ABIN DA KE SHAFIN FARKO: A YAUSHE NE ZA A DAINA NUNA BAMBANCI A DUNIYA?
Nuna Bambanci Matsala Ce Gama-gari
JONATHAN, wani ɗan Korea da aka haifa a Amirka ya fuskanci wani yanayi na wariyar launin fata tun yana ƙarami. Sa’ad da Jonathan ya girma, ya nemi yankin da zai zauna, inda ba za a nuna masa bambanci saboda kamanninsa ko kuma launin fatarsa ba. Ya zama likita a wani gari da ke arewacin Alaska, a Amirka, inda kamanninsa ya zo ɗaya da na yawancin mutanen da suke zuwa jinya a wurinsa. Yana begen cewa a wannan garin, ba zai ƙara fuskantar wannan mummunar yanayi ba.
Amma, wata rana da yake yi wa wata mata ’yar shekara 25 da ta yi dogon suma jinya ne ya gano cewa babu inda ba a nuna bambanci. Sa’ad da ta farfaɗo, ta kalli fuskar Jonathan sai ta yi zagi don ta tsani ’yan Korea tun tana ƙarama. Wannan abin da ya faru ya sa Jonathan ya fahimci cewa duk iya ƙoƙarinsa don ya guje wa nuna bambanci kuma ya kasance a inda mutane suke mutunta juna, ƙwalliya ce da ba ta biya kuɗin sabulu ba.
Labarin Jonathan ya bayyana abin da ke faruwa a dukan duniya. Kamar dai a duk inda akwai mutane, ana nuna bambanci a wurin.
Duk da cewa nuna bambanci yana ko’ina, yawancin mutane suna Allah wadai da shi. Amma, me ya sa wannan mugun halin da mutane suka tsana ya zama ruwan dare? Hakika, mutane da yawa ba su san cewa su da kansu suna da wannan halin ba. Kai fa, hakan ya shafe ka ne? Mece ce amsarka?
MATSALA DA TA SHAFI KOWANNENMU
Gaskiyar al’amarin ita ce, yana da wuya mutum ya gane ko yana da wannan halin. Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalilin hakan sa’ad da ya ce: “Zuciya ta fi komi rikici.” (Irmiya 17:9) Saboda haka, za mu iya ɗauka cewa muna girmama dukan mutane da suka fito daga wurare dabam-dabam. Wani lokaci kuma muna iya ba da hujja cewa nuna wariya ga wasu mutane ba laifi ba ne.
Ga wani kwatance da zai taimaka mana mu fahimci yadda yake da wuya mu gane ko muna da irin wannan halin a zuciyarmu: A ce kana tafiya kai kaɗai a kan titi da daddare. Sai ka ga samari guda biyu da ba ka taɓa saninsu ba suna zuwa ta wurinka. Samarin ƙaƙƙarfa ne, kuma kamar ɗaya daga cikinsu yana riƙe da wani abu a hannunsa.
Shin, za ka kammala cewa waɗannan samarin za su yi maka barazana ne? Hakika, wani yanayi da ka taɓa samun kanka a dā zai sa ka yi hattara, amma ya kamata hakan ya sa ka tunanin cewa waɗannan samari biyu za su raunata ka? A ganinka, waɗannan samarin ’yan wane yare ne? Wannan tambaya ta biyu za ta iya taimaka maka ka gane ko kana da wannan halin ko a’a. Kuma za ta iya bayyana ko wannan halin nuna bambanci ya ɗan shafe ka.
Idan muna faɗa wa kanmu gaskiya, za mu amince cewa dukanmu muna nuna bambanci a wani lokaci. Littafi Mai Tsarki ma ya bayyana wata hanya da mutane suke yawan nuna bambanci sa’ad da ya ce: “Mutum yakan dubi kyan tsari.” (1 Sama’ila 16:7, Littafi Mai Tsarki) Tun da yake wannan halin ya shafe kowannenmu kuma hakan yakan jawo mugun sakamako, akwai bege cewa za mu iya kawar da halin nuna bambanci a zuciyarmu? Shin, akwai lokaci da ke zuwa da dukan mutane za su daina nuna bambanci gaba ɗaya?