Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a tattauna tambayoyin da ke gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 28 ga Disamba, 2015. An saka kwanan watan da za a tattauna waɗannan bayanan domin ku yi bincike sa’ad da kuke shirya makaranta a kowane mako.
Ta yaya Dauda ya ɗauki sunan Allah? (1 Laba. 16:8-10) [2 ga Nuwamba, w12 11/15 shafi na 3 sakin layi na 4]
Me ya taimaka wa Dauda ya zama mai karimci, kuma me zai taimaka mana mu bi misalinsa? (1 Laba. 22:5) [9 ga Nuwamba, w05 10/1 shafi na 31 sakin layi na 6]
Mene ne Dauda yake nufi sa’ad da ya ce wa Sulemanu: “Ka san Allah na ubanka”? (1 Laba. 28:9) [16 ga Nuwamba, w11 1/1 shafi na 28 sakin layi na 3, 7]
Abin da Sulemanu ya roƙi Jehobah a 2 Labarbaru 1:10 ya nuna me game da shi, kuma ta yaya hakan zai taimaka mana wajen bincika yadda muke addu’a ga Jehobah? (2 Laba. 1:11, 12) [23 ga Nuwamba, w05 12/1 shafi na 29 sakin layi na 6]
Wane hali na musamman ne Jehobah yake da shi bisa ga 2 Labarbaru 6:29, 30, kuma me ya sa ya kamata mu gaya wa Jehobah duk wani abin da yake damunmu? (Zab. 55:22) [30 ga Nuwamba, w11 1/1 shafi na 11 sakin layi na 7]
Me ya sa Sarki Asa ya yi addu’a don ya yi nasara a kan wata runduna mai girma, kuma wane tabbaci za mu kasance da shi sa’ad da muke ƙoƙarin kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah? (2 Laba. 14:11) [7 ga Disamba, w12 8/15 shafi na 8 sakin layi na 6 zuwa shafi na 9 sakin layi na 1]
Ta yaya yadda Jehobah ya bi da Sarki Jehoshaphat sa’ad da ya yi laifi ya tabbatar mana cewa Jehobah mai ƙauna ne sosai, kuma ta yaya wannan batun zai shafi yadda muke bi da mutane? (2 Laba. 19:3) [14 ga Disamba, w03 7/1 shafi na 29 sakin layi na 13; cl shafi na 245 sakin layi na 12]
Me ya sa za mu “yi shiri” kuma mu “tsaya shuru” a zamaninmu kuma ta yaya za mu yi hakan? (2 Laba. 20:17) [21 ga Disamba, w05 12/1 shafi na 31 sakin layi na 1; w03 6/1 shafi na 29 sakin layi na 15-16]
Ta yaya mutanen Allah suka kasance da haɗin kai a zamanin Jehoshaphat? (2 Laba. 20:13) [21 ga Disamba, w14 12/15 shafi na 23 sakin layi na 8]
Bisa ga 2 Labarbaru 26:5, wa ya taimaka wa matashi Uzziah ya kasance mutumin kirki, kuma ta yaya matasa za su koyi darasi daga Kiristoci da suka manyanta a ikilisiya? [28 ga Disamba, br1-HA shafi na 32 sakin layi na 2, 4]