Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w24 Agusta pp. 14-19
  • Mu Bi Raꞌayin Jehobah Game da Wadanda Suka Yi Zunubi Mai Tsanani

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mu Bi Raꞌayin Jehobah Game da Wadanda Suka Yi Zunubi Mai Tsanani
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YADDA AKA BI DA WANI DA YA YI ZUNUBI MAI TSANANI
  • DA MAI ZUNUBIN YA TUBA, MENE NE AKA CE ꞌYANꞌUWA SU YI?
  • YADDA ZA MU YI ADALCI DA JINƘAI KAMAR JEHOBAH
  • Yadda Za A Taimaka wa Waɗanda Aka Cire Daga Ikilisiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Yadda Za A Nuna wa Mai Zunubi Kauna da Jinkai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Nemi Amsoshin Waɗannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Daꞌira na Mai Kula da Daꞌira na 2026
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
w24 Agusta pp. 14-19

TALIFIN NAZARI NA 33

WAƘA TA 130 Mu Riƙa Gafartawa

Mu Bi Raꞌayin Jehobah Game da Waɗanda Suka Yi Zunubi Mai Tsanani

“In har wani ya yi zunubi, to, muna da mai tsaya mana.” —1 YOH. 2:1.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga darussa masu muhimmanci daga yadda aka bi da wani ɗanꞌuwa da ya yi zunubi mai tsanani a ikilisiyar Korinti.

1. Wane zaɓi ne Jehobah yake so kowa ya yi?

JEHOBAH ya halicci mutane yadda za su iya zaɓan abin da za su yi. Kuma ba ranar da ba ma yin zaɓi. Zaɓi mafi muhimmanci da mutum zai iya yi shi ne na bauta wa Jehobah tare da bayinsa. Kuma zaɓin da Jehobah yake so kowa ya yi ke nan. Me ya sa? Domin yana ƙaunar kowa kuma yana so su ji daɗi. Ƙari ga haka, yana so kowa ya zama amininsa kuma ya more rayuwa har abada.—M. Sha. 30:​19, 20; Gal. 6:​7, 8.

2. Mene ne Jehobah yake so masu zunubi su yi? (1 Yohanna 2:1)

2 Amma Jehobah ba ya tilasta wa mutum ya bauta masa. Yana barin kowa ya zaɓi abin da zai yi. Me zai faru idan wanda ya yi baftisma ya yi zunubi mai tsanani kuma ya ƙi ya tuba? Dole a cire shi daga ikilisiya. (1 Kor. 5:13) Amma Jehobah ba ya ƙin waɗanda aka cire daga ikilisiya, a ko-da-yaushe yana fatan za su komo gare shi. Wani babban dalilin da ya sa ya yi tanadin fansa shi ne, domin ya iya yafe zunuban waɗanda suka tuba. (Karanta 1 Yohanna 2:1.) Jehobah Allah mai ƙauna ne sosai, shi ya sa yake ƙarfafa masu zunubi su tuba.—Zak. 1:3; Rom. 2:4; Yak. 4:8.

3. Me za mu tattauna a talifin nan?

3 Jehobah yana so mu kasance da raꞌayinsa game da zunubi da masu zunubi. Kuma wannan talifin zai nuna mana yadda za mu yi hakan. Yayin da kake karanta talifin, ka lura da (1) yadda aka bi da wani ɗanꞌuwa da ya yi zunubi mai tsanani a ikilisiyar Korinti, (2) umarni da manzo Bulus ya bayar saꞌad da mutumin ya tuba, kuma (3) abin da labarin nan ya nuna mana game da yadda Jehobah yake ɗaukan waɗanda suka yi zunubi.

YADDA AKA BI DA WANI DA YA YI ZUNUBI MAI TSANANI

4. Mene ne ya faru a ikilisiyar da ke Korinti? (1 Korintiyawa 5:​1, 2)

4 Karanta 1 Korintiyawa 5:​1, 2. A karo na uku da Bulus ya je waꞌazi a ƙasar waje, ya sami labari cewa wani mugun abu yana faruwa a sabuwar ikilisiya da ke Korinti. Wani ɗanꞌuwa yana lalata da matar babansa. Wannan abin ƙyama ne “ko a cikin waɗanda ba su san Allah ba.” Amma ꞌyanꞌuwan da ke ikilisiyar sun ƙyale shi. Wataƙila wasu daga cikinsu sun ɗauka cewa jinƙai suke masa kamar Jehobah. Amma Jehobah ba ya amincewa da zunubi. Ba mamaki halinsa ya sa waɗanda ba sa bauta wa Jehobah sun soma yi wa bayinsa kallon masu ƙazanta. Kuma idan aka ci-gaba da ƙyale shi a ikilisiyar, mai yiwuwa wasu a ikilisiya su soma bin halinsa. Mene ne Bulus ya ce su yi?

5. Mene ne Bulus ya ce ikilisiyar su yi, kuma me hakan yake nufi? (1 Korintiyawa 5:13) (Ka kuma duba hoton.)

5 Karanta 1 Korintiyawa 5:13. Jehobah ya sa Bulus ya rubuta wa ikilisiyar cewa su cire wannan mai zunubin da ya ƙi tuba daga ikilisiya. Yaya ya kamata hakan ya shafi maꞌamalarsu da shi? Bulus ya ce musu ‘kada su haɗa kai’ da shi. Me hakan yake nufi? Bulus ya bayyana cewa ‘ko cin abinci’ kada su yi da shi. (1 Kor. 5:11) Idan aka zauna ana cin abinci tare da mutum, za a yi hira da shi. Don haka, abin da Bulus yake nufi shi ne kada su yi tarayya da mutumin. Hakan zai taimaki mutanen da ke ikilisiyar kada su koyi mugun halinsa. (1 Kor. 5:​5-7) Ƙari ga haka, zai taimaki mutumin ya ga cewa ya ɓata wa Jehobah rai sosai. Mai yiwuwa ya ji kunya kuma hakan ya sa ya tuba.

Manzo Bulus yana rubutu a kan wata takarda, irin wadda ake naɗewa.

Jehobah ya sa Bulus ya rubuta wa ikilisiyar cewa su cire wannan mai zunubin da ya ƙi ya tuba daga ikilisiya (Ka duba sakin layi na 5)


6. Mene ne ꞌyanꞌuwan suka yi da suka karanta wasiƙar Bulus, kuma wane sakamako aka samu?

6 Bayan da Bulus ya aika musu wasiƙar, ba mamaki ya yi ta tunanin yadda za su ji da kuma abin da za su yi. Sai Titus ya kawo masa wani rahoto mai daɗi. Ya gaya masa cewa ꞌyanꞌuwan sun bi abin da ya ce da zuciya ɗaya. (2 Kor. 7:​6, 7) A sakamakon haka, ba da daɗewa ba mutumin ya tuba! Ya canja halinsa da tunaninsa kuma ya soma yin nufin Jehobah. (2 Kor. 7:​8-11) Mene ne Bulus ya gaya wa ikilisiyar su yi wannan karon?

DA MAI ZUNUBIN YA TUBA, MENE NE AKA CE ꞌYANꞌUWA SU YI?

7. Ta yaya horon da aka yi wa mutumin ya cim-ma nufinsa? (2 Korintiyawa 2:​5-8)

7 Karanta 2 Korintiyawa 2:​5-8. Bulus ya ce musu: “Horon da mutumin nan ya sha a ta wannan hanya daga wurin yawancinku, ya isa haka.” Wato, horon da suka yi masa ya cim-ma nufinsa. Dā ma an yi masa horon ne don hakan ya taimaka masa ya tuba.—Ibran. 12:11.

8. Mene ne Bulus ya ce su yi da mai zunubin ya tuba?

8 Yanzu da mutumin ya tuba, Bulus ya ce wa ꞌyanꞌuwan: “Ku yafe masa, ku kuma yi masa taꞌaziyya.” Ya kuma ce: “Ku tabbatar masa cewa kuna ƙaunarsa sosai.” Ka lura cewa ba dawo da shi cikin ikilisiya ne kawai Bulus ya ce su yi ba. Amma ya so su tabbatar masa cewa sun yafe masa kuma suna ƙaunarsa, ta ayyukansu da kalamansu. Hakan zai sa ɗanꞌuwan ya ga cewa an karɓe shi hannu bibbiyu.

9. Me ya sa wataƙila ya yi ma wasu wuya su karɓi mutumin hannu bibbiyu?

9 Wataƙila ya yi ma wasu wuya su karɓi mutumin hannu bibbiyu. Me ya sa muka ce hakan? Domin abin da ya yi ya jawo matsaloli a ikilisiya kuma wataƙila ya kunyatar da wasu ꞌyanꞌuwa. Ƙari ga haka, riƙe aminci bai da sauƙi. Don haka, wataƙila wasu ꞌyanꞌuwan sun ga kamar bai dace a bar wannan da ya yi sakaci sosai ya dawo cikinsu ba. (Ka duba Luka 15:​28-30.) Amma me ya sa yake da muhimmanci ꞌyanꞌuwan su nuna masa ƙauna a wannan lokacin?

10-11. Me zai faru idan dattawan sun ƙi su yafe wa mutumin?

10 Yaya mutumin zai ji a ce bayan ya tuba, dattawa ba su dawo da shi cikin ikilisiya ba? Ko kuma yaya zai ji a ce an dawo da shi amma ꞌyanꞌuwa sun ƙi su nuna masa ƙauna? Mai yiwuwa “baƙin ciki ya sha ƙarfinsa.” Ko ya ga kamar ba zai iya bauta wa Jehobah kuma ba, ko kuma ya daina ƙoƙarin gyara dangantakarsa da Jehobah.

11 Abu mafi muni ma shi ne, idan ꞌyanꞌuwan suka ƙi su yafe masa, Jehobah zai yi fushi da su. Me ya sa? Domin hakan zai nuna cewa ba sa koyi da shi, Allah mai gafartawa. A maimakon haka, suna bin halin Shaiɗan, wanda shi mugu ne kuma marar tausayi. Kuma hakan zai sa Shaiɗan ya yi amfani da su wajen hana mutumin bauta wa Jehobah.—2 Kor. 2:​10, 11; Afis. 4:27.

12. Ta yaya ꞌyanꞌuwan za su nuna cewa suna koyi da Jehobah?

12 Ta yaya ꞌyanꞌuwan za su nuna cewa suna koyi da Jehobah, ba Shaiɗan ba? Ta wajen yafe wa mai zunubin kamar yadda Jehobah yake yi. Ga abin da wasu marubutan Littafi Mai Tsarki suka ce game da Jehobah. Dauda ya ce shi “mai alheri ne kuma mai yin gafara.” (Zab. 86:5) Mika ya ce: “Kai Allah ne mai yafe laifi, mai kawar da zunubi.” (Mik. 7:18) Ishaya kuma ya ce: “Bari mai mugunta ya bar hanyarsa, marar adalci kuma ya bar tunaninsa. Bari ya komo ga Yahweh, shi kuwa zai yi masa jinƙai, ya komo ga Yahweh gama a shirye yake ya gafarce shi.”—Isha. 55:7.

13. Me ya sa ya dace a dawo da mutumin cikin ikilisiya ba tare da ɓata lokaci ba? (Ka duba akwatin nan, “A Wane Lokaci Ne Aka Dawo da Mai Zunubin nan a Ikilisiyar Korinti?”)

13 ꞌYanꞌuwa da ke Korinti suna bukatar su yafe wa mai zunubin kuma su nuna masa cewa suna ƙaunarsa. Abin da zai nuna cewa suna koyi da Jehobah ke nan. Ƙari ga haka, Bulus ya ce idan suka yafe masa, za su nuna cewa su masu biyayya ne. (2 Kor. 2:9) Ko da yake ꞌyan watanni ne suka wuce daga lokacin da aka cire mutumin daga ikilisiya, yanzu ya tuba. Don haka, bai kamata a yi jinkirin dawo da shi cikin ikilisiya ba.

A Wane Lokaci Ne Aka Dawo da Mai Zunubin nan a Ikilisiyar Korinti?

Kamar dai mai zunubin da aka ambata a 1 Korintiyawa sura 5, bai daɗe sosai ba kafin aka dawo da shi. Me ya sa muka ce haka?

Ka lura da lokacin da Bulus ya rubuta wasiƙu biyun da ya aika wa ꞌyanꞌuwan da ke Korinti. A farko-farkon shekara ta 55 bayan haihuwar Yesu ne ya rubuta na farkon, wato a karo na uku da ya je waꞌazi a ƙasar waje. Kuma da alama cewa daga baya a wannan shekarar ne ya rubuta na biyun.

Ƙari ga haka, a wasiƙarsa ta farko ne manzo Bulus ya ba da umarni a kan yadda za a tattara kayan agaji don ꞌyanꞌuwa da ke yankin Yahudiya. Ana bukatar kayan agajin da gaggawa don ꞌyanꞌuwan suna fama da yunwa. Saboda haka, ba mamaki Bulus bai ɗauki lokaci sosai kafin ya tura musu wasiƙarsa ta biyu ba, inda ya ce a haɗa gudummawar da wuri a kai musu.—1 Kor. 16:1; 2 Kor. 9:5.

Wani babban dalili kuma da zai sa Bulus ya rubuta wasiƙarsa ta biyu ba tare da ɓata lokaci ba shi ne, ya ji cewa mutumin ya tuba. A zamaninsu, za a iya yin kwanaki da yawa kafin wasiƙar ta kai hannun ꞌyanꞌuwan. Saboda haka, ba mamaki Bulus bai ɓata lokaci wajen rubuta masu wasiƙarsa ta biyu ba, don ya gaya musu abin da za su yi.

Kiristoci a Korinti suna marabtar mutumin da aka dawo da shi cikin ikilisiya.

Hakan ya nuna cewa tsakanin lokacin da aka cire mutumin daga ikilisiya da lokacin da Bulus ya ce a dawo da shi, bai daɗe sosai ba. Wataƙila ꞌyan watanni ne kawai.

YADDA ZA MU YI ADALCI DA JINƘAI KAMAR JEHOBAH

14-15. Me muka koya daga yadda aka bi da mai zunubin nan a Korinti? (2 Bitrus 3:9) (Ka kuma duba hoton.)

14 Me ya sa aka rubuta labarin yadda aka bi da mai zunubin nan a Korinti? Domin “a koyar da mu” ne. (Rom. 15:4) Labarin ya nuna mana cewa Jehobah ba ya barin waɗanda suka yi zunubi mai tsanani kuma sun ƙi tuba, su ci-gaba da zama a ikilisiya. Wasu suna ganin kamar da yake Jehobah mai jinƙai ne, zai ƙyale masu zunubin da ba su tuba ba su ci-gaba da zama a ikilisiya. Amma a gun Jehobah, barin mai zunubin da ya ƙi tuba a ikilisiya, ba jinƙai ba ne. Jehobah mai jinƙai ne kam, amma ba kome ne yake amincewa da shi ba. (Yahu. 4) Idan Jehobah ya bar masu zunubin da suka ƙi tuba a ikilisiya, hakan zai zama matsala sosai ga sauran ꞌyanꞌuwa.—K. Mag. 13:20; 1 Kor. 15:33.

15 Amma labarin ya kuma nuna cewa Jehobah ba ya so wani ya halaka. A kullum yana so ya ceci mai zunubi. Idan mutum ya tuba kuma ya nuna cewa yana so ya kusaci Jehobah, Jehobah zai yi masa jinƙai. (Ezek. 33:11; karanta 2 Bitrus 3:9.) Shi ya sa da mai zunubin nan a Korinti ya tuba kuma ya canja halinsa, Jehobah ya sa manzo Bulus ya gaya wa ikilisiyar da ke Korinti su yafe masa kuma su dawo da shi.

Wata ꞌyarꞌuwa a Majamiꞌar Mulki ta rungumi wata da aka dawo da ita cikin ikilisiya ranar. Ga wasu ꞌyanꞌuwa kewaye da su.

Idan muna nuna wa waɗanda aka dawo da su ƙauna, hakan zai nuna cewa muna koyi da Jehobah (Ka duba sakin layi na 14-15)


16. Me ya burge ka game da yadda Jehobah ya sa aka bi da mai zunubin nan a ikilisiyar Korinti?

16 Yadda aka bi da mai zunubin nan a Korinti ya taimaka mana mu ga yawan ƙaunar Jehobah da adalcinsa. (Zab. 33:5) Muna yabon Jehobah don waɗannan halayen nasa masu burgewa. Dukanmu masu zunubi ne kuma muna bukatar Jehobah ya gafarta mana. Shi ya sa ya kamata mu gode wa Jehobah don fansar da ya bayar. Fansar ce ta sa yake iya gafarta mana. Muna samun ƙarfafa sosai a duk lokacin da muka tuna cewa Jehobah yana ƙaunarmu kuma yana so mu ji daɗin rayuwa har abada!

17. Waɗanne tambayoyi ne za a amsa a talifofi na gaba?

17 A yau kuma fa, idan mutum ya yi zunubi yaya ya kamata a bi da shi? Ta yaya dattawa za su yi koyi da Jehobah kuma su taimaki mai zunubi ya tuba? Idan an cire mutum daga ikilisiya ko an dawo da shi, me ya kamata ꞌyanꞌuwa su yi? Za a amsa tambayoyin nan a talifofi na gaba.

MECE CE AMSARKA?

  • Wane zaɓi ne Jehobah yake so kowa ya yi?

  • Da wani ɗanꞌuwa a ikilisiyar da ke Korinti ya ƙi tuba, me Bulus ya ce ꞌyanꞌuwan su yi?

  • Bayan da ɗanꞌuwan ya tuba, me Bulus ya ce su yi?

WAƘA TA 109 Mu Kasance da Ƙauna ta Gaske

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba