Kuɗi Yana Kawo Farin Ciki na Gaske Ne?
AN HAIFI Sonia a ƙasar Spain. Sa’ad da take yarinya, ta halarci taron Shaidun Jehobah tare da mahaifiyarta. Amma sa’ad da ta yi girma, sai ta ƙaura zuwa Landan, a ƙasar Ingila, kuma ta soma aiki a ma’aikatar kuɗi.
Sonia tana son aikinta sosai. Tana samun kuɗi sosai kuma tana yi wa masu yin ajiya dillanci sosai. Abin sha’awa ne, kuma ta yi nasara sosai. Sonia takan yi aiki awa sha takwas kullum kuma a wasu dare takan yi barci na awa biyu ko uku ne kawai. Ta mai da duka hankalinta ga aikinta. Sai farat ɗaya, komai ya soma lalacewa. Sonia ta samu cutar gazawar jiki, wataƙila saboda irin mugun aikin da take yi. A lokacin ita ’yar shekara talatin ce kawai.
Ɓangare ɗaya na jikinta ya shanye, kuma likitoci ba su tabbata cewa za ta taɓa sake yin magana ba. Sai mahaifiyarta ta tafi Ingila don ta kula da ita. Sa’ad da Sonia ta soma yin tafiya, mahaifiyarta ta gaya mata, “Za ni taron ikilisiya, kuma sai kin bi ni domin ba zan iya barin ki ke kaɗai ba.” Sonia ta yarda ta bi ta. Menene sakamakon?
“Dukan abin da na ji gaskiya ne. Abu ne mai ban al’ajabi,” Sonia ta tuna. “Na yi farin cikin amincewa da yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare da ɗaya daga cikin waɗanda suka gaida ni a rana ta farko da na je Majami’ar Mulki. Abokai na na dā sun daina zuwa wuri ta, amma sababbin abokaina masu ƙauna da kuma kula ne sosai.”
A hankali a hankali, Sonia ta sake soma yin magana, kuma ta samu ci gaba sosai a ruhaniya. Ƙasa da shekara ɗaya, ta yi baftisma. Yawancin sababbin abokanta suna hidimar Kirista ta cikakken lokaci, kuma ta ga yadda suke farin ciki. “Ni ma ina son na zama kamar hakan,” Sonia ta yi tunani. “Ina so na ba Jehobah Allah dukan abin da zan iya!” A yanzu Sonia tana hidima na cikakken lokaci.
Wane darasi ne Sonia ta koya daga labarinta? “Ko da ina samun kuɗaɗe da yawa, alhini da rashin tsaro da na fuskanta a aikin ya sa ni cikin tunani da kuma rashin farin ciki. A yanzu na gane cewa abu mafi muhimmanci a rayuwa shi ne samun dangantaka mai kyau da Ubanmu na sama, Jehobah. A yanzu ina farin ciki sosai.”
Manzo Bulus ya rubuta cewa “son kuɗi asalin (tushen) kowace irin mugunta ne. Waɗansu kuwa garin begen samu sun ratse daga imani, sun huda kansu da baƙinciki mai-yawa.” (1 Timotawus 6:10) Sonia za ta iya tabbatar da cewa waɗannan kalaman gaskiya ne.