yawa. Idan da bukata, ku yi gwara a salon rayuwarku don kada ku faɗa cikin bashi.

4. Ku rarraba hakkokin. “Gwamma biyu da ɗaya; domin suna da arziki cikin aikinsu.” (Mai-Wa’azi 4:9, 10) A waɗansu iyalai, maigida ne yake kula da sha’anonin kuɗi. A wasu kuma matar ce take kula da wannan nauyin. (Misalai 31:10-28) Ma’aurata da yawa kuwa suna yarda su raba nauyin. “Matata ce take kula da kuɗin da muke biya kuma ita ke biyan ƙananan kuɗaɗe,” in ji Mario, wanda ya yi aure shekaru 21 da suka shige. “Ni ke biyan haraji, kuɗin mota, da na haya. Muna gaya wa juna abubuwan da muka kashe kuma muna aiki tare.” Ko da wane tsari ne kuke bi, abu mafi muhimmanci shi ne yin aiki tare.

GWADA WANNAN: Bayan kun yi la’akari da ƙarfi da kuma kasawar juna, ku tattauna hakkin da kowannenku zai kula da shi. Ku sake bincika shirin bayan ’yan watanni. Ku amince da yin gyara. Don ka san ayyukan da abokiyar aurenka take yi, kamar biyan kuɗin lantarki ko tarho, ko kuma yin sayayya, za ka iya canja hakkokin a wasu lokatai.

Abin da Tattaunawarku Game da Kuɗi Ya Kamata Ya Bayyana

Tattaunawa game da kuɗi bai kamata ya hana ƙauna ba. Leah, wadda ta yi aure shekaru 5 da suka shige, ta ga cewa hakan gaskiya ne. Ta ce: “Ni da mijina mun koyi yin magana game da kuɗi cikin gaskiya babu ɓoye-ɓoye. Sakamakon haka shi ne, muna yin aiki tare, kuma ƙauna da ke tsakaninmu ta daɗu.”

Sa’ad da ma’aurata suka tattauna yadda za su kashe kuɗi, za su kasance da manufa guda kuma za su ƙarfafa gamin aurensu. Sa’ad da suka tattauna da juna kafin su yi sayayya mai tsada, za su nuna daraja ga ra’ayoyi da tunanin juna. Sa’ad da suka yarda su kashe wasu ƙayyadadden kuɗaɗe ba tare da sun tuntuɓi juna ba, hakan zai nuna cewa sun amince da kansu. Waɗannan abubuwan suna daɗa ɗanɗano ga dangantaka ta ƙauna. Babu shakka, irin wannan dangantakar ta fi kuɗi tamani, saboda haka, menene amfanin yin gardama game da kuɗi?

[Hasiya]

a An canja sunayen.

b Littafi Mai Tsarki ya ce “miji kan mata ya ke,” saboda haka, shi ne ke da hakkin faɗin yadda za a kashe kuɗin iyalin da kuma hakkin bi da matarsa cikin ƙauna, ba tare da son kai ba.—Afisawa 5:23, 25.

KA TAMBAYI KANKA . . .

▪ A yaushe ne ni da matata muka tattauna game da kuɗi cikin natsuwa?

▪ Menene zan iya cewa kuma na yi da zai nuna godiya ga taimakon da abokiyar aureta take ba wa iyalin?

[Hotunan da ke shafi na 12]

Menene ya fi muhimmanci a gare ka—Kuɗi ko kuwa aurenka?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba