Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 7/1 pp. 3-4
  • Nuna Bambanci Matsala Ce Gama-gari

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Nuna Bambanci Matsala Ce Gama-gari
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MATSALA DA TA SHAFI KOWANNENMU
  • A Yaushe Ne Za A Daina Nuna Bambanci a Duniya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Mu Zama Tsintsiya Madaurinki Daya Kamar Jehobah da Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Koyarwar Allah Tana Sa Mu Daina Nuna Wariya
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 7/1 pp. 3-4

ABIN DA KE SHAFIN FARKO: A YAUSHE NE ZA A DAINA NUNA BAMBANCI A DUNIYA?

Nuna Bambanci Matsala Ce Gama-gari

JONATHAN, wani ɗan Korea da aka haifa a Amirka ya fuskanci wani yanayi na wariyar launin fata tun yana ƙarami. Sa’ad da Jonathan ya girma, ya nemi yankin da zai zauna, inda ba za a nuna masa bambanci saboda kamanninsa ko kuma launin fatarsa ba. Ya zama likita a wani gari da ke arewacin Alaska, a Amirka, inda kamanninsa ya zo ɗaya da na yawancin mutanen da suke zuwa jinya a wurinsa. Yana begen cewa a wannan garin, ba zai ƙara fuskantar wannan mummunar yanayi ba.

Amma, wata rana da yake yi wa wata mata ’yar shekara 25 da ta yi dogon suma jinya ne ya gano cewa babu inda ba a nuna bambanci. Sa’ad da ta farfaɗo, ta kalli fuskar Jonathan sai ta yi zagi don ta tsani ’yan Korea tun tana ƙarama. Wannan abin da ya faru ya sa Jonathan ya fahimci cewa duk iya ƙoƙarinsa don ya guje wa nuna bambanci kuma ya kasance a inda mutane suke mutunta juna, ƙwalliya ce da ba ta biya kuɗin sabulu ba.

Labarin Jonathan ya bayyana abin da ke faruwa a dukan duniya. Kamar dai a duk inda akwai mutane, ana nuna bambanci a wurin.

Duk da cewa nuna bambanci yana ko’ina, yawancin mutane suna Allah wadai da shi. Amma, me ya sa wannan mugun halin da mutane suka tsana ya zama ruwan dare? Hakika, mutane da yawa ba su san cewa su da kansu suna da wannan halin ba. Kai fa, hakan ya shafe ka ne? Mece ce amsarka?

MENE NE NUNA BAMBANCI YA ƘUNSA?

Wasu mutane sun ce nuna bambanci ya ƙunshi ƙin jinin wani saboda inda ya fito. Wasu kuma sun ce mutum zai iya kasance da irin wannan halin domin bai da cikakken bayani game da mutanen wata ƙabila ko al’umma, kuma hakan yakan kai ga kasancewa da ra’ayin da bai dace ba game da waɗannan mutane. Ko ma mene ne yake sa mutane su kasance da irin wannan halin, mutum zai iya ƙin jinin wani saboda bambancin launin fata ko jiki ko jinsi ko yare ko addini ko kuma duk wani abin da yake ganin ya bambanta shi da wancan mutumin.

MATSALA DA TA SHAFI KOWANNENMU

Gaskiyar al’amarin ita ce, yana da wuya mutum ya gane ko yana da wannan halin. Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalilin hakan sa’ad da ya ce: “Zuciya ta fi komi rikici.” (Irmiya 17:9) Saboda haka, za mu iya ɗauka cewa muna girmama dukan mutane da suka fito daga wurare dabam-dabam. Wani lokaci kuma muna iya ba da hujja cewa nuna wariya ga wasu mutane ba laifi ba ne.

Ga wani kwatance da zai taimaka mana mu fahimci yadda yake da wuya mu gane ko muna da irin wannan halin a zuciyarmu: A ce kana tafiya kai kaɗai a kan titi da daddare. Sai ka ga samari guda biyu da ba ka taɓa saninsu ba suna zuwa ta wurinka. Samarin ƙaƙƙarfa ne, kuma kamar ɗaya daga cikinsu yana riƙe da wani abu a hannunsa.

Shin, za ka kammala cewa waɗannan samarin za su yi maka barazana ne? Hakika, wani yanayi da ka taɓa samun kanka a dā zai sa ka yi hattara, amma ya kamata hakan ya sa ka tunanin cewa waɗannan samari biyu za su raunata ka? A ganinka, waɗannan samarin ’yan wane yare ne? Wannan tambaya ta biyu za ta iya taimaka maka ka gane ko kana da wannan halin ko a’a. Kuma za ta iya bayyana ko wannan halin nuna bambanci ya ɗan shafe ka.

Idan muna faɗa wa kanmu gaskiya, za mu amince cewa dukanmu muna nuna bambanci a wani lokaci. Littafi Mai Tsarki ma ya bayyana wata hanya da mutane suke yawan nuna bambanci sa’ad da ya ce: “Mutum yakan dubi kyan tsari.” (1 Sama’ila 16:7, Littafi Mai Tsarki) Tun da yake wannan halin ya shafe kowannenmu kuma hakan yakan jawo mugun sakamako, akwai bege cewa za mu iya kawar da halin nuna bambanci a zuciyarmu? Shin, akwai lokaci da ke zuwa da dukan mutane za su daina nuna bambanci gaba ɗaya?

NUNA BAMBANCI MATSALA CE DA KE KO’INA

Kyanada: “Duk da cewa [ƙasar] tana ƙunshe da mutane daga al’adu dabam-dabam kuma an kafa dokoki da dama don kāre ’yancin al’ummai dabam-dabam da ke cikinta, nuna bambancin launin fata ya ci gaba da zama babbar matsalar da ake fama da shi.”—Ƙungiyar Kāre Hakkin Bil Adama ta Amnesty International, a wani bayani game da ƙasar Kyanada a shekara ta 2012.

Turai: “Mutane kashi 48 a Turai sun amince cewa ba a ɗaukan matakan da suka dace don magance matsalar nuna bambanci a ƙasarsu.”—Intolerance, Prejudice and Discrimination: A European Report, 2011.

Afirka: “Mata suna fuskantar wulaƙanci da wariya sosai a ƙasashe da yawa.”—Amnesty International Report 2012.

Nepal: “Ana nuna wa Dalits, (wata al’umma da ake zalunta) wariya, musamman ma a fannin tattalin arziki, hulɗa da jama’a da kuma a batutuwan al’ada.”—Human Rights Watch World Report, 2012.

Gabashin Turai: “Mutanen Roma da ke gabashin Turai sun zama ƙaramin kuka mai daɗin hawa a ƙasashen waje, sa’an nan a ƙasarsu, suna fuskantar wulaƙanci sosai.”—The Economist, 4 ga Satumba, 2010.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba