Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 7/1 pp. 5-7
  • A Yaushe Ne Za A Daina Nuna Bambanci a Duniya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • A Yaushe Ne Za A Daina Nuna Bambanci a Duniya?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • LITTAFI MAI TSARKI YA TAIMAKA MUSU SU DAINA NUNA WARIYA
  • MULKIN ALLAH ZAI KAWAR DA NUNA BAMBANCI GABA ƊAYA
  • Nuna Bambanci Matsala Ce Gama-gari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Mu Zama Tsintsiya Madaurinki Daya Kamar Jehobah da Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Koyarwar Allah Tana Sa Mu Daina Nuna Wariya
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 7/1 pp. 5-7

A Yaushe Ne Za A Daina Nuna Bambanci a Duniya?

“INA da wani bege.” Shugaban ƙungiyar kāre ’yancin jama’a ta Amirka, Martin Luther King, Jr. ne ya yi waɗannan kalaman shekaru 50 da suka shige, a wani sanannen jawabinsa a ranar 28 ga Agusta, 1963. Da waɗannan kalmomi masu ban sha’awa da aka sha maimaitawa, shugaba King ya bayyana begen da yake da shi cewa, wata rana mutane za su ji daɗin rayuwa a wani yanayi da babu wariyar launin fata. Ko da yake King ya bayyana ra’ayinsa ga mutanen Amirka ne, amma mutane a ƙasashe da yawa ma sun amince da ƙa’idodin da suka sa ya kasance da wannan kyakkyawar ra’ayi.

Watanni uku bayan shugaba King ya yi jawabin, a rana ta 20 ga Nuwamba, 1963, sama da ƙasashe 100 sun rungumi ƙudurin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi a kan kawar da wariya ta launin fata gaba ɗaya, wato, United Nations Declaration on the Elimination of All Forms of Racial Discrimination. Akwai wasu ƙudurorin da aka yi a ƙasashen duniya da wasu suka ƙara amincewa da su shekaru bayan haka. Shin duk da waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarcen, Mene ne aka cim ma?

A ranar 21 ga Maris, 2012, shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, Ban Ki-moon ya ce: “An yi ƙudurori kuma an ƙulla yarjejeniya masu kyau da yawa, ƙari ga haka, akwai ingantacciyar tsari da aka kafa a ƙasashe don kawar da nuna bambancin launin fata, ƙin bare da kuma wasu halayen wariya. Duk da haka, miliyoyin mutane a faɗin duniya sun ci gaba da shan wahala saboda nuna bambancin launin fata.”

Ko da yake akwai ƙasashen da sun yi ɗan nasara wajen rage nuna bambancin launin fata da kuma wariya, amma har ila, tambayar da za mu yi ita ce: Waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarcen da aka yi sun kawar da ƙiyayya daga zukatan mutane ne, ko kuma sun sa mutane canja yadda suke bayyana ra’ayinsu ne kawai? Wasu mutane sun amince cewa waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarce sun hana mutane nuna wariya a fili ne kawai amma hakan bai kawar da wannan halin daga zukatansu ba. Me ya sa? Domin a bisa doka, nuna bambanci laifi ne da zai sa a hukunta mutum idan an kama shi, amma, da yake ba a sanin abin da ke zuciyar mutum, ba safai ba ne ake gane wanda yake da wannan halin.

Saboda haka, duk wani mataki da za a ɗauka don kawar da nuna bambanci ya kamata ya sa mutane canja tunaninsu game da jama’ar wata al’umma dabam, ba kawai ya sa a hukunta waɗanda aka kama da laifin nuna bambanci ba. Shin, hakan zai yiwu kuwa? Idan zai yiwu, ta yaya? Bari mu yi la’akari da labaran wasu da za su taimaka mana mu san cewa zai yiwu mutane su canja halinsu da kuma abin da zai taimake su su kawar da wannan halin.

LITTAFI MAI TSARKI YA TAIMAKA MUSU SU DAINA NUNA WARIYA

Linda: An haife ni a Afirka ta Kudu. Ina ɗaukan mutanen Afirka ta Kudu da ba Turawa ba a matsayin jahilai, marasa aminci, kuma ina yi musu kallon bayin Turawa. Ina da halin nuna bambanci sosai amma ban san da haka ba. Sa’ad da na soma nazarin Littafi Mai Tsarki, sai na soma canja hali na. Na koyi cewa “Allah ba mai-tara ba ne” kuma halin mutum yana da muhimmanci a gaban Allah fiye da launin fata ko yaren da muke yi. (Ayyukan Manzanni 10:34, 35; Misalai 17:3) Nassin da ke Filibiyawa 2:3 ya sa na gane cewa idan ina ɗaukan mutane da mutunci fiye da yadda na ɗauki kaina, zan iya daina nuna bambanci. Yin rayuwa bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kamar waɗannan ya sa na so mutane ko da launin fatarmu ba ɗaya ba ne. Yanzu ina da kwanciyar hankali don na daina nuna wariya.

Michael: A inda na girma, mutanen Ostareliya masu farar fata ne suka fi yawa, saboda haka, na raina mutanen Asiya sosai, musamman ma Sinawa. Idan ina tuki kuma na ga wani da ya yi kama da ɗan Asiya, nakan sauke gilashin motata kuma in masa ashar kamar “Koma garinku, kai ɗan Asiya!” Daga baya, da na soma nazarin Littafi Mai Tsarki, na zo na fahimci yadda Allah yake ɗaukan mutane da mutunci. Yana ƙaunar dukan mutane ba tare da yin la’akari da inda suka fito ko kuma yadda kamanninsu yake ba. Ƙaunar Allah ta ratsa zuciyata kuma na soma ƙaunar mutane maimakon ƙin jinin su. Na ji daɗin waɗannan canje-canjen da na yi sosai. Yanzu ina sha’awar yin tarayya da mutane da suka fito daga ƙasashe da kuma al’adu dabam-dabam. Hakan ya sa ni farin ciki sosai kuma ya kyautata dangantakata da mutane.

Sandra: Mahaifiyata ’yar Umunede ce a Jihar Delta, a Nijeriya. Amma dangin mahaifina sun fito daga Jihar Edo ne kuma suna yaren Esan. Saboda wannan bambancin, iyalin mahaifina sun nuna wa mamata wariya har ranar mutuwarta. Sai na ƙudurta cewa ba zan yi sha’ani da mutanen Esan ba kuma ba abin da zai sa in auri mutumin Jihar Edo. Amma sa’ad da na soma nazarin Littafi Mai Tsarki, sai na soma tunani a kan al’amarin. Tun da Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ba mai tara ba ne kuma duk wanda yake da tsoron Allah abin karɓa ne a gare shi, yaya zan tsani mutane saboda ƙabilarsu ko kuma yarensu? Hakan ya sa na canja ra’ayina kuma na yi sulhu da dangin mahaifina. Bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ya sa ni farin ciki da kwanciyar hankali. Ƙari ga haka, ya taimaka mini a yadda nake bi da mutane ko da a ce ƙabilarmu ko launin fatarmu ko kuma ƙasarmu ba ɗaya ba. Kuma yanzu mutumin da na aura daga jihar Edo ne kuma ɗan Esan ne!

Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya sa waɗannan mutanen da kuma wasu suka yi nasara wajen kawar da ƙiyayya da nuna bambanci da suka yi saiwa a zukatansu? Domin Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce. Yana da ikon canja tunani da kuma ra’ayin mutum game da wasu. Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki ya nuna mana abin da ake bukata don kawar da nuna bambanci gaba ɗaya.

MULKIN ALLAH ZAI KAWAR DA NUNA BAMBANCI GABA ƊAYA

Ko da yake ilimin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu rage ko kuma mu daina yin mugun tunani a kan mutane, har ila akwai wasu abubuwa biyu da ya kamata a magance kafin a kawar da nuna bambanci gaba ɗaya. Na farko shi ne zunubi da ajizanci. Littafi Mai Tsarki ya bayyana a fili cewa: “Babu mutum wanda ba shi yin zunubi.” (1 Sarakuna 8:46) Shi ya sa, duk iya ƙoƙarin da muka yi don kawar da wannan halin, mukan sami kanmu a yanayi ɗaya da na manzo Bulus, sa’ad da ya ce: “Ni da na ke nufi in aika nagarta, ga mugunta gare ni.” (Romawa 7:21) Saboda wannan ajizancin, a wasu lokatai mukan koma ga yin “miyagun tunani” da ke haifar da nuna bambanci.—Markus 7:21.

Dalili na biyu shi ne tasirin Shaiɗan Iblis. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta shi a matsayin “mai-kisan kai” kuma ya ce shi ne “mai-ruɗin dukan duniya.” (Yohanna 8:44; Ru’ya ta Yohanna 12:9) Hakan ya bayyana dalilin da ya sa nuna bambancin launin fata da na addini da wariya da kisan ƙare-dangi da kuma tsattsauran ra’ayi sun zama ruwan dare gama-gari kuma ’yan Adam ba za su iya kawar da su ba.

Saboda haka, kafin a magance nuna bambanci gaba ɗaya, wajibi ne a kawo ƙarshen zunubi da ajizanci da kuma tasirin da Shaiɗan Iblis yake da shi. Hakika, abin da Littafi Mai Tsarki ya ce Mulkin Allah zai cim ma ke nan.

Yesu Kristi ya koya wa mabiyansa su yi addu’a ga Allah cewa: “Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) Mulkin Allah ne zai kawo ƙarshen rashin adalci, haɗe da nuna bambanci da wariya gaba ɗaya.

Sa’ad da Mulkin Allah ya soma sarauta a duniya, za a “ɗaure” Shaiɗan don kada “ya ƙara ruɗin al’ummai.” (Ru’ya ta Yohanna 20:2, 3) Bayan haka, za a yi “sabuwar duniya,” ko kuma al’umma “inda adalci yake zaune.”a—2 Bitrus 3:13.

Za a mai da waɗanda za su yi rayuwa a cikin sabuwar duniyar nan kamilai, marasa zunubi. (Romawa 8:21) Za su zama talakawan Mulkin Allah kuma ‘ba za su cuci kowa ba; kuma ba za su yi ɓarna’ ba. Me ya sa? Domin “duniya za ta cika da sanin Ubangiji.” (Ishaya 11:9) A lokacin, dukan mutane za su san ƙa’idodin Jehobah kuma za su yi koyi da halayensa masu ban sha’awa. Ta hakan ne za a kawo ƙarshen nuna bambanci gaba ɗaya, “gama a wurin Allah babu tara.”—Romawa 2:11.

a Don ƙarin bayani game da Mulkin Allah da kuma abubuwan da zai cim ma ba da daɗewa ba, ka duba babi na 3, 8 da 9 na littafin nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba