Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yadda Za Mu Bi da Maigidan da Ya Hasala
Muhimmancinsa: Mutane da yawa da muke haɗuwa da su a lokacin da muke wa’azi suna da ladabi. Amma Yesu ya annabta cewa wasu za su ƙi mu. (Yoh. 17:14) Saboda wannan, kada mu yi mamaki idan wasu magidanta suka yi fushi da mu sosai. Idan hakan ya faru, zai dace mu bi da yanayin a hanyar da za ta faranta wa Jehobah rai, da yake shi ne muke wakilta. (Rom. 12:17-21; 1 Bit. 3:15) Mai yiwuwa idan muka yi hakan, yanayin ba zai daɗa muni ba. Ƙari ga haka, halinmu zai zama shaida ga magidantan da kuma masu kallo, kuma hakan yana iya sa su saurari Shaidun Jehobah a nan gaba.—2 Kor. 6:3.
Ku Bi Shawarar Nan a Wannan Watan:
Ku yi gwaji a kan wannan batun sa’ad da kuke ibada ta iyali.
Bayan kun bar wani maigidan da ya hasala, ku tambayi wanda kuke wa’azi tare yadda yake ganin zai fi dacewa ku bi da yanayin.