‘Ku Yi Zaman Lafiya da Dukan Mutane’
1. Wace shawarar Littafi Mai Tsarki ce za mu bi sa’ad da muka haɗu da mutanen da suke fushi da mu a wa’azi?
1 Mutanen Jehobah suna son zaman lafiya kuma saƙon da muke bayarwa na salama ne. (Isha. 52:7) Duk da haka, wani lokaci, mukan haɗu da mutanen da suke fushi da mu don mun zo yi musu wa’azi. Mene ne zai taimaka mana mu zauna lafiya da mutane a irin wannan yanayi?—Rom. 12:18.
2. Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da fahimi?
2 Ku Kasance Masu Fahimi: Ko da yake wasu mutane sukan yi fushi da mu don ba sa son su ji bishara, akwai wasu da suke fushi don wani dalili dabam, ba domin saƙon da muka kawo musu ba. Wataƙila mun zo yi musu wa’azi a lokacin da bai dace musu ba ne. Wani yana iya yin fushi saboda wata matsala da yake fuskanta. Amma ko da bisharar ce take sa shi fushi da mu, ya kamata mu tuna cewa mai yiwuwa don an yi masa bayanin da ba daidai ba ne game da mu. (2 Kor. 4:4) Fahimtar yanayinsa zai taimaka mana mu kame kanmu don kada mu yi fushi da shi.—Mis. 19:11.
3. Ta yaya za mu bi da maigida cikin mutunci?
3 Ku Mutunta Mutane: Mutane da yawa a yankinmu sun yarda da koyarwar addininsu sosai. (2 Kor. 10:4) Suna da ’yancin zaɓan ko za su saurare mu ko a’a. Bai kamata mu raina addinin wani ko kuma mu nuna masa cewa mun fi shi sanin Littafi Mai Tsarki ba. Idan ya ce mu bar masa gidansa, ya kamata mu yi hakan cikin ladabi.
4. Mene ne yin magana da alheri yake nufi?
4 Ku Yi Magana Mai Daɗin Ji: Ya kamata mu sāka wa mutane da alheri ko da sun zage mu ne. (Kol. 4:6; 1 Bit. 2:23) Maimakon mu yi gardama da su, mu mai da hankali ga tattauna batun da ra’ayinmu da su ya zo ɗaya. Wataƙila, a cikin sanin yakamata za mu iya tambayarsa dalilin da ya sa ba ya son sauraronmu. Amma idan ci gaba da tattaunawar zai ƙara ɓata masa rai, zai fi dacewa mu dasa aya a wurin.—Mis. 9:7; 17:14.
5. Mene ne amfanin bi da mutane a hankali sa’ad da muke wa’azi?
5 Idan wani ya yi mana baƙar magana sa’ad da muke wa’azi kuma ba mu rama ba, wani lokaci idan wasu Shaidu suka zo masa wa’azi zai iya tuna da hali mai kyau da muka nuna kuma ya saurare su. (Rom. 12:20, 21) Ko da ya ci gaba da yi mana tsayayya, wata rana zai iya zama ɗan’uwanmu. (Gal. 1:13, 14) Amma ko da ba zai taɓa son bishara ba, idan muka kame kanmu kuma muka bi da shi cikin hankali, za mu ɗaukaka Jehobah da kuma koyarwarmu.—2 Kor. 6:3.