Ka Yi Shiri don Jinyar Gaggawa?
Jinya ta gaggawa tana iya faruwa farat ɗaya. (Yaƙ. 4:14) Saboda haka, mai hikima yakan yi shiri sosai. (Mis. 22:3) Shin ka tsai da shawara a kan irin jinyar da za a yi maka kuma ka rubuta hakan? Don a taimake ka, an yi bidiyon nan Transfusion-Alternative Health Care—Meeting Patient Needs and Rights, wanda shi ne na biyu a cikin faifan DVD nan Transfusion-Alternatives—Documentary Series. Yayin da kake kallon wannan bidiyon, ka ga ko za ka iya amsa waɗannan tambayoyi na gaba. Domin bidiyon yana ɗauke da wasu hotunan da suka nuna yadda ake yi wa mutane fiɗa, iyaye su yi amfani da sanin ya kamata sa’ad da suke kallon bidiyon tare da yaransu ƙanana.
(1) Me ya sa masu ba da magani suke sake bincika yin amfani da ƙarin jini? (2) Ka ba da misalai uku na fiɗa masu wuya da aka yi ba tare da ƙarin jini ba. (3) Me ya sa likitoci da yawa a dukan duniya suke da niyyar yi wa majiyyata jinya ba tare da ƙarin jini ba? (4) Mene ne bincike na kwanan bayan nan ya nuna game da yin amfani da jini? (5) Mene ne haɗarin da ke cikin ƙarin jini? (6) Wace kammalawa gwanaye da yawa suka yi game da fa’idodin abubuwan taimako maimakon ƙarin jini? (7) Me ke jawo rashin isashen jini a jiki, kuma me za a yi don jini ya ƙaru cikin jiki? (8) Ta yaya za a daɗa yawan jajayen ƙwayoyin jini a jikin majiyyaci? (9) Ta waɗanne hanyoyi ne ake iya rage zubar da jini a lokacin fiɗa? (10) Abubuwan taimako maimakon ƙarin jini suna taimaka wa yara ko kuwa mutanen da suke yanayi na gaggawa? (11) Wace ce ƙa’ida ta musamman game da magani mai kyau?
Tun da yake wasu irin hanyar jinya da aka nuna a wannan bidiyon ya dangana ga lamirinka, kada ka jira har sai jinya ta gaggawa ta same ka kafin ka yi tunanin irin jinya da za ka amince a yi maka. Babi na 7 na littafin nan Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah da kuma wuraren bincike da aka ambata a ciki da kuma ’yar cikin Hidimarmu Ta Mulki ta Disamba 2006 na Turanci za su taimaka maka ka tsai da shawara mai kyau. Ka cika dukan zaɓin da ka yi cikin katin DPA da aka ba waɗanda suka yi baftisma, kuma ka riƙa ɗaukan katin a kowane lokaci.
[Bayanin da ke shafi na 3]
Ka riga ka yanke shawara game da irin jinyar da za a yi maka kuma ka rubuta hakan?