Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb17 Afrilu p. 6
  • Wakokin Mulki Suna Sa Mu Yi Karfin Hali

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wakokin Mulki Suna Sa Mu Yi Karfin Hali
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Mu Yabi Jehobah Ta Wurin Rera Waka da Farin Ciki
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Shawara a Kan Yin Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Sababbin Waƙoƙi don Ibada!
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Kana Shirye Ka Yi Waƙa Ga Jehobah a Taronmu?
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
mwb17 Afrilu p. 6

RAYUWAR KIRISTA

Waƙoƙin Mulki Suna Sa Mu Yi Ƙarfin Hali

Dan’uwa Erich Frost ya zauna kusa da fiyano

Sa’ad da Bulus da Sila suke kurkuku, sun rera waƙoƙin yabo ga Allah. (A. M. 16:25) A zamaninmu ma, ’yan’uwanmu sun rera waƙoƙin Mulki sa’ad da suke fursuna a Saiberiya da kuma ƙasar Jamus. Misalinsu ya nuna cewa waƙoƙi suna iya sa Kiristoci su yi ƙarfin hali sa’ad da suke fuskantar tsanantawa.

Nan ba da daɗewa ba, yaruka da yawa za su sami sabon littafin waƙa mai jigo “Sing Out Joyfully” to Jehovah. Idan mun karɓi littafin, za mu iya koyan waƙoƙin sa’ad da muke ibada ta iyali. (Afi 5:19) Ruhu mai tsarki zai taimaka mana mu tuna da su sa’ad da muke fuskantar tsanantawa. Waƙoƙin Mulki za su taimaka mana mu mai da hankali ga begenmu. Za su iya sa mu yi ƙarfin hali a lokacin jarrabawa. Kuma sa’ad da muke farin ciki, waƙar za ta sa mu “tada murya da murna” saboda farin cikin da muke ciki. (1Lab 15:16; Za 33:​1-3) Bari mu yi iya ƙoƙarinmu wajen rera waɗannan waƙoƙi na Mulki!

KU KALLI BIDIYON NAN WAƘAR DA TA ƘARFAFA FURSUNONI, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Mene ne ya sa Ɗan’uwa Frost ya rubuta waƙa?

  • Ta yaya waƙar ta sa ’yan’uwan da ke sansanin Sachsenhausen ƙarfin hali?

  • A wane irin yanayi ne waƙoƙin Mulki za su iya ƙarfafa ka?

  • Waɗanne waƙoƙin Mulki ne za ka so ka haddace?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba