Tsarin Ayyuka na Makon 10 ga Maris
MAKON 10 GA MARIS
Waƙa ta 1 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 4 sakin layi na 1-9 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Farawa 40-42 (minti 10)
Na 1: Farawa 41:1-16 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Su Waye Za Su Je Sama?—td 38A (minti 5)
Na 3: Muna Bukatar Mu Tsayayya wa Jaraba—lr babi na 9 (minti 5)
Taron Hidima:
Waƙa ta 88
Minti 15: Ibada ta Iyali Mai Armashi. Ka gana da wata iyali game da ibadarsu ta iyali. Yaya suke gudanar da ita? Ta yaya suke sanin abin da za su tattauna? Waɗanne abubuwa da ke www.pr418.com/ha ne suka taɓa amfani da su? Ta yaya tsarin da suka yi ya taimaka musu a yin wa’azi? Ta yaya suka tsara ayyukansu don kada su fasa yin wannan ibadar? Ta yaya suka amfana daga ibada ta iyali?
Minti 15: “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yadda Za Mu Bi da Masu Ba da Hujja don Kada Su Saurare Mu.” Tattaunawa. Ka tattauna hujjoji biyu ko uku da mutane suke bayarwa don kada su saurari saƙonmu, kuma ka ba masu sauraro damar faɗin yadda za su ba da amsa idan suka haɗu da irin waɗannan mutanen. Ka tuna wa masu shela cewa a makon 7 ga Afrilu, za a ba su damar faɗin yadda suka yi amfani da wannan shawarar.
Waƙa ta 97 da Addu’a