Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yadda Za Mu Bi da Masu Ba da Hujja don Kada Su Saurare Mu
Abin da Ya Sa Yake da Muhimmanci: A ce ka sami labari cewa za a yi wani bala’i nan ba da daɗewa ba, kuma mutane za su mutu idan ba su nemi mafaka ba. Sai ka je gidan maƙwabcinka don ka sanar da shi, amma ya katse maka magana yana cewa ba shi da lokaci. Shin za ka bar shi kurum ba tare da ka ƙoƙarta ka taimaka masa ba? Mutane da yawa a yankunanmu suna mana kunnen-ƙashi, da yake ba su san cewa saƙon da muke kawo musu zai iya ceton rayukansu ba. Wataƙila mu tarar cewa sun shagala da wasu ayyuka a lokacin da muka ziyarce su. (Mat. 24:37-39) Ko kuma ba sa so su saurare mu don ƙaryace-ƙaryacen da mutane suke yaɗawa game da mu. (Mat. 11:18, 19) Suna iya zata cewa mu ɗaya ne da sauran addinan da ke aikata munanan ayyuka. (2 Bit. 2:1, 2) Idan da farko maigida ba ya so ya saurare mu, kada mu yi saurin fid da rai.
Ku Bi Wannan Shawarar a Watan Nan:
Bayan kun bar wurin wani da ya ba ku hujja, ku tattauna da abokin wa’azinku yadda yake ganin zai fi dacewa ku bi da irin wannan yanayin.